Koma ka ga abin da ke ciki

Bayanai Game da Yadda Muke Amfani da Cookies da Kuma Wasu Fasahohi Irin Wannan

Bayanai Game da Yadda Muke Amfani da Cookies da Kuma Wasu Fasahohi Irin Wannan

Kamar yadda yake da wasu dandalin yanar gizo, idan ka shiga wannan dandalin, wayarka ko kwamfutarka ta hannu ko kuma kwamfutarka tana iya tara wasu bayanai ta wajen yin amfani da cookies ko abin da ke lura da ayyukan masu shiga dandalin yanar gizo wato web beacons ko kuma wasu fasahohi dabam. Kalmar nan “cookies” da za mu bayyana a wannan Tsare Sirrin ya hada da abubuwan fasaha kamar localStorage wato wurin adana bayanai na kwamfuta. Cookies yana taimaka mana mu inganta dandalinmu ta wajen nuna mana yadda mutane ke amfani da dandalin. Muna amfani da bayanan nan don inganta dandalin. Ba ma kokarin sanin dukan mutanen da suka ziyarci dandalinmu sai dai in suna so mu yi hakan ta wajen cika fom a dandalin ko kuma a cikin manhajar da suke dandalin.

Cookies. Da akwai cookies da yawa da suke yin abubuwa dabam-dabam don su sa ka ji dadin bincika yanar gizo. Muna yin amfani da cookies don mu san ko ka taba ziyarta dandalinmu ko kuma mu san abubuwan da ka zaba a lokacin da ka shiga dandalin. Alal misali, muna iya yin amfani da cookies don mu tuna yaren da ka zaba a lokacin da ka shiga dandalin. Ba ma yin amfani da cookies don yin tallace-tallace.

Ana iya bayyana irin cookies da muke amfani da shi a wannan dandalin ta hanyoyi uku:

  1. Wadanda Ake Bukata. Ana bukatar irin wadannan cookies din domin su ne za su taimaka maka ka iya yin amfani da wasu abubuwa kamar ka shiga ko kuma tura fom a dandalin. Idan babu irin cookies nan ba za ka iya ba da gudummawa don aikinmu a dukan duniya ta yanar gizo ba. Kari ga haka, muna amfani da cookies da ke taimaka mana mu aikata sabi din da kake bukata yayin da kake bincika dandalin. Irin wannan cookies ba sa karban bayanai game da kai don a yi amfani da su don kasuwanci ko kuma don tuna wuraren da ka shiga a yanar gizo.

  2. Cookies da Ake Amfani da Su. Ana amfani da irin wannan cookies din don a tuna irin zabin da ka yi (kamar sunan mai amfani, ko yare, ko kasa) kuma a inganta dandalin don ka ji dadin yin bincike.

  3. Cookies Masu Muhimmanci. Ana yin amfani da irin wadannan cookies din don a san abin da masu ziyartan dandalin suke a dandali, ban da haka, ana amfani da shi don a san ko mutane nawa ne suka ziyarci dandalin da kuma lokacin da suka dauka a dandalin. Ana amfani da wannan bayanin ne don a inganta dandalin kadai.

Wasu cookies din shafinmu ne ya kirkiro don mutumin farko. Wasu kuma masu tanadar da sabis ne. Dandalinmu na amfani da cookies din da muka kirkiro kadai, sai kuma cookies din Google reCAPTCHA. Ana yin amfani da Google reCAPTCHA don a sani ko mutum ya shiga dandalin yanar gizon ko kuma kwamfuta don a gujewa spam da ke sarrafa kansa. Don Allah ka duba tsare sirri na Google a https://www.google.com/intl/en/policies/privacy/.

Abin da ke lura da ayyuka wato Web Beacons. A shafin dandalin kana iya gamuwa da abin da ke lura da ayyuka, wannan abu yana taimaka mana mu adana abubuwan da ka yi a dandalin, kamar yayin da ka bincika wani shafi. Ana amfani da abin lura don a san yadda mutane ke amfani da dandalin da kuma yadda shafuffukan suke aiki.

Amfani da adireshin IP. Adireshin IP shi ne lambar da za ta bayyana wata kwamfuta a cikin intane. Muna yin amfani da adireshin IP da kuma irin nau’in burauzar da kake amfani da shi don mu tantance yadda kake amfani da dandalin, kuma mu bincika ko kana fuskantar wata matsala a dandalin don inganta sabis inda muke ba ka. Amma idan ba ka ba da bayanai game da kanka ba adireshin IP baya bayyana ko wane ne kai.

Zabin da Ka Yi. Sa’ad da ka shiga wannan dandalin mun tura cookies din mu zuwa burauzar kuma an adana su a kwamfutarka. Ta wajen yin amfani da dandalinmu, ka nuna ka amince da yin amfani da cookies da kuma wasu abubuwa kamar haka. Idan ba ka son yi amfani da su, kana iya shiga satin a burauzarka don ka dakatar da shi. Amma ka lura cewa idan ka dakatar da shi, ba za ka iya yi amfani da wasu abubuwa a dandalin ba. Yadda yake share cookies ya bambanta sosai. Za ka iya duba Help menu da ke burauzarka don samun Karin bayani umarnin.