Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Suna Raba Kan Iyalai Ne ko Suna Sa Su Zauna Lafiya?

Shaidun Jehobah Suna Raba Kan Iyalai Ne ko Suna Sa Su Zauna Lafiya?

 Mu Shaidun Jehobah muna iya kokari mu zauna lafiya da iyalanmu kuma mu taimaka wa mutane su yi hakan. Muna daukaka Allah wanda ya kafa dukan iyalai. (Farawa 2:​21-24; Afisawa 3:​14, 15) Allah ya ba da ka’idodi a Littafi Mai Tsarki don ya koya wa mutane a duk duniya yadda za su zauna lafiya a iyalinsu kuma su yi farin ciki.

Yadda Shaidun Jehobah Suke Inganta Zaman Iyali

 Muna iya kokarinmu mu bi shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki don suna taimaka mana mu zama maza da mata da kuma iyayen kirki. (Karin Magana 31:​10-31; Afisawa 5:22–6:4; 1 Timoti 5:8) Ka’idodin da ke Littafi Mai Tsarki suna taimaka wa iyalan da ba sa bin addini daya su zauna lafiya. (1 Bitrus 3:​1, 2) Ga abin da wasu da ba Shaidun Jehobah ba amma matansu ko mazansu sun zama Shaidun Jehobah suka ce:

  •   Wani mai suna Clauir daga Brazil ya ce, “Bayan aurenmu, mun yi shekaru shida muna ta samun sabani sosai. Amma da matata Ivete ta zama Mashaidiyar Jehobah, sai ta zama mai hakuri da nuna kauna sosai fiye da dā. Yadda ta gyara halinta ne ya sa ba mu rabu ba.”

  •   Wata mai suna Agness daga Zambiya ta ce, “Ban ji dadi ba da maigidana Chansa ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, domin na dauka za su sa mu sami sabani a iyalinmu. Amma daga baya, na lura cewa nazarin da yake yi ne ya inganta zaman aurenmu.”

 Yayin da muke wa’azi, mukan nuna wa mutane yadda bin shawarar da ke Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka musu su

Canja addini yana kawo matsala a aure ne?

 E, hakan yana faruwa a wasu lokuta. Alal misali, a shekara ta 1998, wani kamfanin bincike mai suna Sofres ya ba da rahoto cewa, iyali 1 cikin iyalai 20 da abokin auren ya zama Mashaidi sun sami matsala sosai a aurensu lokacin da hakan ya faru.

 Yesu ya ce a wasu lokuta, wadanda suka bi koyarwarsa za su fuskanci matsaloli a iyalinsu. (Matiyu 10:​32-36) Wani masanin tarihi mai suna Will Durant ya ce a lokacin Mulkin Romawa, “an zargi Kiristoci da raba kan iyalai,” a kuma irin zargin da ake wa wasu Shaidun Jehobah a yau ke nan. Amma shin, wanda ya zama Mashaidin ne yake janyo tashin hankali a iyalin?

Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam

 Da Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam yake yanke hukunci a kan zargin da ake yi wa Shaidun Jehobah cewa suna raba kan iyalai, kotun ya ce sau da yawa, wadanda ba Shaidun Jehobah ba sukan tā da rikici ta wajen kin “amincewa da kuma daraja ’yancin da danginsu suke da shi na zaban addinin da suke so su bi.” Kotun ya dada cewa: “Dukan ma’auratan da addininsu ba daya ba sukan fuskanci wannan matsalar, ba Shaidun Jehobah kadai ba.” b Amma ko da an ki Shaidun Jehobah domin imaninsu, suna iya kokari su bi shawarar Littafi Mai Tsarki da ta ce: “Idan wani ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. . . . Ku yi iyakar kokarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.”​—Romawa 12:​17, 18.

Abin da ya sa Shaidun Jehobah suka yi imani cewa ’yan addininsu ne kadai ya dace su aura

 Shaidun Jehobah suna bin umurnin Littafi Mai Tsarki cewa su auri “mai bin Ubangiji” kadai, wato wadanda suke da imani daya da su. (1 Korintiyawa 7:39) Wannan umurnin daga Littafi Mai Tsarki ne kuma yana da amfani sosai. Alal misali, a 2010, an rubuta wani talifi a mujallar nan Journal of Marriage and Family da ta ce, “ma’aurata da suke bin addini daya kuma suna da imani daya” sun fi samun zaman lafiya a aurensu. c

 Duk da haka, Shaidun Jehobah ba sa karfafa ’yan’uwansu masu bi su rabu da abokan aurensu da ba Shaidu ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan wani dan’uwa yana da mace marar bi, ta kuma yarda su zauna tare, to, kada ya rabu da ita. Idan kuma wata mace tana da miji marar bi, ya kuwa yarda su zauna tare, to, kada ta rabu da shi.” (1 Korintiyawa 7:​12, 13) Umurnin da Shaidun Jehobah suke bi ke nan.

a Ka duba littafin nan Caesar and Christ, shafi na 647.

b Ka ga hukuncin da aka yanke a takardar shari’ar nan Jehovah’s Witnesses of Moscow and Others v. Russia, shafuffuka na 26-​27, sakin layi na 111.

c Ka duba mujallar nan Journal of Marriage and Family, Volume 72, Number 4, (August 2010), shafi na 963.