Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Lefèvre d’Étaples​—⁠Ya So Mutane da Yawa Su San Kalmar Allah

Lefèvre d’Étaples​—⁠Ya So Mutane da Yawa Su San Kalmar Allah

A SAFIYAR Lahadi a tsakanin shekara ta 1520 zuwa 1523, mazaunan garin Meaux kusa da birnin Faris, sun yi mamaki sosai don abin da suka ji a coci. Sun ji karatun Linjila a yarensu Faransanci maimakon Latinanci!

Daga baya, mafassarin wannan juyin Littafi Mai Tsarki mai suna Jacques Lefèvre d’Étaples ya ce wa amininsa: “Abin mamaki ne sosai yadda Allah yake taimaka wa mutane da yawa su fahimci Kalmarsa.”

A lokacin, limaman Cocin Katolika da kuma wasu limamai a birnin Faris sun haramta yin amfani da Littafi Mai Tsarki da aka fassara zuwa ƙananan yaruka. Amma mene ne ya motsa Lefèvre ya fassara Littafi Mai Tsarki a Faransanci? Kuma ta yaya ya taimaka wa mutane da yawa su fahimci Kalmar Allah?

YIN BINCIKE DON SANIN MA’ANAR NASSOSI

Kafin Lefèvre ya zama mafassarin Littafi Mai Tsarki, ya ba da kai wajen gyara kurakuren da ke littattafan ilimin falsafa da kuma tauhidi. Ya ce an yi kurakurai da yawa a cikin littattafan. Sa’ad da ya soma binciken littattafai na zamanin dā, sai ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki na Cocin Katolika, wato Latin Vulgate.

Nazarin Nassosin da ya yi ya sa ya kammala cewa “yin nazarin gaskiya daga Allah ne kawai . . . zai iya sa mu farin ciki sosai.” Saboda haka, Lefèvre ya daina nazarin littattafan ilimin falsafa kuma ya mai da hankali wajen fassara Littafi Mai Tsarki.

A shekara ta 1509, Lefèvre ya yi bincike a kan juyi guda biyar na littafin Zabura na yaren Latin * kuma hakan ya taimaka masa wajen wallafa nasa juyin. Ƙari ga hakan, ya yi gyara ga juyin Vulgate. Lefèvre bai bi misalin limamai na zamaninsa ba, maimakon haka, ya fassara ainihin saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Yadda wannan mutumin ya bayyana Nassosi ya taimaka wa wasu mafassaran Littafi Mai Tsarki.​—⁠Ka duba akwatin nan “ Yadda Fassarar Lefèvre Ta Shafi Martin Luther.”

Laƙabin Allah a littafin Zabura da ke cikin Fivefold Psalter, da aka wallafa a shekara ta 1513

Da yake an haifi Lefèvre cikin cocin Katolika, ya gaskata cewa za a iya yin gyare-gyare a cocin idan aka koya wa mutane da yawa Nassosi. Amma ta yaya mutane za su amfana daga Nassosi da yake yawanci a yaren Latin ne?

FASSARAR LITTAFI MAI TSARKI DON KOWA

Gabatarwar Linjila ta nuna cewa Lefèvre ya so kowa ya karanta Littafi Mai Tsarki a yarensu

Yadda Lefèvre yake son Kalmar Allah ne ya sa ya tsai da shawarar fassara ta don mutane da yawa su karanta. A watan Yuni na shekara ta 1523 ne ya fassara Linjila zuwa ƙananan kundi guda biyu a Faransanci don ya iya cim ma maƙasudinsa. Littafin ƙarami ne kuma kuɗinsa bai kai na babba ba. Hakan ya sa ya yi wa talakawa sauƙi su saye shi.

Mutanen sun ji daɗin karanta juyinsa sosai. Maza da mata sun yi farin cikin karanta kalaman Yesu a yarensu shi ya sa kofi 1,200 da aka soma bugawa suka ƙare a cikin ‘yan watanni kawai.

YA YI GABA GAƊI DOMIN LITTAFI MAI TSARKI

Lefèvre ya faɗa a cikin gabatarwar Linjilar cewa ya yi fassarar zuwa Faransanci ne domin “talakawan” cocin su iya “fahimtar Nassosi a nasu yaren kamar yadda ‘yan Latin suke fahimta a nasu yaren.” Amma me ya sa Lefèvre yake so ya taimaka wa mutane su san ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa?

