Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Har Yanzu Gaskiya Tana da Muhimmanci Kuwa?

Har Yanzu Gaskiya Tana da Muhimmanci Kuwa?

 Shin, yana yi maka wuya ka bambanta gaskiya da karya? Mutane a yau sun fi yarda da abu bisa ga yadda suke ji, da kuma abin da suka yi imani da shi maimakon gaskiya da kuma tabbaci. A duk fadin duniya, mutane da yawa ba su yarda cewa akwai abin ake kira gaskiya ba.

 Mun sha gani irin raꞌayin nan. A shekaru 2000 da suka shige, Gwamnan Roma mai suna Pontius Pilate ya tambayi Yesu cewa: “Mece ce gaskiya?” (Yohanna 18:38) Ko da yake Pilate bai jira Yesu ya ba shi amsa ba, amma tambayar da ya yi tana da muhimmanci. Littafi Mai Tsarki na dauke da amsa mai gamsarwa da zai iya taimaka maka a duniyar nan da mutane ba su san gaskiya ko karya ba.

Shin akwai gaskiya kuwa?

 E. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “gaskiya” a duk lokacin da yake magana game da abin da ke da tabbaci. Hakan na nuna mana cewa Jehobah a Allah mai fadin gaskiya ne, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira shi “Allah na gaskiya.” (Zabura 31:5) Littafi Mai Tsarki yana dauke da gaskiyar da Allah ya bayyana, kuma ya kwatanta gaskiyar nan da haske domin tana koya mana yadda za mu yi rayuwa a wannan duniyar da mutane sun rikice.​—Zabura 43:3; Yohanna 17:17.

Ta yaya za ka san gaskiya?

 Allah ba ya so mu amince da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki haka kawai. A maimakon haka, yana so mu yi nazarin Kalmarsa, kuma mu yi amfani da hankalinmu, ba yadda muke ji kawai ba. (Romawa 12:1) Yana so mu koya game da shi kuma mu kaunace shi da ‘dukan hankalinmu,’ yana kuma karfafa mu mu tabbata cewa abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki gaskiya ne.​—Matiyu 22:​37, 38; Ayyukan Manzanni 17:11.

Wane ne ya soma yin karya?

 Littafi Mai Tsarki ya ce makiyin Allah, wato Shaidan Iblis ne ya fara yin karya, shi ya sa ya kira shi “uban karya.” (Yohanna 8:44) Ya yi wa Adamu da Hauwaꞌu karya game da Allah. (Farawa 3:​1-6, 13, 17-19; 5:5) Tun daga lokacin Shaidan yana kan yada karya game da Allah da kuma hana mutane sanin gaskiya game da shi.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9.

Me ya sa yawancin mutane suke karya sosai a yau?

 Littafi Mai Tsarki ya kira zamaminmu “kwanakin karshe,” kuma yadda Shaidan yake rinjayar mutane ya karu fiye da dā. Mutane sukan yi karya ne don su rudi wasu kuma su cuce su. (2 Timoti 3:​1, 13) Addinai da yawa a yau ma suna karya. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta, mutane a zamaninmu suna “tattara wa kansu masu koyarwa, su koyar da abin da kunnensu masu kaikayi suke marmarin ji,” kuma sun gwammace “su toshe kunnensu ga jin koyarwar gaskiya.”​—2 Timoti 4:​3, 4.

Me ya sa gaskiya take da muhimmanci?

 Mutane suna bukatar su san gaskiya game da kansu don su iya yarda da juna. Idan mutane ba su yarda da juna ba, ba za su iya kulla abokantaka da juna ba, kuma zaman tare ba zai yiwu ba. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana so mu bauta masa bisa ga gaskiya. Ya ce: “Masu yi [wa Allah] sujada kuma sai su yi masa sujada cikin ruhu, da cikin gaskiya kuma.” (Yohanna 4:24) Don ka san yadda gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki za ta taimaka maka ka san karyar da addinai suke yi, kuma ka daina yarda da su, ka karanta jerin talifofin nan mai jigo “Lies That Make God Seem Unlovable.”

Me ya sa Allah yake so in san gaskiya?

 Allah yana so ka sami rai na har abada, amma kafin ka sami wannan damar, kana bukatar ka san gaskiya game da shi. (1 Timoti 2:4) Idan ka koyi dokokin Allah game da abu mai kyau da marar kyau kuma ka bi su, za ka kasance da dangantaka mai kyau da shi. (Zabura 15:​1, 2) Allah ya aiko Yesu duniya don ya taimaka wa mutane su koyi gaskiya game da shi. Allah yana so mu bi abin da Yesu ya koya mana.​—Matiyu 17:5; Yohanna 18:37.

Allah zai sa a daina yin karya?

 Kwarai kuwa. Allah ya tsani mutanen da suke yin karya don su cuce wasu. Ya yi alkawarin cewa zai hallaka wadanda suka ci-gaba da yin karya. (Zabura 5:6) Bayan Allah ya yi hakan, zai kuma cika wannan alkawarin da ya ce: “Gaskiya za ta kasance har abada.”​—Karin Magana 12:19.

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah. (Zabura 83:18) Ka ga talifin nan “Wane ne Jehovah?