Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABUBUWAN DA ZA KU IYA YIN NAZARI A KAI

Ku Zauna da Shiri Ta Wurin Yin Nazari Sosai

Ku Zauna da Shiri Ta Wurin Yin Nazari Sosai

Ku karanta Daniyel 9:1-19 don ku ga muhimmancin yin nazari mai zurfi.

Ku bincika labarin sosai. Waɗanne abubuwa ne ba su jima da faruwa ba a lokacin, kuma ta yaya suka shafi Daniyel? (Dan. 5:29–6:5) Yaya za ka ji idan kai ne Daniyel?

Ku nemi ƙarin bayani. Waɗanne “littattafai masu tsarki” ne wataƙila Daniyel ya bincika? (Dan. 9:2; w23.08 shafi na 4 sakin layi na 7) Ta yaya adduꞌar da Daniyel ya yi a Daniyel 9:11-13 ta nuna cewa yana nazarin Littafi Mai Tsarki sosai?—L. Fir. 26:39-42; 1 Sar. 8:46-50.

Ku yi tunani a kan abubuwan da kuka koya. Kowa ya tambayi kansa:

  • ‘Me zan yi don kada abubuwa da suke faruwa a duniya su raba hankalina?’ (Mik. 7:7)

  • ‘Ta yaya zan amfana idan ina nazarin Littafi Mai Tsarki sosai kamar Daniyel?’ (w04 8/1 22 sakin layi na 17)

  • ‘Waɗanne batutuwa ne za su taimaka mini in “zauna da shiri” idan na yi nazari a kansu?’ (Mat. 24:42, 44; w12 8/15 5 sakin layi na 7-8)