Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ra’ayin Shaidun Jehobah Game da Jana’iza?

Mene ne Ra’ayin Shaidun Jehobah Game da Jana’iza?

 Muna bin koyarwar Littafi Mai Tsarki a batun jana’iza kuma hakan ya kunshi wadannan abubuwa:

  •   Ya dace mutum ya yi makoki idan aka yi masa rasuwa. Almajiran Yesu sun yi makoki sa’ad da aka yi musu rasuwa. (Yohanna 11:33-35, 38; Ayyukan Manzanni 8:2; 9:39) Saboda haka, ba ma daukan jana’iza cewa lokacin yin liyafa ne. (Mai-Wa’azi 3:1, 4; 7:1-4) Maimakon haka, muna daukan ta a matsayin lokacin nuna juyayi.—Romawa 12:15.

  •   Matattu ba su san kome ba. Ko daga wace kabila ko al’ada ce muka fito, muna guje wa kowace koyarwar da take nuna cewa matattu sun san abubuwan da ke faruwa kuma suna iya rinjayar masu rai. (Mai-Wa’azi 9:5, 6, 10) Al’adu kamarsu kwanan zaune, bukukuwa na jana’iza, tuna lokacin mutuwa, hadayu ga matattu, da kuma takaba. Muna guje wa dukan wadannan al’adu da ayyuka don muna bin umurnin Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Ku ware [kanku] . . . Kada ku taba kowane abu marar-tsarki.”—2 Korintiyawa 6:17.

  •   Matattu suna da bege. Littafi Mai Tsarki ya ce za a ta da matattu daga mutuwa kuma lokaci yana zuwa da mutane ba za su mutu kuma ba. (Ayyukan Manzanni 24:15; Ru’ya ta Yohanna 21:4) Wannan begen yana taimaka mana mu guji wuce gona da iri sa’ad da aka yi mana rasuwa, kamar yadda ya taimaki Kiristoci na karni na farko.—1 Tasalonikawa 4:13.

  •   Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi abubuwa daidai wa daida. (Misalai 11:2) Ba mu gaskata ba cewa jana’iza lokacin nuna arziki ko kuma wadatarmu ba ne. (1 Yohanna 2:16) Ba ma shirya babbar liyafa a lokacin jana’iza don mutane su sakata su wala ko kuma mu saya akwati mai tsada sosai ko mu saka kaya na a zo a gani don mu burge mutane.

  •   Ba ma tilasta wa mutane su bi imaninmu game da jana’iza. Muna bin ka’idar da ta ce: “Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Romawa 14:12) Amma, muna kokari mu bayyana wa mutane imaninmu “da ladabi da tsoro” idan muka sami damar yin hakan.—1 Bitrus 3:15.

Yaya Shaidun Jehobah suke yin jana’iza?

 Wuri: Idan iyali suka tsai da shawara cewa za a yi jana’iza, za a yi hakan a wurin da iyalin suka zaba, kamar Majami’ar Mulki ko gidan da aka shirya don yin jana’iza ko wurin da ake kona gawa ko wurin bizina ko kuma a wani wuri dabam.

 Jawabi: Ana ba da jawabi don a yi wa wadanda aka yi musu rasuwa ta’aziyya ta wurin bayyana musu abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da mutuwa da kuma begen tashi daga mutuwa. (Yohanna 11:25; Romawa 5:12; 2 Bitrus 3:13) Jawabin jana’izar zai tuna wa mutane halaye masu kyau na wanda ya rasu, kuma a nuna darussa da za a koya daga misalinsa na kasancewa da aminci ga Allah.—2 Sama’ila 1:17-27.

 Za a rera waka da aka dauko daga Nassosi. (Kolosiyawa 3:16) Za a kammala jawabin da addu’a mai ban karfafa.—Filibiyawa 4:6, 7.

 Karban kudi: Ba ma karban kudi daga mambobinmu don ayyuka na addini har da jana’iza kuma ba ma karban kudi a taronmu.—Matta 10:8.

 Mahalarta: Wadanda ba Shaidu ba suna iya halartar jana’iza da aka yi a Majami’ar Mulki. Kamar taronmu, mutane sukan halarci jana’iza.

Shaidu suna iya halarta jana’iza da wasu addinai suke yi ne?

 Kowane Mashaidi zai tsai da shawara ko zai yi hakan ko ba zai yi ba. (1 Timotawus 1:19) Amma ba ma saka hannu a bukukuwan addini da ba su jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ba.—2 Korintiyawa 6:14-17.