Koma ka ga abin da ke ciki

Su Waye ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?

Su Waye ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?

 Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah wani karamin rukunin Kiristoci ne masu aminci da suke ja-gorantar ayyukan Shaidun Jehobah a fadin duniya. An raba ayyukansu zuwa kashi biyu:

  •   Su ne suke kula da abubuwan da ake koyarwa a littattafai da taro da kuma makarantun Shaidun Jehobah.—Luka 12:42.

  •   Suna kula da ayyukan Shaidun Jehobah a fadin duniya ta wajen ba da ja-goranci a wa’azin da muke yi da kuma kula da kudade.

 Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suna bin gurbin da “manzanni da dattawa” a Urushalima suka kafa a karni na farko, wadanda suka yanke muhimman shawarwari a madadin dukan Kiristoci a lokacin. (Ayyukan Manzanni 15:2) Kamar wadannan mazaje masu aminci, mambobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ba shugabannin kungiyarmu ba ne. Suna bin ja-gorancin da Littafi Mai Tsarki ya bayar, kuma sun ba da gaskiya cewa Jehobah Allah ya nada Yesu Kristi ya zama Shugaban ikilisiya.—1 Korintiyawa 11:3; Afisawa 5:23.

Su wane ne mambobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?

 Mambobin Hukumar su ne: Kenneth Cook, Jr., Samuel Herd, Geoffrey Jackson, Stephen Lett, Gerrit Lösch, Anthony Morris III, Mark Sanderson, da kuma David Splane. Suna hidima a hedkwatar Shaidun Jehobah a Warwick, jihar New York, a Amirka.

Yaya aka tsara Hukumar?

 Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta kafa kwamitoci shida da za su kula da ayyuka dabam-dabam da muke yi, kuma kowane mamba na Hukumar yana hidima a daya daga cikin kwamitocin ko fiye da haka.

  •   Kwamitin Masu Tsara Ayyuka: Yana kula da batutuwan da suka shafi shari’a da ba da agaji a lokacin bala’i, da taimakawa sa’ad da ake tsananta wa Shaidun Jehobah domin imaninsu, da batutuwan gaggawa da suka shafi Shaidun Jehobah.

  •   Kwamiti Mai Kula da Ma’aikata: Yana kula da batutuwan da suka shafi masu hidima a ofisoshinmu.

  •   Kwamitin Buga Littattafai: Yana kula da buga littattafai da aika su, da gina wuraren da muke ibada da ofisoshin fassara da kuma gine-ginen reshen ofisoshinmu.

  •   Kwamitin Hidima: Yana kula da ayyukan da suka shafi yin wa’azin Mulkin Allah.—Matiyu 24:14.

  •   Kwamitin Koyarwa: Yana kula da kuma shirya bayanai da ake tattaunawa a taronmu, da makarantunmu, da kuma shirye-shiryen bidiyo da sauti.

  •   Kwamitin Rubuce-rubuce: Yana kula da shirya bayanai da ake bugawa a littattafai da wadanda ake sakawa a dandalinmu, yana kuma kula da ayyukan fassara.

 Kari ga ayyukan da wadannan kwamitocin suke yi, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah takan yi taro a kowane mako don ta tattauna bukatun kungiyarmu. A wannan taron, mambobin Hukumar sukan tattauna abin da Nassosi suka ce, kuma yayin da suke yanke shawarwari, suna barin ruhun Allah ya yi musu ja-goranci don su kasance da ra’ayi daya.—Ayyukan Manzanni 15:25.

Su wane ne mataimakan Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?

 Wadannan Kiristoci ne masu aminci da suke taimaka wa kwamitocin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. (1 Korintiyawa 4:2) Suna da kwarewa da iyawa a ayyukan da suke yi a kwamitin da suke hidima, kuma suna halartan taron da kwamitin ke yi a kowane mako. Ko da yake ba sa yanke shawarwari, amma sukan ba da bayanai da shawarwari masu amfani, da tabbatar da cewa an bi shawarwarin kwamitin, kuma sukan lura da sakamakon da aka samu daga shawarwarin. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu takan ba wa mataimakanta aikin ziyartar ’yan’uwa a wasu kasashe, ko ba da jawabai a taron shekara-shekara ko a bikin sauke karatun makarantar Gilead.

MATAIMAKAN

Kwamiti

Suna

Masu Tsara Ayyuka

  • Ekrann, John

Mai Kula da Ma’aikata

  • Grizzle, Gerald

  • LaFranca, Patrick

  • Molchan, Daniel

  • Walls, Ralph

Buga Littattafai

  • Butler, Robert

  • Corkern, Harold

  • Glockentin, Gajus

  • Gordon, Donald

  • Luccioni, Robert

  • Reinmueller, Alex

  • Sinclair, David

Hidima

  • Breaux, Gary

  • Dellinger, Joel

  • Hyatt, Seth

  • Mavor, Christopher

  • Perla, Baltasar, Jr.

  • Turner, William, Jr.

  • Weaver, Leon, Jr.

Koyarwa

  • Curzan, Ronald

  • Flodin, Kenneth

  • Malenfant, William

  • Noumair, Mark

  • Schafer, David

Rubuce-rubuce

  • Ciranko, Robert

  • Mantz, James

  • Marais, Izak

  • Martin, Clive

  • Myers, Leonard

  • Smalley, Gene

  • van Selm, Hermanus