Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Ba Ku Bikin Kirsimati?

Me Ya Sa Ba Ku Bikin Kirsimati?

Kurakuran da ake yawan yi

 Kage: Dalilin da ya sa Shaidun Jehobah ba sa bikin Kirsimati shi ne cewa ba su gaskata da Yesu ba.

 Gaskiya: Mu Kiristoci ne. Mun gaskata cewa za a sami ceto kadai ta wurin Yesu Kristi ne.—Ayyukan Manzanni 4:12.

 Kage: Kuna raba iyalai da koyarwarku cewa kada su yi bikin Kirsimati.

 Gaskiya: Mun damu sosai da iyalai, kuma muna amfani da Littafi Mai Tsarki don mu karfafa su su kasance da hadin kai.

 Kage: Ba ku saka hannu a kyautar da ake bayarwa a lokacin “Kirsimati” da zaman lafiya a duniya, da kuma alheri ga mutane.

 Gaskiya: Muna kokarin kasance da karimci da kuma salama kowace rana. (Misalai 11:25; Romawa 12:18) Alal misali, yadda muke tafiyar da taronmu da kuma wa’azi da muke yi daidai ne da umurnin Yesu: “Kyauta kuka karba, sai ku bayar kyauta.” (Matta 10:8) Ban da haka, muna karfafa mutane su kasance da bege na gaske na kawo salama a duniya wato Mulkin Allah.—Matta 10:7.

Me ya sa Shaidun Jehobah ba sa bikin Kirsimati?

  •   Yesu ya ba da umurnin mu tuna da mutuwarsa, ba haihuwarsa ba.—Luka 22:19, 20.

  •   Manzannin Yesu da almajiransa na farko ba su yi bikin Kirsimati ba. Kundin New Catholic Encyclopedia ya ce “asalin tushen bikin an soma shi ne tun kafin shekara ta 243 bayan haihuwar Yesu,” wato fiye da karni guda bayan mutuwar manzo na karshe.

  •   Babu tabbaci cewa an haifi Yesu a ranar 25 ga Disamba; babu kwanan watan haihuwarsa cikin Littafi Mai Tsarki.

  •   Mun tabbata Allah bai aminci da Kirsimati ba domin daga al’adun arna ne da bukukuwansu.—2 Korintiyawa 6:17.

Me ya sa ba ku a yin Kirsimati ba?

 Mutane da yawa har yanzu suna bikin Kirsimati duk da sanin cewa tushensa daga arna ne kuma Littafi Mai Tsarki bai goyi bayansa ba. Irin mutanen nan za su iya tambaya: Me ya sa Kiristoci za su ki da farin jinin nan? Me ya sa ba za su yi bikin ba?

 Littafi Mai Tsarki ya karfafa mu mu yi tunani, mu yi amfani da ‘azancinmu.’ (Romawa 12:1, 2) Ya koya mana mu daraja gaskiya. (Yohanna 4:23, 24) Saboda haka, ko da muna son wasu, muna bin ka’idodin Littafin Mai Tsarki ko idan ba mu da farin jini.

 Ko da yake mun zabi ba za mu yi bikin Kirsimati ba, muna daraja yancin da kowane mutum ya tsai da shi game da wannan batun. Kuma ba ma kushe su domin suna yin bikin.