Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Ina Wa’azi Ko da Yake Ni Kurma Ne

Ina Wa’azi Ko da Yake Ni Kurma Ne

Na yi baftisma a shekara ta 1941, a lokacin shekaruna 12. Amma ban fahimci abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki ba, sai a shekara ta 1946 na yi hakan. Me ya sa? Bari in ba ku labarin abin da ya faru.

A TSAKANIN shekara ta 1910 zuwa 1919 ne iyayena suka ƙaura daga birnin Tbilisi da ke Georgia zuwa ƙasar Kanada, kuma suka zauna a wani ƙaramin gida da yake cikin gona a ƙauyen Pelly da ke yankin Saskatchewan a yammacin Kanada. An haife ni a shekara ta 1928, kuma ni ne auta cikin yara shida da iyayena suka haifa. Mahaifina ya mutu wata shida kafin a haife ni, kuma mahaifiyata ma ta mutu a lokacin da nake shekara ɗaya. A lokacin da nake shekara 17, sai yayata babba mai suna Lucy ta mutu. Bayan wannan, kawuna mai suna Nick ya kawo mu gidansa don mu zauna tare da shi.

A lokacin da nake shekara biyu, sai na je ina wasa da wutsiyar dokin da yake gonarmu, da ’yan gidanmu suka hango ni, sun ji tsoro sosai don kada dokin ya ji mini rauni, sai suka yi ihu suna ce min in daina, amma ni kuma ko motsawa ban yi ba. Da yake ban gan su ba, ban ji cewa suna yin min ihu ba. Dokin bai mini rauni ba, amma a wannan ranar ne suka san cewa ni kurma ne.

Wani aminin iyalinmu ya ba su shawara cewa su kai ni makarantar kurame, sai kawuna Nick ya kai ni makarantar da ke birnin Saskatoon a yankin Saskatchewan. Wurin yana da nisa sosai, kuma shekarata biyar ne kawai, don haka na ji tsoro. Sai an ba da hutu ne nake iya zuwa gida. Na koyi yaren kurame kuma na soma yin wasa da yaran da ke wurin.

NA KOYI GASKIYAR DA KE LITTAFI MAI TSARKI

A shekara ta 1939, yayata mai suna Marion ta auri Bill Danylchuck, kuma ni da ’yar’uwata muka je muka zauna da su. Su ne suka fara yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Kuma suna koya mini duk abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki a duk lokacin da na je wurinsu hutu. A gaskiya, yi musu magana bai kasance mini da sauƙi ba, saboda su ba su iya yaren kurame ba. Duk da haka, sun lura cewa ina son Kalmar Allah. Ban da haka ma, na fahimci cewa suna yin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, don haka, na bi su zuwa wa’azi. Bayan wani lokaci na so in yi baftisma, kuma a ranar 5 ga Satumba 1941, Bill ya yi mini baftisma a wani babban durum na ƙarfe cike da ruwan rijiya mai sanyi!

Ni da wasu kurame a babban taro a birnin Cleveland da ke jihar Ohio a shekara ta 1946

A shekara ta 1946 da na samu hutu daga makaranta kuma na koma gida, sai muka halarci babban taro a birnin Cleveland da ke jihar Ohio a Amurka. A ranar farko, yayuna mata sun taimaka suna rubuta mini abubuwan da ake faɗa a taron. A rana ta biyu kuma sai muka gano cewa akwai kurame a wani gefe da ake musu fassara, sai na je wurin. A ƙarshe, na ji daɗin taron saboda ya taimaka mini in fahimci gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki da kyau!

