Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotuna 2 a Kasar Filifin (Yuni 2015 Zuwa Yuni 2016)

Rumbun Hotuna 2 a Kasar Filifin (Yuni 2015 Zuwa Yuni 2016)

Shaidun Jehobah na kasar Filifin sun kammala wani babbar aikin gyara da suka yi a ofishinsu a birnin Quezon. Za ka ga yadda aka yi aikin da kuma yadda masu ba da kai suka tallafa wa aikin tsakanin Yuni 2015 zuwa Yuni 2016 a cikin wannan hotunan. An gama gyare-gyaren bayan ’yan watanni, za a iya amfani da su yanzu, kuma an yi hidimar kebe su ga Jehobah a Fabrairu 2017.

Yadda ofishin Shaidun Jehobah da ke Filifin yake bayan an kammala shi. Gidajen da aka gina ko kuma yi musu gyara sun kunshi:

  • Gini na 4 (Masauki)

  • Gini na 5 (Wurin Daukar Murya/Da Bidiyo, Sashen da Ke Kula da Hidima)

  • Gini na 6 (Sashen Kula da Mahalli, Wurin Gyara Motoci, Inda Ake Aikin Walda)

  • Gini na 7 (Sashen Kwamfuta, Wurin Aikin Zane-zane/Da Gine-gine, Wurin Gyare-gyare, Inda Ake Lodin Littattafai, Sashen Fassara)

15 ga Yuni, 2015​—Filin Gini a Birnin Quezon

Masu aikin kankare suna gina hanyar da za a bi daga gini na 1 zuwa gini na 2 da gini na 7.

15 ga Yuni, 2015​—Gini na 5

Kafin su fara aiki, masu aikin kafinta suna duban zane zanen da Sashen Gine-gine da Zane-zane ta Asiya da Facific suka shirya. A watan Maris 2016, wannan sashen ta kaura daga Ostareliya zuwa ofishin dake Filifin.

23 ga Yuni, 2015​—Filin gini a Birnin Quezon

Na’urar tauna kasa na rurrusa wata hanya da aka yi kankare don a haka rami. Nan ne za a saka bututu na ruwa mai sanyi domin shirya na’urar kawo sanyi inda akwai zufa.

20 ga Yuni, 2015​—Filin gini a Birnin Quezon

Wasu ma’aurata daga kasar Amirka suna shirin yin aikin walda a hanyar tafiya da kafa.

20 ga Yuli, 2015​—Filin gini a Birnin Quezon

Ma’aikata suna binne bututu na ruwan sanyi tsakanin Gini na 4 da gini na 5.

18 ga Satumba, 2015​—Gini na 5

Mai aikin kafinta na dauke da kayan aikinsa yana saka abin rufe wundo.

18 ga Satumba, 2015​—Gini na 5

Ana shimfida kafai. An shimfida kafat a bene na hawa biyu a gini na 5, domin kada surutu ya shiga sashen da ake daukan murya da bidiyo.

22 ga Oktoba, 2015​—Gini na 5

Masu aikin fenti suna shafa fenti mai daukan zafi a wannan ginin. Fentin zai iya hana zafi shigowa cikin ginin, hakan zai sa ginin ya yi sanyi, kuma hakan zai sa a rage kudin da za a kashe wurin biyan kudin lantarki.

10 ga Fabrairu, 2016​—Gini na 4

Mai aikin kankare na cire wani abin da aka sa dama domin gina katanga. Gini na 4 yana da hawa biyu, a nan ne dalibai dabam-dabam na makarantar Littafi Mai Tsarki za su zauna.

10 ga Fabrairu, 2016​—Gini na 4

Daya daga cikin masu aiki yana saka na’urar kawo iska kuma yana binne su bututu na ruwan sanyi. Hakan zai inganta yanayin ruwan sanyi kuma ya hana ruwan daskarewa.

16 ga Fabrairu, 2016​—Gini na 4

Daya daga cikin masu aiki a fuskar fasaha daga Ostareliya yana gwada kayan gudanar da lantarki. An gayyaci ma’aikata fiye da 100 da suka gwanince a ayyuka dabam-dabam daga wasu kasashe don su taimaka a wannan aikin gyaran.