Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Nineba birni ne da ke da gidaje da kuma abubuwan tarihi masu kyaun gaske

Ka Sani?

Ka Sani?

Mene ne ya faru da Nineba?

A WAJEN shekara ta 670 kafin haihuwar Yesu, Assuriya ce daular da ta fi girma a duniya. Dandalin British Museum Blog ya ce, “girman daular ya kai daga Kuburus ta yamma zuwa Iran ta gabas, kuma akwai lokacin da ya ma kai Masar. A lokacin, birnin tarayyarsu Nineba ce ta fi girma a duniya. Akwai lambuna masu kyaun gaske da manyan gine-gine da kuma manyan ma’adanar littattafai a birnin. Zane-zane a jikin bango a Nineba sun nuna cewa Sarki Ashurbanipal ya kira kansa “sarkin duniya,” kamar yadda wasu sarakunanta ma suka kira kansu. A lokacin, kamar dai ba za a iya cin Assuriya da Nineba a yaƙi ba.

A lokacin, Daular Assuriya Mai Girma ce daula mafi girma a duk duniya

Duk da haka, a lokacin da Assuriya ce ƙasa mafi iko a duniya, annabin Jehobah Zafaniya ya annabta cewa: “Yahweh zai . . . halaka Assuriya. Zai mai da Nineba kufai.” Ƙari ga haka, annabin Jehobah Nahum ma ya annabta cewa: “Ku kwashi azurfa! Ku kwashe zinariya! . . . Nineba ta lalace, ta halaka, ta zama kufai! . . . Duk waɗanda suka dube ki za su ja baya su ce, ‘Abin mamaki! Nineba ta zama kufai!’ ” (Zaf. 2:13; Nah. 2:​9, 10; 3:7) Wataƙila da mutane suka ji annabce-annabcen nan sun yi tunanin tambayoyin nan: “Hakan zai yiwu kuwa? Za a iya cin Assuriya da yaƙi duk da ƙarfinta? Mai yiwuwa ya yi musu wuya su gaskata da hakan.

Nineba ta zama kufai

Duk da haka, an ci ƙasar a yaƙi! A ƙarshen shekara ta 670 kafin haihuwar Yesu, Babiloniyawa da mutanen Midiya sun ci Assuriya da yaƙi. A ƙarshe, mutane sun daina zama a Nineba kuma an mance da birnin gabaki ɗaya! Wani littafin da The Metropolitan Museum of Art suka wallafa ya ce: “An hallaka birnin Nineba kuma daga baya, sai ta wurin Littafi Mai Tsarki ne ake jin sunan birnin.” The Biblical Archaeology Society sun ce “babu ma wanda ya san ko babban birnin Assuriyawa ya taɓa wanzuwa.” Amma a shekara ta 1845, wani ɗan tone-tonen ƙasa mai suna Austen Henry Layard ya soma tone-tone a wurin da birnin Nineba take. Abubuwan da ya gano sun nuna cewa da gaske Nineba ta yi suna a dā.

Annabce-annabcen da aka yi game da Nineba da suka cika sun ƙarfafa bangaskiyarmu cewa annabcin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da gwamnatocin duniya ma zai cika.​—Dan. 2:44; R. Yar. 19:​15, 19-21.