Koma ka ga abin da ke ciki

Su Waye ne “Maza Uku Masu Hikima”? Sun Bi ‘Tauraro’ Zuwa Betelehem Ne?

Su Waye ne “Maza Uku Masu Hikima”? Sun Bi ‘Tauraro’ Zuwa Betelehem Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 A lokacin Kirisitimeti, mutane da yawa suna yin magana game da “maza uku masu hikima” ko kuma “sarakuna uku” don su bayyana matafiya uku da suka ziyarci Yesu bayan an haife shi. (Matiyu 2:1) Matiyu marubucin Linjila ya yi amfani da kalmar Helenanci ma’go don ya bayyana mutanen da suka ziyarci Yesu. Da alama wannan kalmar tana nufin masu ilimin gane taurari da kuma wasu ayyukan da suka shafi aljanu. a Juyin Littafi Mai Tsarki da yawa sun yi amfani da kalmar nan “shehuna” ko kuma “masanan taurari.” b

 ‘Maza masu hikimar’ su nawa ne?

 Littafi Mai Tsarki bai fada ba, kuma mutane suna da ra’ayi dabam-dabam game da ko maza masu hikimar nawa ne. Littafin nan Encyclopedia Britannica ya ce: “Mutane da yawa da suke zama a Asiya sun gaskata cewa mazan guda 12 ne, amma mutanen Turai da kuma Amirka sun gaskata cewa mutanen uku ne, watakila sun gaskata hakan ne domin Matiyu 2:11 ya ce sun ba Yesu kyauta uku wato “kyautar zinariya, da turaren lubban, da mur.”

 ‘Maza masu hikimar’ sarakuna ne?

 Ko da yake a Kirisimeti ana cewa mazan sarakuna ne, Littafi Mai Tsarki bai ce su sarakuna ne ba. Littafin nan Encyclopedia Britannica ya ce darurruwan shekaru bayan an haifi Yesu, mutane sun yi karin gishiri a labarin haihuwar Yesu kuma da yawa suka soma cewa mazan da suka ziyarce Yesu sarakuna ne.

 Mene ne sunayen ‘maza masu hikimar’?

 Littafi Mai Tsarki bai ambata sunayen masana taurarin ba. Littafin nan The International Standard Bible Encyclopedia ya ce, “akwai tatsuniyoyi da suka ce sunayen mutanen Gaspar da Melchior da Balthasar ne.”

 Yaushe ne ‘maza masu hikimar’ suka ziyarci Yesu?

 Watakila masu ilimin gane taurarin sun ziyarci Yesu ne bayan wasu watanni da aka haife shi. Mun san hakan ne domin Sarki Hirudus wanda yake so ya kashe Yesu ya ba da umurni cewa a kashe yara masu shekara biyu zuwa kasa. Ya yanke wannan shawarar ne domin labarin da ya ji daga masu ilimin gane taurarin game da Yesu.​—Matiyu 2:16.

 Masu ilimin gane taurarin ba su ziyarci Yesu a daren da aka haife shi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da suka shiga gidan kuwa sai suka ga ɗan yaron da mamarsa Maryamu.” (Matiyu 2:11) Hakan yana nufin cewa Yesu da iyayensa suna zama a gida kuma Yesu ba jariri ba ne a kwance a abin da ake ba dabbobi abinci.​—Luka 2:16.

 Allah ne ya sa ‘maza masu hikimar’ suka bi “taurari” zuwa Betelehem?

 Wasu mutane sun gaskata cewa Allah ne ya turo tauraro don ya kai masu ilimin gane taurari wurin Yesu. Ka yi la’kari da dalilin da ya sa hakan ba gaskiya ba ne.

  •   Abin da ya fito kamar tauraro ya fara kai masu ilimin gane taurari Urushalima. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wadansu masu ilimin gane taurari daga gabas suka zo Urushalima. Sai suka yi tambaya suka ce, ‘Ina sabon sarkin Yahudawa da aka haifa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, kuma mun zo ne mu yi masa sujada.’”​—Matiyu 2:​1, 2.

  •   Sarki Hirudus ne da farko ba ‘tauraro’ ba ya sa masu ilimin gane taurarin su je Betelehem. Sa’ad da ya ji cewa za a haifi wani “sarkin Yahudawa,” Hirudus ya yi bincike kuma ya gano wurin da aka ce za a haifi Kristi. (Matiyu 2:​3-6) Da ya gano cewa a Betelehem ne, sai ya gaya wa masu ilimin gane taurarin cewa su je wurin su nemi yaron kuma su zo su gaya masa.

     A wannan lokaci ne masu ilimin taurarin suka je Betelehem. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Su kuwa da suka gama jin maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Tauraron da suka gani a gabas kuwa yana gabansu suna binsa har ya zo ya tsaya a kan inda dan yaron yake.”​—Matiyu 2:9.

  •   Bayan mutanen sun ga ‘tauraron’ abubuwa sun faru da suka sa ran Yesu a hadari kuma suka yi sanadiyyar mutuwar yaran da ba su san kome ba. Sa’ad da masu ilimin gane taurarin suka bar Betelehem, Allah ya umurce su cewa kada su koma wurin Hirudus.​—Matiyu 2:12.

 Mene ne Hirudus ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da Hirudus ya gane cewa masu ilimin nan sun yi masa wayo ne, sai ya yi fushi sosai. ya aika a kakkashe dukan ’yan yara maza wadanda suke cikin Betelehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da masu ilimin nan suka fada masa game da yaron.” (Matiyu 2:16) Allah ba zai iya sa wannan mugun abu ya faru ba.​—Ayuba 34:10.

a Wani masanin tarihi dan girka a karni na biyar kafin haihuwar Yesu mai suna Herodotus, ya ce ma’goi a zamaninsu mutanen Midiya da Fasiya ne kuma sun kware a gane taurari da kuma fadan ma’anar mafarki.

b Ka duba New American Standard Bible da New American Bible da New English Bible, da kuma New International Version Study Bible. Littafi Mai Tsarki juyin King James Version ya kira wadannan mutanen “maza masu hikima” amma bai ambata cewa su uku ne ba.