Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sunan Wani da ya Bayyana a Littafi Mai Tsarki a Tulu na Dā

Sunan Wani da ya Bayyana a Littafi Mai Tsarki a Tulu na Dā

A shekara ta 2012, an tono wani tulun da ya farfashe da ya yi shekaru 3,000 a cikin ƙasa kuma wannan tulun ya sa masana sun soma bincike sosai. Me suka gani a tulun da ya jawo hankalinsu? Ba tulun ba ne, amma rubutun da ke jikinsa ne.

Masu bincike sun harhaɗa tulun don su iya karanta rubutun Kan’aniyawa da ke jikinsa. Abin da yake a rubuce shi ne: “Eshba’al Ben [ɗan] Beda’.” Wannan shi ne lokaci na farko da masu tonon ƙasa suka sami wannan sunan a wani rubutu na dā.

Littafi Mai Tsarki ya ambata wani mutum mai suna Eshbaal, kuma ɗan Sarki Saul ne. (1 Laba. 8:33; 9:39) Farfesa Yosef Garfinkel da ke cikin waɗanda suka tono tulun ya ce: “Wannan sunan Eshba’al yana cikin Littafi Mai Tsarki, kuma masana sun fahimci cewa an yi amfani da shi ne a lokacin Sarki Dauda.” Mutane da yawa suna ganin cewa an yi amfani da wannan sunan a dā ne kawai. Kuma wannan abin da masu tonon ƙasa suka gano ya ƙara tabbatar mana cewa duk abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne.

A wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki an yi amfani da sunan Ish-bosheth maimakon Eshbaal don an sauya “baal” da “bosheth.” (2 Sam. 2:10) Me ya sa? Masu bincike sun ce: “A littafin Sama’ila na biyu ba a yi amfani da sunan Eshba’al ba, saboda ya yi kama da sunan allan Kan’aniyawa wato Ba’al, amma a cikin littafin Labarbaru . . . an yi amfani da sunan nan Eshbaal.”