Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Neman Kudi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?

Neman Kudi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?

Mutane da yawa suna ganin idan suka yi karatu sosai kuma suka yi kuɗi, rayuwarsu za ta yi kyau. A nasu ra’ayin, idan mutum ya je jami’a ya dawo, zai zama ƙwararren ma’aikaci kuma zai taimaka wa iyalinsa da ƙasarsa sosai. Ƙari ga haka, suna ganin idan mutum ya yi karatu sosai, zai sami babban aiki. Kuma in yana samun kuɗi, zai more rayuwa.

ZUWA JAMI’A MUTANE SUKA SA A GABA

Wani mutum mai suna Zhang Chen daga ƙasar China ya ce: “Na ɗauka cewa zuwa jami’a ne zai sa in rabu da talauci. Kuma cewa idan na sami babban aiki, kome zai tafi sumul a rayuwata.”

Mutane da yawa suna zuwa manyan makarantu, wasu har suna zuwa makaranta a ƙasashen waje garin neman ilimi don su ji daɗin rayuwa a nan gaba. Annobar korona ce ta sa waɗanda suke zuwa karatu a ƙasashen waje suka ragu kwanan nan. Wani rahoto da Ƙungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziki da Ci-gaba (OECD) ta bayar a 2012 ya ce: “Fiye da rabin mutanen da suke zuwa karatu a ƙasashen waje, daga Asiya suke.”

Iyaye da dama sukan yi aiki tukuru don yaransu su samu su je karatu a ƙasar waje. Wani mai suna Qixiang, daga ƙasar Taiwan ya ce: “Iyayena ba masu kuɗi ba ne, amma sai da suka yi iya ƙoƙari suka tura dukanmu ’ya’yansu huɗu mu je jami’a a Amirka.” Sai da iyayensa suka ci bashi kafin suka iya yin hakan kuma abin da mutane da yawa suke yi ke nan.

WANE SAKAMAKO AKA SAMU?

Mutane da yawa sun je babbar makaranta kuma sun sami kuɗi, duk da haka ba sa jin daɗin rayuwa

Ilimi yakan taimaka wa mutane a wasu hanyoyi, amma mutane da yawa da suka yi karatun ba sa samun abin da suke nema. Alal misali, akwai mutanen da suka yi iya ƙoƙari kuma suka ci bashi don su je babbar makaranta, amma a ƙarshe sun kāsa samun aikin da suke so. Wata ’yar jarida mai suna Rachel Mui a ƙasar Singapore ta ce: “Adadin waɗanda suka sauke karatu daga jami’a ba tare da samun aiki ba, sai daɗa karuwa yake yi.” Wani mai digirin digirgir mai suna Jianjie, daga ƙasar Taiwan ya ce: “Rashin aiki yana tilasta wa mutane da yawa su karɓi aikin da bai shafi abin da suka karanta a jami’a ba.”

Waɗanda suka sami irin aikin da suke so ma, rayuwa ba ta musu daɗi yadda suka zata ba. Alal misali, da wani mai suna Niran ya gama karatu a Turai kuma ya dawo ƙasar Thailand, ya ce: “Digiri da na samu ya sa na sami babban aikin da nake nema. Amma aikin yana bukatar kuzari da lokaci sosai. A ƙarshe an sallami yawancin ma’aikantan kamfanin har da ni. A nan ne na gano cewa, ba wani babban aiki da zai ba mutum tabbacin cewa zai ji daɗin rayuwa.”

Wasu suna da kuɗin kuma ana ganin kamar suna jin daɗin rayuwa. Duk da haka, suna fama da rashin lafiya da matsaloli a iyalinsu, kuma suna tsoro kar su rasa kuɗin da suke da shi. Alal misali, wani mai suna Katsutoshi daga Japan ya ce: “A dā ni mai kuɗi ne sosai, duk da haka rayuwa ba ta min daɗi ba domin mutane da yawa sun yi kishin abin da nake da shi, kuma sun yi ta wulaƙanta ni.” Wata mai suna Lam da take zama a Vietnam ta ce: “Na ga mutane da yawa da suka yi ƙoƙari su sami aiki mai kyau don su more rayuwa, amma hakan bai sa sun more rayuwar ba. Kuɗi yana ƙara wa mutum damuwa, ya sa shi rashin lafiya da kuma baƙin ciki.”

Akwai mutane da yawa da ra’ayinsu ya zo ɗaya da na Franklin, sun ga cewa neman ilimi da kuɗi ba shi ne zai sa su more rayuwa ba. Don haka, maimakon su sunkuya neman abin duniya, wasu suna iya ƙoƙarinsu su zama mutanen kirki, suna yi wa mutane alheri. A nasu ra’ayin, abin da zai sa su ji daɗin rayuwa ke nan. Amma idan mutum ya zama mutumin kirki, shi ke nan zai more rayuwa? Za a ba da amsar a talifi na gaba.