Koma ka ga abin da ke ciki

Yaushe ne Aka Rubuta Labarai Game da Yesu?

Yaushe ne Aka Rubuta Labarai Game da Yesu?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Game da labaran da ya rubuta game da rayuwar Yesu, manzo Yohanna ya ce: “Shi wanda ya gani kuma ya bada shaida, shaidatasa gaskiya ce kuwa: ya sani kuma yana faɗin gaskiya, domin ku kuma ku bada gaskiya.”—Yohanna 19:35.

 Dalili ɗaya da ya sa za a gaskata da labaran Lingila da Matta, Markus, Luka, da kuma Yohanna suka rubuta shi ne cewa an rubuta su yayin da waɗanda suka shaida abubuwan da suka faru suke da rai. Wasu sun ce, an rubuta Lingilar Matta ne shekara takwas bayan mutuwar Kristi, wato, a misalin shekara ta 41 a Zamaninmu. Ɗalibai da yawa kuma sun ce a wani kwanan wata dabam ne , amma galibin mutane sun amince cewa an rubuta dukan Nassosin Hellenanci na Kirista a ƙarni na farko a Zamaninmu ne.

 Mutanen da suka ga Yesu sa’ad da yake duniya kuma suka shaida mutuwarsa da kuma tashinsa daga matattu sun tabbatar da labaran Lingila. Ai da sun nuna kuskurensa idan da akwai wani. Farfesa F. Bruce ya ce: “Abu mafi kyau game da wa’azin manzannin shi ne cewa masu sauraron sun san abin da ake faɗi; ba kawai suna cewa, ‘Mu shaidu ne na abubuwan da ya faru,’ amma ‘yadda ku kanku kuka sani ne’ (Ayukan Manzanni 2:22).”