Koma ka ga abin da ke ciki

Ya Koyi Gaskiya Daga Fursunoni

Ya Koyi Gaskiya Daga Fursunoni

 A shekara ta 2011, wani mutum ya yi gudun hijira daga kasar Eritrea zuwa kasar Norway. Sa’ad da Shaidun Jehobah suka je yi masa wa’azi, ya gaya musu cewa ya taba haduwa da Shaidun Jehobah a kasarsu. Mutumin ya ce a lokacin da yake aikin soja a kasarsu, ya lura cewa Shaidun Jehobah da aka saka a kurkuku saboda imaninsu sun ki shiga soja duk da azaba da aka ba su.

 Abin takaici, wani abu ya faru da mutumin da ya sa aka saka shi a kurkuku. A kurkukun, ya hadu da Shaidu guda uku masu suna Paulos Eyasu da Negede Teklemariam da Isaac Mogos da aka saka a kurkuku tun shekara ta 1994 don imaninsu.

 Sa’ad da yake kurkuku, mutumin ya ga cewa Shaidun Jehobah suna aikata abubuwan da suke wa’azi a kai. Ya lura cewa suna fadin gaskiya kuma har suna ba wasu fursunoni abincinsu. Kari ga haka, ya lura da yadda wadannan Shaidun Jehobah da suke kurkuku suke yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare kowace rana kuma suna gayyatar wasu su bi su yin hakan. An ce za a sake su daga kurkuku idan suka amince da su saka hannu cewa ba za su sake bauta wa Jehobah ba, amma sun ki yin hakan.

 Wannan abu ya burge mutumin sosai kuma bayan ya koma Norway, ya yi kokari ya san abin da ya sa Shaidun Jehobah suke da bangaskiya haka. Don haka, sa’ad da Shaidun suka zo wa’azi, nan da nan ya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma ya soma halartan taron.

 A watan Satumba 2018, mutumin ya yi baftisma kuma yanzu shi Mashaidin Jehobah ne. Yanzu yana yin amfani da dukan damar da ya samu don ya yi wa mutanen Eritrea da kuma Sudan wa’azi. Kuma yana karfafa su su yi nazarin Littafi Mai Tsarki don su kasance da bangaskiya.