Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Dabbar Slug na da Gansakuka Mai Kama da Gam

Dabbar Slug na da Gansakuka Mai Kama da Gam

 Tun da dadewa, likitoci masu yin tiyata suna neman gam da zai taimaka musu sa’ad da suke tiyata da kuma warkar da rauni. Ba shi da kyau a saka gam da yawa da ake amfani da su yanzu a cikin jiki. Suna da guba kuma sukan yi karfi sa’ad da suka bushe. Ban da haka, ba sa mannewa a kan abin da bai bushe ba. Masanan kimiyya sun gano hanyar da za su magance wannan matsala ta wajen bincika gamsakukar dabbar da ake kira slug. a

 Alal Misali: Idan dabbar slug ta ji kamar za a kawo mata hari, sai ta fito da gamsakuka mai kauri da za ta iya rike dabbar a kan ganye da bai bushe ba. Wannan gamsakuka tana kāre dabbar slug, kuma har ila za ta iya yin tafiya ta jujjuya jikinta ba tare da wata matsala ba.

 Masu bincike sun yi bincike a kan wannan gamsakuka kuma suka gano abubuwa da yawa da suka sa take rike abubuwa sosai. Alal misali, gamsakukar tana amfani da sinadarai biyu da ke jawo da kuma rike abu. Tana shiga wurin da dabbar ta manne kanta kuma ta bude kamar roba sa’ad da abu ya matse ta. Ta wajen kera wani abu da ke dauke da sinadarai na gamsakukar dabbar slug, masu bincike sun kirkiro wani gam mai karfi sosai fiye da wanda likitoci ke yin amfani da shi a yanzu. Kuma tana iya manne wa abu mai rai. An ce za ta iya manne wa gabobi “kamar yadda guringuntsi yake manne wa kashi.”

 Masana sun gaskata cewa kowane likita mai yin tiyata zai bukaci wannan gam ya rika kasancewa a cikin kayan aikinsa. Hakan zai sa a daina dinka jikin mutum sa’ad da aka yi masa tiyata ko kuma yin amfani da wayoyi sa’ad da aka yi tiyatar. Za a iya yin amfani da shi don warkar da guringuntsi ko kuma a manne wasu na’urorin jinya a cikin jiki. Gwaje-gwaje da aka yi sun nuna cewa an riga an yi nasara wajen yin amfani da gam don rufe ramin da ke zuciyar alade. Kuma an yi amfani da shi wajen rufe ramuka da ke hantar bera.

 Sau da yawa masana suna samun hanyoyi mafi kyau na magance matsaloli ta wajen bincika halittu da ke duniya. Wani darektan makarantan da ke kera gam manne abubuwa mai suna Donald Ingber ya ce: “Kana bukatar sanin wurin da za ka duba da kuma yin amfani abin da ka binciko.”

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa gam na gamsakukar dabbar slug sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?

a Wani suna da ake kiran dabbar shi ne Arion subfuscus