Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ƙauna ce take sa mu damu da mutane ba kanmu kawai ba

Yadda Za Mu Nuna Cewa Muna Ƙaunar Mutane

Yadda Za Mu Nuna Cewa Muna Ƙaunar Mutane

Da yake dukanmu ’ya’yan Adamu ne, daga iyali ɗaya muka fito. Ya kamata mutanen da suka fito daga iyali ɗaya su ƙaunaci juna kuma su daraja juna. Amma a yau yana da wuya mutane su nuna irin wannan ƙaunar. Ba haka Allah yake so ’yan Adam su kasance ba.

ABIN DA NASSOSI MASU TSARKI SUKA FAƊA GAME DA ƘAUNA

“Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”​—LITTAFIN FIRISTOCI 19:18.

“Ku ƙaunaci waɗanda ba sa ƙaunarku.”​—MATIYU 5:44.

ME ZAI NUNA CEWA MUNA ƘAUNAR MUTANE?

Ga abin da Allah ya faɗa game da nuna ƙauna a 1 Korintiyawa 13:​4-7:

“Ƙauna tana da haƙuri da kirki.”

Ka yi tunani a kan wannan: Yaya za ka ji idan mutane suna haƙuri da kai, suna maka kirki, kuma ba sa saurin fushi da kai ko da ka yi kuskure?

“Ƙauna ba ta . . . kishi.”

Ka yi tunani a kan wannan: Yaya za ka ji idan mutane suna yawan sa maka ido kuma suna kishin abin da kake da shi?

Ƙauna “ba ta ƙin kula da yadda waɗansu za su ji.”

Ka yi tunani a kan wannan: Yaya za ka ji idan mutane suna daraja ra’ayinka kuma ba sa cewa sai ka bi ra’ayinsu a kullum?

Ƙauna “ba ta riƙe laifi a zuciya.”

Ka yi tunani a kan wannan: Allah yana gafarta wa mutanen da suka yi zunubi, muddin sun tuba. “Ba zai yi ta tsawatarwa kullum ba, ba kuwa zai yi ta yin fushi” ba. (Zabura 103:9) Idan muka yi wa wani laifi kuma ya gafarta mana, hakan yana sa mu murna. Don haka, ya kamata mu ma mu dinga gafarta wa mutane.​—Zabura 86:5.

“Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta.”

Ka yi tunani a kan wannan: Idan wani abu marar kyau ya same mu, ba za mu ji daɗi ba idan wasu suka yi mana dariya. Don haka, bai kamata mu yi murna idan mun ga wasu a cikin matsala ba, ko da sun taɓa wulaƙanta mu a dā.

Idan muna so Allah ya yi mana albarka, wajibi ne mu ƙaunaci mutane ko da inda muka fito, da addininmu da shekarunmu ba ɗaya ba ne da su. Kuma za mu iya yin hakan ta wajen taimaka wa duk wanda yake cikin matsala.