Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Nufin Allah a Gare Ni?

Mene Ne Nufin Allah a Gare Ni?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Allah yana so ka san shi sosai, ka zama abokinsa, ka ƙaunace shi kuma ka bauta masa da dukan zuciyarka. (Matta 22:37, 38; Yaƙub 4:8) Za ka iya sanin nufin Allah ta wajen yin la’akari da rayuwar Yesu da kuma koyarwarsa. (Yohanna 7:16, 17) Yesu ya koya wa mutane nufin Allah, kuma ya yi rayuwa da ta jitu da wannan nufin. Shi ya sa ya ce abin da ya fi masa muhimmanci a rayuwa shi ne yin ‘nufin wanda ya aiko shi,’ ba na kansa ba.—Yohanna 6:38.

Shin zan iya sanin nufin Allah a gare ni ba tare da ya gaya mini ta wahayi ko mafarki ko kuma mu’ujiza ba?

 E, domin Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da saƙon Allah, kuma zai iya shirya ka “domin kowane managarcin aiki.” (2 Timotawus 3:16, 17) Allah yana so ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma “basirarka” don ka san nufinsa a gare ka.—Misalai 3:21, 22, Littafi Mai Tsarki; Afisawa 5:17.

Zan iya yin nufin Allah kuwa?

 Hakika, za ka iya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dokokinsa fa ba su da ban ciwo [wuya] ba.” (1 Yohanna 5:3) Hakan ba ya nufin cewa bin dokokin Allah yana da sauƙi a kowane lokaci. Amma idan ka ƙoƙarta wajen binsu, kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Yesu ya ce: “Albarka tā fi tabbata ga waɗanda ke jin maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”—Luka 11:28, LMT.