Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Suke Koma Wajen Mutanen da Suka Ce Ba Sa So Su Saurari Wa’azinsu?

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Suke Koma Wajen Mutanen da Suka Ce Ba Sa So Su Saurari Wa’azinsu?

 Shaidun Jehobah suna kai wa makwabtansu bisharar Mulkin Allah, har da wadanda suka ce ba sa so su saurari wa’azinsu domin suna kaunar Allah da kuma makwabtansu. (Matta 22:37-39) Yadda muke kaunar Allah ne yake sa mu bi umurnin da Dansa ya bayar cewa mu “yi ma jama’a wa’azi.” (Ayyukan Manzanni 10:42; 1 Yohanna 5:3) Idan muna so mu cika wannan wa’adin, wajibi ne mu yi wa mutane wa’azi fiye da sau daya kamar yadda annabawan Allah suka yi a dā. (Irmiya 25:4) Muna yi wa makwabtanmu wa’azin ‘bishara ta mulki’ duk da wadanda a dā ba sa so su ji bisharar domin muna kaunarsu.​—Matta 24:14.

 Idan muka koma gidajen da a dā masu gidan suka ce ba sa so su ji wa’azi, mukan iske wadanda suke so su saurara. Ga dalilai uku da suke sa hakan ya faru:

  •   Mutane sukan kaura daga inda suke zuwa wani wuri dabam.

  •   Wadansu da suke cikin gidan za su so su ji wa’azinmu.

  •   Mutane suna iya canja ra’ayinsu. Canjin yanayin rayuwa yana iya sa wasu su nemi yadda za su kulla dangantaka da Allah, don haka, sukan saurari wa’azin da muke yi. (Matta 5:3) Wadanda suka ki jin wa’azinmu a dā za su iya canja ra’ayinsu kamar yadda ya faru da manzo Bulus.​—1 Timotawus 1:13.

 Amma ba ma tilasta wa mutane su ji wa’azin da muke yi. (1 Bitrus 3:15) Kowane mutum yana da ’yancin ya zaɓi yadda zai yi ibada.​—Kubawar Shari’a 30:19, 20.