NA KOYA MA WASU GASKIYAR DA KE LITTAFI MAI TSARKI

A lokacin da aka daina Yaƙin Duniya na Biyu, mutane ba su daina nuna kishin ƙasa ba. Da na dawo daga babban taron, na tsai da shawara cewa ba zan yi abin da zai ɓata dangantakata da Allah ba. Don haka, sai na daina sara wa tuta kuma na daina rera taken ƙasa. Ban da haka ma, na daina yin bukukuwan hutu kuma na daina zuwa cocin makarantarmu da ake sa mu dole mu riƙa zuwa. Malamanmu ba su ji daɗin matakin da na ɗauka ba, don haka, suka fara tsoratar da ni da kuma yi min ƙarya don in canja ra’ayina. Abin ya jawo ɗan matsala a ajinmu amma hakan ya ba ni damar yi musu wa’azi. Na yi wa Larry Androsoff da Norman Dittrick da Emil Schneider wa’azi kuma suka soma bauta wa Jehobah, har yanzu suna bauta wa Jehobah da aminci.

A duk lokacin da na ziyarci wasu birane, ina zuwa in yi wa kurame wa’azi. Alal misali, a wani kulob na kurame a birnin Montreal, na yi ma wani ɗan daba mai suna Eddie Taeger wa’azi. Kafin ya mutu a shekarar da ta shige, yana hidima a ikilisiyar yaren kurame da ke birnin Laval a yankin Quebec. Ban da haka ma, na yi wa Juan Ardanez wa’azi, shi wani mutumi ne da ya nuna halin mutanen Biriya kuma ya bincika abin da yake koya don ya ga ko gaskiya ne. (A. M. 17:​10, 11) Shi ma ya bauta wa Jehobah da aminci a matsayin dattijo a birnin Ottawa da ke yankin Ontario har mutuwarsa.

A tsakanin shekara ta 1950 zuwa 1959 muna yin wa’azi a kan titi

A shekara ta 1950, na ƙaura zuwa birnin Vancouver. Ko da yake ina son yi wa kurame wa’azi, ba zan taɓa manta da abin da ya faru da ni a lokacin da na yi ma wata mata mai suna Chris Spicer wa’azi a kan titi ba. Ita ba kurma ba ce amma ta karɓi mujallar da na ba ta kuma ta so in haɗu da mijinta mai suna Gary. Na ziyarce su kuma mun tattauna sosai ta wajen yi wa juna rubutu. Wannan shi ne farkon haɗuwarmu da su, bayan wasu shekaru, na yi mamakin haɗuwa da su a babban taron da muka je a birnin Toronto da ke yankin Ontario. A wannan ranar ne Gary ya yi baftisma. Hakan ya sa na fahimci cewa ci gaba da yi ma mutane wa’azi yana da muhimmanci sosai don ba mu san ko su waye ne za su zama abokan Jehobah gobe ba.

Bayan haka, na ƙaura zuwa birnin Saskatoon. A wurin na haɗu da wata mata da ta ce in riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da yaranta ’yan biyu masu suna Jean da Joan Rothenberger, su ɗalibai ne a makarantar kurame da na yi. Nan ba da daɗewa ba, ’yan biyun sun soma gaya wa ’yan ajinsu abubuwan da suke koya. ’Yan ajinsu guda biyar suka zama Shaidun Jehobah, ɗaya daga cikinsu sunanta Eunice Colin. A lokacin da nake kusan kammala sakandare, na haɗu da Eunice a makarantar kurame. A wannan lokacin ta ba ni alewa kuma ta ce ko zan zama abokinta.

Ni da Eunice a shekara ta 1960 da kuma shekara ta 1989

Da mahaifiyar Eunice ta ji cewa tana yin nazarin Littafi Mai Tsarki, sai ta gaya wa shugaban makarantar don ya hana ta yin nazarin. Har ma ya kwace littattafan da take yin nazari da su. Duk da haka, Eunice ba ta karaya ba amma ta ci gaba da yin nazarinta. Da ta tsai da shawarar yin baftisma, sai iyayenta suka ce mata, “Idan kika zama memban Shaidun Jehobah, za ki bar gidanmu!” An kori Eunice daga gidansu a lokacin da take shekara 17, kuma wasu Shaidun Jehobah suka ce ta zo ta zauna da su. Ta ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki har daga baya ta yi baftisma sai muka yi aure. A shekara ta 1960 da muka yi aure, iyayen Eunice sun ƙi su zo aurenmu. Amma da shigewar lokaci, sun soma daraja mu saboda imaninmu da kuma yadda muka yi renon yaranmu.

