Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Gam Din Wani Abu Mai Kama da Dodon Kodi

Gam Din Wani Abu Mai Kama da Dodon Kodi

 Tun da dadewa, masanan dabbobi sun lura cewa wasu abubuwa masu rai da ke kama da dodon kodi suna iya makalewa gam-gam a jikin duwatsu da ginshikin gada da kuma karkashin jirgin ruwa. Gam na wannan dabbar da ke kama da dodon kodi ya fi duk wani abu da ’yan Adam suka taba yi karfi manne wa abubuwa. Bai dade ba da masana suka koyi yadda wannan abu mai rai ke iya mannewa ga abin da ke jike.

 Alal misali: Bincike da aka yi ya nuna cewa wadannan abubuwa masu rai suna bincika wurare dabam-dabam kafin su zaba wurin da za su makale. Masana sun gaskata cewa bayan sun zabin wurin da za su makale, sai su yi amfani da sinadarai iri biyu a wuraren. Na farko shi ne wani abu mai kama da māi da suke amfani da shi don su hana ruwa shiga wurin da suke so su makale. Kari ga haka, mān yana shirya wurin don ya sa sinadari na biyun ya manne wa abun. Sinadari na biyu yana dauke da abubuwan gina jiki da ake kira phosphoproteins.

 Wadannan sinadarai biyu suna hada gam mai karfi da kwayar cuta ba ta iya kashewa. Yana da muhimmanci gam ya yi karfi sosai domin wurin ne wannan abu mai rai da ke kama da dodon kodi zai kasance muddar ransa.

Abubuwa masu rai da ke kama da dodon kodi da kuma igiyoyin gam da suke yi

 Yadda wannan abu mai rai ke yin gam ya fi abin da masana suke tunaninsa a dā. Wani da ke cikin rukunin da suka gano wannan tsarin ya ce: “Hanya mai kyau ce na magance yadda ruwa ke hana gam manne wa abubuwa.” Wannan binciken zai iya taimaka wa masu bincike su yi gam da za a yi amfani da shi a cikin ruwa. Ban da haka, zai taimaka don a yi gam da za a iya yin amfani da shi a abubuwa da ke amfani da wutar lantarki. Kuma likitoci za su iya yin amfani da gam don manne abu a jiki.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa gam na abu mai rai da ke kama da dodon kodi sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?