Lefèvre ya san yadda ƙarya da kuma ilimin falsafa da limamai suke koyarwar suka ɓata Cocin Katolika. (Markus 7:7; Kolosiyawa 2:⁠8) Kuma ya yi imani cewa lokacin yaɗa bishara a “dukan duniya ya yi don kada a sake ruɗan mutane da koyarwar ƙarya.”

Lefèvre ya kuma ƙaryata mutanen da suka ce bai kamata a fitar da Littafi Mai Tsarki a Faransanci ba. Ya ce: “Ta yaya za su koya wa mutane cewa su riƙa bin dukan abin da Yesu ya umurta, idan su da kansu ba su yarda jama’a su karanta Bishara ta Allah a yarensu ba?”​—Romawa 10:14.

Shi ya sa malaman addinai a Jami’ar Faris, wato Sorbonne suka yi ƙoƙarin hana Lefèvre yin fassara. A watan Agusta ta shekara ta 1523, sun haramta karanta wasu littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da kuma juyin Littafi Mai Tsarki a wasu harsuna, suna cewa irin littattafan za su “ɓata koyarwar Cocin.” Da ba don Sarkin Faransa mai suna Francis na Ɗaya ya saka baki ba, da an ce Lefèvre ya yi ridda.

MAFASSARI DA AKA “HARAMTA” YA CIM MA BURINSA

Lefèvre bai yarda wata muhawwarar banza ta raɓa hankalinsa daga aikin fassara Littafi Mai Tsarki ba. A shekara ta 1524, bayan da ya gama fassarar Nassosin Helenanci (da ake kira Sabon Alkawari), sai ya fito da juyin Zabura a Faransanci domin masu bi su yi amfani da shi wajen yin addu’a “da zuciya ɗaya.”

Malaman addinai da suke jami’ar Sorbonne ba su ɓata lokaci wajen yin nazarin fassarar da Lefèvre ya yi ba. Nan da nan suka ba da umurni cewa a fito da dukan fassarar Nassosin Helenanci da ya yi a fili kuma a ƙone su. Kuma sun yi da’awar cewa wasu littattafan da ya rubuta suna “goyon bayan koyarwar Luther.” Sa’ad da malaman addinai suka ce Lefèvre ya zo ya yi bayani, bai ce “kome ba,” sai ya gudu zuwa birnin Strasbourg. A nan, ya ci gaba da fassarar da yake yi na Littafi Mai Tsarki. Ko da yake wasu suna ɗaukansa matsoraci don bai ce kome ba sa’ad aka ce ya yi bayani, amma a ganinsa matakin da ya ɗauka ya dace da waɗannan malaman da ba su daraja gaskiyar Littafi Mai Tsarki da ke kamar ‘lu’u lu’u’ ba.​—Matta 7:6.

Wajen shekara ɗaya da guduwa, sai Sarki Francis na Ɗaya ya sa Lefèvre ya zama malamin yaronsa, ɗan shekara huɗu mai suna Charles. Wannan aikin ya ba Lefèvre damar kammala fassarar Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1530, an buga cikakken juyin Littafi Mai Tsarki da ya yi a Antwerp, ƙasar Belgium da izinin Sarki Charles na Biyar. *

ABUBUWAN DA YA SO BA SU FARU BA

A dukan rayuwarsa, Lefèvre ya sa rai cewa limaman coci za su yi watsi da al’adun mutane kuma su soma bin koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ya yi imani cewa kowane Kirista yana da hakkin karanta Littafi Mai Tsarki da kansa. Shi ya sa ya yi aiki tuƙuru don kowa ya sami Littafi Mai Tsarki. Ko da yake begen da ya yi cewa limaman cocin da za su daina bin al’adun mutane bai faru ba, amma misalin Lefèvre fitacce ne sosai. Ya taimaka wa mutane su san Kalmar Allah.

^ sakin layi na 21 Shekara biyar bayan haka, wato a shekara ta 1535, wani mafassari Bafaranse mai suna Olivétan ya fitar da Littafi Mai Tsarki da ya fassara daga yaren Ibrananci da Helenanci. Ya yi amfani da fassarar Lefèvre sosai sa’ad da yake juya Nassosin Helenanci.