Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tone-tone Sun Nuna Inda Wata Kabilar Isra’ila Ta Taba Zama

Tone-tone Sun Nuna Inda Wata Kabilar Isra’ila Ta Taba Zama

 Baibul ya ce a lokacin da Isra’ilawa suka shiga Kasar Alkawari, kuma aka raba wa kowace kabila kasa, zuriya goma a kabilar Manassa sun sami babban fili a yammacin Urdun, nesa da sauran kabilun. (Yoshuwa 17:​1-6) Akwai wani abu da aka tono da ya tabbatar da hakan?

 A shekara ta 1910, an tono wasu gutsuren tukwane a Samariya da ke dauke da rubutu. Wadannan gutsurin tukwane na dauke da rubutu a Ibrananci kuma ya nuna kaya masu tsada kamar su ruwan inabi da kuma māi mai tsada da ake kai fādar sarki a birnin. Gutsurori 102 ne aka samo, kuma an yi su ne a karni na takwas kafin haihuwar Yesu, amma guda 63 ne kadai za a iya karantawa. Dukan wadannan gutsurori 63 sun nuna lokaci da sunayen zuriya da sunayen wadanda suke aika da kuma masu karbar kayayyakin.

 Hakazalika, duka zuriyar da aka rubuta a gutsurin tukwane a Samariya ʼyan kabilar Manassa ne. Juyin NIV Archaeological Study Bible ya ce hakan ya ba da “karin bayani a kan abin da Baibul ya ce game da zuriyar Manassa da kuma wurin da suka zauna.”

Wannan rubutun ya ambata wata ʼyar zuriyar Manassa mai suna Noah

 Gutsurarrun tukwane da aka samo a Samariya sun tabbatar da abin da Amos, wani marubucin Baibul ya ce game da masu arziki a lokacin. Ya ce: “Kuna shan ruwan inabi daga manyan kwanoni, kuna shafa wa jikinku māi mafi tsada.” (Amos 6:​1, 6) Gutsurarrun tukwanen Samariya sun nuna cewa an shigar da wadannan kayayyakin zuwa inda zuriya goma na Manassa suka mallaka.