Koma ka ga abin da ke ciki

Shin Allah Yana Ko’ina Ne a Sama da Ƙasa?

Shin Allah Yana Ko’ina Ne a Sama da Ƙasa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Allah yana iya ganin ko’ina kuma zai iya yin abin da yake so ya yi a duk wurin da ya ga dama. (Misalai 15:3; Ibraniyawa 4:13) Amma Littafi Mai Tsarki bai koya mana cewa Allah yana ko’ina a sama da duniya ba. A maimakon haka, Allah yana nan da kansa kuma yana zama a wurin zamansa.

  •   Surar Allah: Allah ruhu ne. (Yohanna 4:24) ‘Yan Adam ba za su iya ganinsa ba. (Yohanna 1:18) A cikin dukan wahayin da ‘yan Adam suka ga Allah, sun gan shi a wurin zamansa ne. Littafi Mai Tsarki bai taba cewa Allah yana kowane wuri ba.​—Ishaya 6:​1, 2; Ru’ya ta Yohanna 4:​2, 3, 8.

  •   Wurin zaman Allah: Allah yana zama a inda halittun ruhu suke, kuma wurin ya bambanta da duk wani wurin da Allah ya halitta. A wannan wurin, an ce ‘sama ne wurin zaman’ Allah. (1 Sarakuna 8:30) Littafi Mai Tsarki ya yi maganar lokacin da halittun ruhu suka je “domin su bayyana a wurin Ubangiji,” a kuma hakan ya nuna cewa Allah yana da wurin zamansa.​—Ayuba 1:6.

Idan Allah ba ya kowane wuri a cikin sama da kasa, ta yaya zai iya kula da ni?

 E. Allah ya damu da kowannenmu sosai. Ko da yake Allah yana zama a inda halittun ruhu suke, yana ganin dukan wadanda suke kokari su yi nufinsa kuma yana taimaka musu. (1 Sarakuna 8:39; 2 Labarbaru 16:9) Ga wasu hanyoyin da Jehobah yake nuna cewa ya damu da bayinsa:

  •   Sa’ad da kake addu’a: Jehobah zai iya jin addu’arka da zarar ka soma yin addu’a.​—2 Labarbaru 18:31.

  •   A lokacin da kake bakin ciki: “Ga wadanda an karya musu karfin gwiwa, Yahweh yana kusa da su, yakan kubutar da masu fid da zuciya.”​—Zabura 34:​18, Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana./ “Ubangiji [“Jehobah,” NW] yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.”​—Littafi Mai Tsarki.

  •   A lokacin da kake bukatar ja-gora: Jehobah zai “koya maka hanyar da za ka bi” ta wajen amfani da Kalmarsa, wato, Littafi Mai Tsarki.​—Zabura 32:​8, Littafi Mai Tsarki.

Ra’ayin da ba daidai ba game da kasancewar Allah a ko’ina

 Karya: Allah yana dukan wuraren da ya halitta.

 Gaskiya: Allah ba ya zama a ko’ina a cikin duniya, ko ma duk wani wurin da ya halitta. (1 Sarakuna 8:27) Hakika, taurari da wasu abubuwan da aka halitta suna ‘bayyana daukakar Allah.’ (Zabura 19:1) Amma Allah ba ya zama a cikin wurin da ya halitta, kamar yadda mai yin zane ba zai iya shiga cikin zanen da ya yi don ya zauna ba. Duk da haka, zanen zai iya nuna mana abubuwa da yawa game da wanda ya yi zanen. Hakazalika, abubuwan da Allah ya halitta a duniya suna koya mana abubuwa da yawa game da “al’amuran Allah da ba su ganuwa,” kamar ikonsa da hikimarsa da kuma kaunarsa.​—Romawa 1:20.

 Karya: Kafin Allah ya san kome har ya zama mai iko duka, wajibi ne ya kasance a ko’ina.

 Gaskiya: Ruhu mai tsarki shi ne ikon da Allah yake amfani da shi ya yi ayyuka da yawa. Ta wurin ruhu mai tsarki, Allah zai iya sanin kome kuma ya yi duk abin da yake so a lokacin da yake so kuma a duk inda ya ga dama. Ba sai ya je ya kasance a wurin a zahiri ba.​—Zabura 139:7.

 Karya: Zabura 139:8 ta nuna cewa Allah yana ko’ina domin ta ce: “Idan na hau zuwa cikin sama, kana can: Idan na yi shimfidata cikin Lahira, ga ka a can kuma.”

 Gaskiya: Wannan ayar ba ta magana game da wurin zaman Allah. Yana dai nuna mana cewa babu wani wurin da za mu kasance da nisan sa zai hana Allah taimaka mana.

a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yahweh ko kuma Jehobah shi ne sunan Allah.