JEHOBAH YA KULA DA NI

Ɗana Nicholas da matarsa Deborah suna hidima a Bethel da ke Landan

Da yake mu kurame ne, kuma yaranmu guda bakwai ba kurame ba, yin renonsu bai mana sauƙi ba. Don haka, sai muka koya musu yaren kurame don mu iya fahimtar juna kuma mu koya musu game da Jehobah. ’Yan’uwa a ikilisiya sun taimaka mana sosai. Alal misali, wani magidanci ya rubuto mana cewa ɗaya daga cikin yaranmu yana maganar banza a Majami’ar Mulki sai nan da nan muka ja masa kunne. Ƙari ga haka, yaranmu huɗu James da Jerry da Nicholas da Steven da kuma iyalansu suna bauta wa Jehobah da aminci. Duka su huɗun suna hidima a matsayin dattawa. Ban da haka ma, Nicholas da matarsa Deborah suna fassara yaren kurame a ofishinmu da ke Biritaniya, kuma Steven da matarsa Shannan suna yin hakan a ofishinmu da ke Amurka.

Yarana James da Jerry da Steven tare da matansu suna taimaka don a yi wa kurame wa’azi a hanyoyi dabam-dabam

Wata ɗaya kafin bikin tunawa da aurenmu na shekara 40, Eunice ta mutu sanadiyyar ciwon kansa. Duk da wahalar da ta sha, ba ta karaya ba, amma da yake ta yi imani da tashin matattu, hakan ya ƙarfafa ta sosai. Ina ɗokin lokacin da zan sake ganin ta.

Faye da James, Jerry da Evelyn, Shannan da Steven

A watan Fabrairu na 2012, na faɗi kuma na karye ƙafata, saboda haka, na bukaci taimako. Sai na ƙaura zuwa gidan ɗaya daga cikin yarana. Har yanzu ina hidima a matsayin dattijo a ikilisiyar kurame da ke birnin Calgary. Wannan shi ne lokaci na farko da na zauna a ikilisiya da ake yaren kurame. Hakan abin mamaki ne, saboda tun shekara 1946 ina ikilisiyar Turanci. Amma, ta yaya na samu na ƙarfafa dangantakata da Jehobah? Babu shakka, Jehobah ya cika alkawarinsa na kulawa da marayu. (Zab. 10:14) Ina gode ma waɗanda suka taimaka min suna rubuta min har ma suka koyi yaren kurame don su riƙa gaya mini abin da ake faɗa a ikilisiya.

Ina da shekara 79 a lokacin da na halarci makarantar majagaba a yaren kurame na Amurka

A gaskiya, akwai wasu lokuta da nakan ji takaici kuma in ji kamar zan karaya, saboda ba na fahimtar abin da ake faɗa kuma mutane ba su fahimci yadda nake ji ba. Amma a duk lokacin da nake jin hakan sai in tuna da abin da Bitrus ya faɗa wa Yesu cewa: “Ubangiji, wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada.” (Yoh. 6:​66-68) Kamar sauran ’yan’uwa kurame, ni ma na fahimci muhimmancin kasancewa da jimiri. Ƙari ga haka, na koyi yadda zan dogara ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa, kuma na amfana sosai don hakan! Yanzu ina da abubuwa da yawa a yarena da suke taimaka min in ci gaba da koya game da Jehobah. Ban da haka, ina farin cikin halartar manya taro a yaren kurame. Babu shakka, Jehobah ya albarkaci rayuwata da kuma hidimar da nake yi masa.