Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotuna na 7 na Ofishin Birtaniya (Satumba 2018 Zuwa Fabrairu 2019)

Rumbun Hotuna na 7 na Ofishin Birtaniya (Satumba 2018 Zuwa Fabrairu 2019)

A wannan rumbun hotunan, za ka ga yadda aka gudanar da aiki a sabon ofishin Shaidun Jehobah a Birtaniya a tsakanin Satumba 2018 da kuma Fabrairu 2019.

  1. Sutudiyo da Ke Arewacin Ofishin

  2. Sutudiyo da Ke Kudancin Ofishin

  3. Ofisoshi

  4. Gidan Zama na A

  5. Gidan Zama na B

  6. Gidan Zama na C

  7. Gidan Zama na D

  8. Gidan Zama na E

  9. Gidan Zama na F

25 ga Satumba 2018​—Gidan Zama na A

Ma’aikata suna amfani da motocin tona kasa guda biyu don su saka bututun ruwa a wurin da ya kamata. Ana iya ganin ginin ofisoshi a can kasa.

26 ga Satumba 2018​—Sutudiyo da Ke Kudancin Ofishin

Ma’aikatan suna saka bangon ginin. An tsara kalar bangon da kuma yadda yake don ya jitu da kalar bishiyoyi da kuma ciyayi da ke kewaye da ginin.

27 ga Satumba 2018​—Sutudiyo da Ke Kudancin Ofishin

Bayan ma’aikatan sun yi daben, sun yi amfani da irin mashin don su sa ya yi sumul ya rika kyalli kuma ya dade.

4 ga Oktoba 2018​—Ofisoshi

Hoton da aka dauka daga arewa maso gabashin wurin da ake ginin. A can kasa, ma’aikata suna kwashe abubuwa don a gina gareji na wurin karban baki. An kammala gina hanyar da ta hada ginin ofisoshi biyun da ke dama a hoton. An iya ganin sutudiyo da ke arewaci da kuma kudancin ofishin a can kasa.

10 ga Oktoba 2018​—Wurin aikin

A kusa da Gidan Zama na A, wata mai bincike tana bincika da kuma rubuta aikin da masu tsara yanayin kasa suka yi. Domin na riga da na tsara yadda yanayin kasar za ta kasance kafin a soma ginin, an shuka bishiyoyi da kuma ciyayi, kuma za su girma kafin a kammala ginin.

31 ga Oktoba 2018​—Gidan Zama na F

Masu fenti suna fenta kasan garejin da fentin da aka yi da karo. Daya cikinsu ta saka takalmin da ba zai bata daben ba. Fentin da aka yi da karo yana da kyau domin yana hana māi bata daben kuma hakan ya dace a wurin da za a rika faka motoci.

6 ga Nuwamba, 2018​—Sutudiyo da Ke Kudancin Ofishin

Masu aikin famfo suna yanka sarka da za a yi amfani da ita don rataye abin da zai rika dumama wurin da ake aiki.

6 ga Nuwamba, 2018​—Ofisoshi

Masu fenti sun soma yin fentin farko a cikin ofisoshin. Kowane ofishi yana da iyakwandishan da da aka rufe da leda don a kāre shi.

8 ga Nuwamba, 2018​—Ofisoshi

Ma’aikata suna saka firam a saman wurin da za a rika karban baki.

7 ga Disamba, 2018​—Ofisoshi

Ma’aikata suna amfani da motar daga kaya don su saka bangon gilashi a wajen dakin cin abinci da kuma wurin taro.

10 ga Disamba, 2018​—Ofisoshi

Ma’aikatan wutan lantarki suna saka soket a bakin waya. An saka waya mai nisan kilomita 50 a kowane bene hudu da ke ginin, gabaki daya an yi amfani da waya mai nisan kilomita 200. An tsara daben a hanyar da zai sauki a canja tsarin a nan gaba.

26 ga Disamba, 2018​—Gidan Zama na A

Masu Ba da Taimakon Gaggawa suna koyan abin da za su yi sa’ad da wani ya fado daga saman gida idan igiyar da ya daure kansa da ita ta rike shi.

8 ga Janairu, 2019​—Ofisoshi

Wata ’yar’uwa tana gwada daidai lebur na hanyar wucewa kafin a zuba kankare. A kusa da hanyar wucewar, wata motar tana tona rami don a shuka bishiyoyi.

9 ga Janairu, 2019​—Sutudiyo

Hotunan yadda aka saka abubuwan da ke mayar da hasken rana wutan lantarki a saman rufin sutudiyon da kuma ofisoshi.

17 ga Janairu, 2019​—Ofisoshi

Wani ma’aikaci yana saka tayil a wurin karban baki mai hawa uku. An saka wani abu mai kalar ruwan lemu a karkashin tayil din don ya taimaka kuma ya kāre tayil din don kada ya rika fashewa.

21 ga Janairu, 2019​—Wurin aiki

Ma’aikata suna diban abinci kuma suna ci a dakin cin abinci da aka gina don a yi amfani da shi na dan lokaci. A wannan dakin cin abinci ana ba da abinci sau uku don a iya ciyar da mutane kusan dubu daya a kowace rana.

30 ga Janairu, 2019​—Ofisoshi

Motar kwashe shara yana kwashe dattin da ke bayan ofisoshin. An saka wani irin labule a hanyar wucewa da wundon ofisoshi da ke dakin cin abinci da kuma wurin taro don ya rika kāre mutane daga hasken rana.

30 ga Janairu, 2019​—Ofisoshi

Ma’aikata suna saka tayil kuma ’yan’uwan da suka ba da kai don su taimaka da aikin na kwana daya suna taya su aiki. Ta wannan tsarin ba da kai, ana gayyatar ’yan’uwa daga ikilisiyoyi a Birtaniya da kuma Ireland don su turo mutanen da za su zo su taimaka da aikin na kwana daya. A karshen watan Fabrairu, fiye da ’yan’uwan 5,500 sun saka hannu a wannan aikin.

12 ga Fabrairu, 2019​—Sutudiyo da Ke Kudancin Ofishin

Ma’aikata suna gina bango don su raba ginin kashi biyu. Abubuwa masu kalar ruwan lemu suna nuna iyakacin wurin da motocin daga abubuwa da ke amfani da su za su iya kai wa.

20 ga Fabrairu, 2019​—Ofisoshi

Ma’aikata suna share wurin da ake aikin kuma ana saka tayil a wurin karban baki.