Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Wata Babban Dabbar Ruwa Mai Fata da ke Tsabtace Kanta

Wata Babban Dabbar Ruwa Mai Fata da ke Tsabtace Kanta

 Wasu abubuwa da ke kama da dodon kodi na makalewa a karkashin jirgin ruwa kuma hakan na jawo wa jirgin matsala sosai. Yana hana jiragen gudu kuma yana sa su shan māi sosai. Ban da haka, a kan sa jiragen su daina aiki bayan wasu shekaru don a tsabtace jikinsu. Amma masanan kimiyya sun kwaikwayi halittun da ke cikin ruwa domin hakan zai taimaka musu su magance wannan matsalar.

 Alal misali: An binciko cewa wani irin babban dabba da ake kira pilot whale tana iya tsabtace fatarta. Jikin dabbar yana da kananan layi, wadannan kananan layin suna hana wasu abubuwa masu rai makalewa a jikin dabbar don babu wurin makalewa. Dabbar na da wani irin māi da ke cika layoyin da ke jikinta kuma wannan mān yana kashe duk wani gamsakuka da kuma kwayoyin cuta da suka makale a jikinta. Wannan dabbar tana fitar da sabon māi yayin da take tsabtacce jikinta.

 Masanan kimiyya suna shirin kwaikwayon yadda wannan dabbar ke tsabtace kanta don su kera karkashin jirgin ruwa a wannan hanyar. A dā ana amfani da wani irin fenti da ake shafawa a karkashin jirgi. Amma a kwanan nan, an hana yin amfani da wannan fenti domin guba ne ga abubuwa masu rai da ke cikin ruwa. Masu bincike sun ce za su magance matsalar ta wajen rufe ramuka da ke karkashin jirgin ruwa da ƙarafa masu sinadarai da ba guba. Wadannan sinadaran ko magunguna marasa guba sukan zama māi mai kauri a cikin ruwa, kuma zai rufe karkashin jirgin gabaki daya. Da shigewar lokaci, ruwa zai wanke wannan māi mai kaurin kusan inci guda, kuma duk abubuwan da suka makale a jikin jirgin zai fita. Bayan hakan, sai na’urar ta saka sabon māi don ta rufe karkashin jirgin ruwan.

Abubuwa masu makalewa a karkashin jirgin ruwa sukan sa ba ya gudu sosai kuma suna da wuyan cirewa

 Gwaje-gwajen da aka yi sun nuna cewa wannan tsarin zai rage yawan abubuwan da ke mannewa a karkashin jiragen ruwa zuwa ninki 100. Kuma kamfanoni masu tura abubuwa zuwa wurare dabam-dabam za su amfana, domin sukan kashe kudi sosai sa’ad da suka kawo jirgin ruwa zuwa gabar teku don su wanke ko kuma tsabtace shi.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda dabbar pilot whale take tsabtace kanta sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce ta?