Koma ka ga abin da ke ciki

Wane ne Mika’ilu, Shugaban Mala’iku?

Wane ne Mika’ilu, Shugaban Mala’iku?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Mika’ilu, ko “waliyyin Mika’ilu,” yadda wasu addinai suke kira, suna ne da ake kiran Yesu kafin ya zo duniya da kuma bayan ya koma sama. a Mika’ilu ya yi gardama da Shaidan bayan mutuwar Musa kuma ya taimaka wa wani mala’ika ya idar da sakon Allah ga annabi Daniyel. (Daniyel 10:​13, 21; Yahuda 9) Ta wurin goyon bayan sarautar Allah da kuma yakar magabtan Allah, Mika’ilu ya nuna cewa yana rayuwar da ta jitu da ma’anar sunansa, wato “Babu Wani Kamar Allah.”​—Daniyel 12:1; Ru’ya ta Yohanna 12:7.

 Ga wasu dalilan da suka sa muka yarda cewa Yesu shi ne Mika’ilu, shugaban mala’iku.

  •   Mika’ilu ne “shugaban mala’iku.” (Yahuda 9) Lakabin nan “shugaban mala’iku” ya bayyana a wurare biyu ne kawai a cikin asalin rubuce-rubuce na dā na Littafi Mai Tsarki. A dukan wuraren da ya bayyana, kalmar tana nufin mutum daya ne, saboda haka, mala’ika daya ne tak ake kiransa da wannan lakabin. Dayan ayar da ke dauke da lakabin nan ta ce Ubangiji Yesu, wanda ya tashi daga mutuwa zai “sauko daga sama, da kira mai karfi, da muryar [“shugaban,” NW] malaiku.” (1 Tasalonikawa 4:16) Yesu yana da muryar ‘shugaban mala’iku’ domin shi ne shugaban mala’iku.

  •   Mika’ilu ne yake yi wa rundunar mala’iku masu aminci ja-gora. ‘Mika’ilu da mala’ikunsa sun yi yaki da macijin nan,’ Shaidan. (Ru’ya ta Yohanna 12:7) Mika’ilu yana da babban matsayi a sama, shi ya sa ake kiran shi “daya daga cikin manyan shugabanni” da kuma ‘babban jarumi.’ (Daniyel 10:​13, 21, Littafi Mai Tsarki Juyi Mai Fitar da Ma’ana; 12:1) Wadannan lakabin sun nuna cewa Mika’ilu ne “shugaban rundunar mala’iku,” kamar yadda wani masanin Littafi Mai Tsarki mai suna David E. Aune ya ce.

     Littafi Mai Tsarki ya ambata sunan mutum daya ne kawai da yake da iko bisa rundunar mala’iku. Ya kwatanta “lokacin bayyanuwar Ubangiji Yesu daga sama tare da mala’ikun ikonsa cikin wuta mai huruwa, yana daukan ramako.” (2 Tasalonikawa 1:​7, 8; Matta 16:27) Sa’ad da Yesu ya koma sama, “an sarayyar da mala’iku da mulkoki da ikoki karkashinsa.” (1 Bitrus 3:​21, 22) Ba zai yiwu a ce Allah ya nada Yesu a matsayin shugaban mala’iku sa’an nan ya sake nada Mika’ilu shi ma ya zama shugaban mala’iku ba. Saboda haka, zai dace mu yarda cewa Yesu da Mika’ilu sunayen mala’ika daya ne.

  •   Mika’ilu ‘zai tashi tsaye’ a “kwanakin wahala irin da ba a taba yi ba.” (Daniyel 12:1) A cikin littafin Daniyel, akan yi amfani da furucin nan “tashi tsaye” idan ana magana game da sarkin da ya tashi don ya dauki wani mataki na musamman. (Daniyel 11:​2-4, 21) Yesu Kristi wanda aka ce da shi “Kalmar Allah,” zai dauki mataki na musamman a matsayinsa na “Sarkin Sarakuna” don ya hallaka dukan magabtan Allah kuma ya kāre bayin Allah. (Ru’ya ta Yohanna 19:​11-16) Zai dauki wannan matakin ne a lokacin “kunci mai girma, irin da ba a taba yi ba tun farkon duniya.”​—Matta 24:​21, 42.

a A cikin Littafi Mai Tsarki, ana iya kiran mutum da suna fiye da daya, alal misali Yakubu (wani sunansa shi ne Isra’ila) da Bitrus (wani sunansa shi ne Siman) da kuma Taddawus (wani sunansa shi ne Yahuda).​—Farawa 49:​1, 2; Matta 10:​2, 3; Markus 3:18; Ayyukan Manzanni 1:13.