Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Za Ki Yi Idan Maigidanki Yana Kallon Batsa?

Me Za Ki Yi Idan Maigidanki Yana Kallon Batsa?
  • “Na ji kamar maigidana ya yi zina sau da yawa.”

  • “Na ji kamar ba ni da kyau, ba ni da amfani, kuma abin ya kunyatar da ni.”

  • “Ban iya gaya wa kowa batun nan ba. Na yi ta fama da baƙin cikin ni kaɗai.”

  • “Na ji kamar Jehobah bai damu da ni ba.”

Waɗannan kalaman sun nuna irin baƙin cikin da mace take yi idan maigidanta yana kallon batsa. Kuma idan ya yi watanni ko shekaru da yawa yana yin hakan a ɓoye, zai yi mata wuya ta sake yarda da shi. Wata mata ta ce: “Na ji kamar akwai abubuwa da yawa da ban sani game da maigidana ba. Anya babu wasu abubuwan da yake ɓoyewa kuwa?”

An shirya wannan talifin ne don mace da maigidanta yake kallon batsa. a Talifin zai ambata ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su ƙarfafa ta kuma su nuna mata cewa Jehobah yana so ya taimake ta. Ƙari ga haka, za su taimaka mata ta samu kwanciyar hankali kuma ta kusaci Jehobah. b

MENE NE MATAR ZA TA IYA YI?

Ko da yake ba za ki iya kafa wa maigidanki doka ba, akwai wasu abubuwan da za ki iya yi don ki rage baƙin ciki kuma ki samu kwanciyar hankali. Ga wasu cikinsu.

Kada ki ɗora wa kanki laifi. Mace tana iya ganin cewa kallon batsa da maigidanta yake yi laifinta ne. Wata mai suna Alice c tana ganin cewa ba ta da kyau, shi ya sa maigidanta yake kallon batsa. Ta ce: ‘Me ya sa maigidana ya fi son kallon wasu mata dabam maimakon ni?’ Wasu mata suna ɗora wa kansu laifi, domin suna ganin yadda suke bi da batun yana ƙara matsalar maimakon ya magance ta. Wata mai suna Danielle ta ce: “Abin da maigidana ya yi ya sa na soma fushi sosai. Amma sai na ga kamar fushin da nake yi ne ya sa bai daina wannan halin ba.”

Idan ke ma haka kike ji, ki san cewa Jehobah ba ya ganin ki da laifi don abin da maigidanki yake yi. Yakub 1:14 ta ce: ‘Kowane mutum dai yakan sami jarraba saꞌad da mugun kwaɗayinsa ya ruɗe shi, ya kuma sha kansa.’ (Rom. 14:12; Filib. 2:12) Maimakon Jehobah ya ɗora miki laifi, yana farin ciki don amincinki.​—2 Tar. 16:9.

Ƙari ga haka, zai yi kyau ki san cewa ba don ba ki da kyau ne maigidanki yake kallon batsa ba. Waɗanda suka ƙware a wannan batun sun ce kallon batsa yana sa mutum ya yi mugun shaꞌawa da babu macen da za ta iya gamsarwa.

Ki guji yawan damuwa. Wata mai suna Catherine ta ce ta damu sosai game da kallon batsa da maigidanta yake yi da har babu wani abin da take tunanin sa in ba abin da yake yi ba. Wata mai suna Frances ta ce: “Ina damuwa sosai musamman ma idan ban san inda maigidana yake ba. Sai in yini ina damuwa.” Wasu mata sun ce sukan ji kunya sosai idan suna tare da ꞌyanꞌuwan da suka san abin da mazajensu suke yi. Wasu kuma sun ce sukan kaɗaita domin a tunaninsu, babu wanda ya fahimci yanayin da suke ciki.

Ba laifi ba ne mutum ya ji haka. Amma idan kina yawan tunani game da abubuwan nan, zai ƙara miki baƙin ciki. Don haka, ki mai da hankali ga dangantakarki da Jehobah. Hakan zai taimaka miki ki jimre yanayin.​—Zab. 62:2; Afis. 6:10.

