Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Ba su Mai da Martani Ga Firistocin da Ke Fushi

Shaidun Jehobah Ba su Mai da Martani Ga Firistocin da Ke Fushi

 Wani mai kula da da’ira mai suna Artur, ya kai wa wata ikilisiya a Armeniya ziyara. Ya lura cewa ’yan’uwa a ikilisiyar ba su taba zuwa yin wa’azi ga jama’a da kuma amfani da amalanken wa’azi dauke da littattafai ba. Don ya karfafa su su yi hakan, Artur da matarsa Anna da kuma wani mai suna Jirayr, sun kafa amalanke wa’azi a wani karamin gari. Sun zabi wurin da mutane ke yawan wucewa.

 Nan da nan mutanen da suke wucewa suka soma karban littattafai. Amma ba da dadewa ba ’yan hamayya suka lura da amalanken wa’azin. Firistoci biyu sun zo wurin amalanken kuma suka ture shi kasa. Dayan firist ya share Artur da mari har sai da tabaraunsa ya fadi kasa. Artur da Anna da kuma Jirayr suna yi kokarin kwantar wa firistocin hankali, amma hakan bai cim ma ruwa ba. Firistocin sun ragargaza amalanke da kafarsu kuma littattafan suka bazu a kasa. Bayan sun zazzagi Shaidun sai suka tafi.

 Artur da Anna da kuma Jirayr sun kai kara ofishin ’yan sanda. Sun bayyana abin da ya faru kuma sun yi wa ’yan sandan da kuma wasu a ofishin wa’azi. Sai aka kai su wurin shugaban ’yan sanda. Da farko yana so ne ya san abin da ya faru. Ya ga cewa Artur mutum ne mai karfi amma bai rama sa’ad da aka mare shi ba. Sai ya daina yin tambayoyi game da abin da ya faru kuma ya soma tambayoyi game da imanin Shaidun Jehobah. Sun dauki awa hudu suna tattaunawa! Abin da dan sandan ya ji ya burge shi sosai kuma ya ce: “Kai wannan addini ne mai kyau! Ina son in zama Mashaidin Jehobah!”

Artur da Anna

 Washegari, Artur ya sake komawa wa’azi da amalanke, sai wani mutumin da ya lura da abin da ya faru ya zo wurin Artur. Mutumin ya yaba wa Artur don yadda ya kasance a natse kuma ya ki rama abin da aka yi masa. Mutumin ya kara da cewa abin da firistoci suka yi ya sa ba zai iya girmama su kuma ba.

 Da yamma sai shugaban ’yan sandan ya sake kiran Artur zuwa ofishin ’yan sanda. Amma maimakon su tattauna game da abin da ya faru, ya sake yin wasu tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki. Wasu ’yan sanda biyu sun saka baki a tattaunawar.

 Washegari, sai Artur ya sake ziyartar dan sandar don ya nuna masa bidiyoyi. Shugaban dan sandar ya kira wasu ’yan sanda don su ma su kalli bidiyon.

 Saboda abin da firistocin nan suka yi, an yi wa ’yan sanda da yawa wa’azi a lokaci na farko. Hakan ya sa su kasance da ra’ayin da ya dace game Shaidun Jehobah.