Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wane ne Sarkin Mulkin Allah?

Wane ne Sarkin Mulkin Allah?

Allah ya sa marubutan Littafi Mai Tsarki da dama su rubuta abubuwan da za su taimaka mana mu san wanda zai zama Sarkin Mulkin Allah. Sarkin zai zama:

  • Wanda Allah ya zaɓa. “Na naɗa sarkina. . . . Zan ba ka al’ummai su zama gādonka, dukan duniya ta zama mallakarka.”​—Zabura 2:​6, 8.

  • Daga zuriyar Sarki Dauda. ‘Dominmu aka haifi yaro! Dominmu aka ba da ɗa! Ƙaruwar mulkinsa za ta ci gaba, mulkinsa zai kasance da salama har abada. Zai gāji kujerar mulkin kakansa Dauda, zai kafa ya riƙe shi.’​—Ishaya 9:​6, 7.

  • Haifaffen Betelehem. “Ke garin Betelehem . . . daga cikinki wani zai fito domina wanda zai yi mulki . . . ikon sunansa, za a san da shi ko’ina a duniya.”​—Mika 5:​2, 4.

  • Wanda mutane suka ƙi kuma za a kashe shi. “Aka rena shi, aka ɗauke shi kamar shi ba kome ba. . . . An soke shi saboda zunubanmu, aka yi masa rauni saboda laifofinmu.”​—Ishaya 53:​3, 5.

  • Wanda za a ta da shi daga mutuwa kuma a ɗaukaka shi. “Ba za ka bar raina a [“Kabari,” New World Translation] ba, ko ka bar mai ƙaunarka ya ruɓa ba. . . . Zama a hannun damanka, jin daɗi ne har abada.”​—Zabura 16:​10, 11.

Abin da Ya Sa Yesu Ne Ya Fi Dacewa Ya Zama Sarki

A duk tarihin ’yan Adam, mutum ɗaya ne kawai ya dace ya zama sarki bisa ga wannan kwatancin; mutumin shi ne Yesu Kristi. Tun kafin Maryamu ta haifi Yesu, wani mala’ika ya gaya mata cewa: “Allah zai ba shi kujerar mulkin kakansa Dauda. . . . Mulkinsa kuma ba zai ƙare ba!”​—Luka 1:​31-33.

Yesu bai yi sarauta a lokacin da yake duniya ba. A maimakon haka, daga sama ne zai yi sarauta a matsayin Sarkin Mulkin Allah. Me ya sa shi ne ya cancanci ya zama Sarki? Bari mu ga wasu abubuwan da ya yi sa’ad da yake duniya.

  • Yesu ya damu da mutane. Yesu ya taimaka wa maza da mata, yara da manya, talakawa da masu kuɗi, har da waɗanda ba a san da su ba. (Matiyu 9:36; Markus 10:16) Sa’ad da wani kuturu ya roƙi Yesu cewa: “Idan ka yarda, kana iya ka tsabtace ni in zama marar ƙazanta,” Yesu ya tausaya masa kuma ya warkar da shi.​—Markus 1:​40-42.

  • Yesu ya koya mana yadda za mu faranta wa Allah rai. Ya ce: “Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga bin kuɗi duk gaba ɗaya.” Ya kuma ce wajibi ne mu riƙa yi wa mutane abin da muke so su yi mana. Ƙari ga haka, ya nuna cewa Allah ya damu da abin da muke tunani, da yadda muke ji, ba ayyukanmu kaɗai ba. Don haka, idan muna so mu faranta wa Allah rai, dole mu guji yin tunanin banza. (Matiyu 5:28; 6:24; 7:12) Yesu ya ce idan muna so mu yi farin ciki a rayuwa, dole ne mu san abin da Allah yake so mu yi kuma mu yi shi.​—Luka 11:28.

  • Yesu ya koya wa mutane yadda za su nuna ƙauna. Abubuwan da Yesu ya yi da kuma koyarwarsa sun ratsa zukatan masu sauraronsa. Kalmar Allah ta ce: “Taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koya musu kamar mutumin da yake da iko.” (Matiyu 7:​28, 29) Yesu ya koya wa mutane su ‘ƙaunaci waɗanda ba sa ƙaunarsu.’ Har ma a lokacin da aka rataye shi a kan gungume, ya yi addu’a cewa: “Uba, . . . ka gafarta musu, gama ba su san abin da suke yi ba.”​—Matiyu 5:44; Luka 23:34.

Yesu ne zai iya yin sarauta a hanyar da za ta amfane kowa. Amma yaushe ne zai soma sarauta?