Akwai labaran mata a Littafi Mai Tsarki da suka yi baƙin ciki, sun yi adduꞌa ga Jehobah kuma ya taimaka musu. Za ki amfana idan kika karanta labaran nan kuma kika yi bimbini a kan su. Ko da yake ba a kowane lokaci ne Jehobah ya cire musu matsalar ba, ya ba su kwanciyar hankali. Alal misali, yanayin da Hannatu ta shiga ya sa ta “ɓacin rai” sosai. Amma bayan da Hannatu “ta jima tana adduꞌa a gaban Ubangiji,” hankalinta ya kwanta, duk da cewa ba ta san mene ne zai faru da ita a nan gaba ba.​—1 Sam. 1:​10, 12, 18, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe; 2 Kor. 1:​3, 4.

Mata da miji za su iya neman taimako daga wurin dattawa

Ki nemi taimako daga wurin dattawa. Za su zama miki “kamar mafaka daga iska, kamar wurin ɓuya daga ruwan ƙanƙara.” (Isha. 32:2) Za ma su iya gaya miki wata ꞌyarꞌuwa da za ki iya gaya mata yadda kike ji kuma ta ƙarfafa ki.​—K. Mag. 17:17.

ZA KI IYA TAIMAKA MASA?

Za ki iya taimaka wa maigidanki ya daina kallon batsa? Hakan zai yiwu. Littafi Mai Tsarki ya ce “gwamma mutum biyu da mutum ɗaya,” idan ana so a sasanta wata matsala ko a yaƙi wani maƙiyi mai ƙarfi sosai. (M. Wa. 4:​9-12) Waɗanda suka ƙware a batun nan sun ce idan maꞌaurata suna taimaka wa juna, maigidan zai iya daina kallon batsa kuma matar za ta iya sake yarda da shi.

Amma fa, za ku yi nasara ne idan maigidan yana a shirye ya yi iya ƙoƙarinsa don ya daina kallon batsa. Shin ya roƙi Jehobah ya taimaka masa kuma ya nemi taimakon dattawa? (2 Kor. 4:7; Yak. 5:​14, 15) Shin ya ɗau matakan da za su taimaka masa ya guji kallon batsa? Alal misali, ya keɓe lokutan da zai riƙa amfani da naꞌurorinsa da lokutan da ba zai yi hakan ba? Yana guje wa yanayoyin da za su sa ya kalli batsa? (K. Mag. 27:12) Shin yana amincewa da taimakon da kike masa kuma yana gaya miki gaskiya? Idan yana abubuwan nan, to za ki iya taimaka masa ke nan.

Ta yaya? Ga misalin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Felicia. Ta auri Ethan, kuma shi tun yana yaro yake kallon batsa. Felicia ta sa ya yi wa maigidanta sauƙi ya gaya mata lokacin da yake shaꞌawar kallon batsa. Ethan ya ce: “Ina gaya wa matata gaskiya game da yadda nake ji a zuciyata. Takan taimaka mini in guji yanayoyin da za su sa na kalli batsa. Kuma takan tambaye ni yaya abubuwa suke tafiya. Tana taimaka mini in yi hankali da wuraren da nake shiga a intane kuma kada in yi hakan a inda babu kowa.” Shaꞌawar kallon batsa da Ethan yake yi tana sa Felicia baƙin ciki. Amma ta ce: “Fushina da kuma baƙin cikin da nake yi ba su taimaka masa ya daina wannan mummunar halin ba. Bayan mun tattauna yadda zai shawo kan matsalarsa, shi ma yana yin iya ƙoƙarinsa don ya taimaka mini in daina baƙin ciki.”

Irin tattaunawar nan zai taimaka wa mijin ya daina kallon batsa. Kuma zai sa matarsa ta sake yarda da shi. Idan miji yana gaya wa matarsa game da kasawarsa, da inda za shi, da kuma abubuwan da yake yi, hakan zai sa matarsa ta yarda da shi don za ta ga cewa ba ya ɓoye mata kome.

