Koma ka ga abin da ke ciki

Ta Juyin Halitta Ne Allah Ya Yi Abubuwa Masu Rai?

Ta Juyin Halitta Ne Allah Ya Yi Abubuwa Masu Rai?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A’a. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ya halicci ’yan Adam da dabbobi da kuma tsire-tsire ‘iri-iri.’ a (Farawa 1:​12, 21, 25, 27; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Ya gaya mana cewa dukan mutane sun samo asali ne daga iyayenmu na farko, Adamu da Hauwa’u. (Farawa 3:20; 4:1) Littafi Mai Tsarki bai amince da ra’ayin nan cewa ta juyin halitta ne Allah ya yi abubuwa masu rai dabam-dabam ba. ’Yan kimiyya sun lura cewa a kowane irin halitta, ana iya samun bambanci a tsakaninsu kuma Littafi Mai Tsarki bai karyata hakan ba.

 Mene ne ra’ayin wasu mutane?

 Mutanen da suke cewa Allah ya yi amfani da juyin halitta wajen yin abubuwa masu rai suna da ra’ayoyin da suka bambanta. Littafin nan Encyclopædia Britannica ya ce, “wasu mutane sun ce Allah yana amfani da juyin halitta wajen sarrafa abubuwan da suke faruwa a duniya.”

 Wasu da ke da wannan ra’ayin sun yi imani cewa:

  •   Dukan halittu masu rai sun samo asali ne daga halitta iri daya da aka yi shekaru da yawa da suka shige.

  •   Wata halitta za ta iya canjawa gabaki daya kuma ta zama wata halitta dabam.

  •   Allah ne yake sa wadannan canje-canjen su faru.

 Shin juyin halitta ya jitu da abin da ke Littafi Mai Tsarki?

 Wadannan suke da ra’ayin nan suna nufin cewa ba dukan abin da littafin Farawa ya fada game da halitta ne daidai ba. Amma, Yesu ya tabbatar mana cewa labarin da ke littafin Farawa abu ne da ya faru da gaske. (Farawa 1:​26, 27; 2:​18-24; Matiyu 19:​4-6) Littafi Mai Tsarki ya ce kafin Yesu ya zo duniya, yana tare da Allah a sama kuma ya taimaka wajen halittar “dukan abubuwa.” (Yohanna 1:3) Saboda haka, ra’ayin nan cewa ta juyin halitta ne Allah ya yi abubuwa masu rai dabam-dabam bai jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba.

 Yadda jikin itatuwa da dabbobi suke canjawa bisa ga yanayinsu fa?

 Littafi Mai Tsarki bai gaya mana yawan bambance-bambancen da za a iya samu tsakanin halittu iri daya ba. Kuma bai ce dabbobi da kuma itatuwan da Allah ya halitta ba za su iya haifar da wani jinsi ko kuma su canja sakamakon wurin da suka samu kansu ba. Ko da yake wasu suna ganin wadannan bambance-bambancen juyin halitta ne, ba wani sabon halitta ne suke haifarwa ba.

a Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “iri” (kind), wadda ma’anar tana da fadi sosai fiye da kalmar nan “nau’i” (species) da ’yan kimiyya suke amfani da ita. A yawancin lokaci, ’yan kimiyya sukan ce wata halitta ta juya ta zama wata halitta dabam, amma gaskiyar ita ce, halittu suna da jinsi ne iri-iri kamar yadda littafin Farawa ya ambata, ba wai suna juyawa su zama wata halitta dabam ba.