Kina ganin ke ma za ki iya taimaka wa maigidanki ya daina kallon batsa? In haka ne, za ki iya karanta talifin nan tare da maigidanki kuma ku tattauna game da shi. Yayin da kuke hakan, zai dace maigidanki ya kasance da burin daina kallon batsa kuma ya sa ki sake yarda da shi. Maimakon ya yi fushi don kina so ki tattauna wannan batun, zai dace ya yi iya ƙoƙari ya fahimci yadda matsalar take damun ki. Ke kuma burinki shi ne ki taimaka masa ya daina wannan halin don ki sake yarda da shi. Ku biyun kuna bukatar ku bincika dalilin da ya sa mutane suke kallon batsa, da yadda za su daina hakan. d

Idan kina tsoron cewa tattaunawar za ta iya jawo rigima, kina iya gaya ma wani dattijo da ku biyun kuka saba da shi, ya kasance tare da ku saꞌad da kuke tattaunawar. Ko da maigidanki ya daina kallon batsa, zai iya ɗaukan lokaci sosai kafin ki sake yarda da shi. Amma kada ki fid da rai. Ki riƙa lura da ƙoƙarin da yake yi. Ki sa a ranki cewa, idan ku biyun kuka ci gaba da haƙuri, a-kwana-a-tashi kome zai gyaru.​—M. Wa. 7:8; 1 Kor. 13:4.

IDAN YA KASA DAINAWA FA?

Idan maigidanki ya sake kallon batsa bayan ya daina na ꞌyan lokuta, hakan yana nufin cewa ba ya so ya canja ne, ko ba zai taɓa dainawa ba? Ba lallai ba. Domin idan kallon batsa ta riga ta zama masa jaraba, zai iya yin fama da wannan yanayin har iyakar rayuwarsa. Zai iya sake kallon batsa ko da ya yi shekaru da yawa bai yi hakan ba. Don haka, sai ya dage sosai. Misali, yana bukatar ya ci gaba da ɗaukan matakan da suka taimaka masa da farko ko da yana ganin ya daina. (K. Mag. 28:14; Mat. 5:29; 1 Kor. 10:12) Yana bukatar ya sake ‘sabunta tunaninsa da hankalinsa,’ kuma ya ‘ƙi mugunta,’ wato ya ƙi halaye marasa kyau kamar kallon batsa da wasa da alꞌaura. (Afis. 4:23; Zab. 97:10; Rom. 12:9) Shin yana iya ƙoƙarinsa ya yi abubuwan nan? Idan haka ne, a-kwana-a-tashi, zai daina halin nan gabaki ɗaya. e

Ki mai da hankali ga dangantakarki da Jehobah

Idan maigidanki ba ya so ya canja wannan halin kuma fa? Abin zai dame ki kam, ƙila ki yi fushi kuma ki dinga jin cewa ya ci amanar ki. Ki bar kome a hannun Jehobah, hakan zai taimaka miki ki samu kwanciyar hankali. (1 Bit. 5:7) Ki ci gaba da kusantar Jehobah ta wajen yin nazari da yin adduꞌa da kuma tunani mai zurfi. Yayin da kike hakan, ki kasance da tabbacin cewa shi ma zai yi kusa da ke. Kamar yadda Zabura 34:18 ta ce, Jehobah yana tare da “waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa,” kuma yana taimaka musu su sake farin ciki. Don haka, ki yi iya ƙoƙarinki ki kasance da halayen Kirista. Ki nemi taimako daga wurin dattawa. Kuma ki sa rai cewa maigidanki zai daina wannan halin wata rana.​—Rom. 2:4; 2 Bit. 3:9.

a A wannan talifin, za mu yi bayani a kan cewa maigidan ne yake kallon batsa. Amma da yawa daga cikin ƙaꞌidodin da za mu tattauna za su taimaka wa miji idan matar ce take kallon batsa.

b Littafi Mai Tsarki bai ba da izini a kashe aure don miji ko mata ta kalli batsa ba.​—Mat. 19:9.

c An canja wasu sunayen.

d Akwai wasu bayanai da za su iya taimaka muku a jw.org da kuma litattafanmu. Alal misali, ku duba talifin nan, “Kallon Batsa Zai Iya Wargaje Aurenku” a jw.org/ha; da “Za Ka Iya Yin Tsayayya da Jaraba!” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu 2014, shafuffuka na 8-10; da kuma “Batsa​—Tana da Lahani ko Aꞌa?” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba 2013, shafuffuka na 3-7.

e Da yake kallon batsa yana iya zama wa mutum jaraba, ban da taimakon da suka samu daga wurin dattawa, wasu maꞌaurata sun yanke shawarar neman taimako daga wurin likitoci.