Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Ra’ayinka Game da Nan Gaba?

Mene Ne Ra’ayinka Game da Nan Gaba?

Shin duniyar nan za ta . . .

  • ci gaba da kasancewa yadda take ne?

  • ƙara lalacewa ne?

  • gyaru ne?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Allah . . . zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4, Littafi Mai Tsarki.

ABIN DA ZA KA IYA MORA SABODA ALKAWARIN NAN

Za ka more aiki mai kyau kuma mai gamsarwa.—Ishaya 65:21-23.

Ba za ka ƙara yin ciwo ko wahala ba.—Ishaya 25:8; 33:24.

Za ka yi farin ciki sosai tare da iyali da abokai har abada.—Zabura 37:11, 29.

ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?

Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai biyu:

  • Allah yana da iko ya cika alkawarin da ya yi. A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah Allah ne kaɗai aka kira “Mai-iko duka” domin shi ne ke da iko marar iyaka. (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Saboda haka, zai iya cika alkawarinsa na mai da wannan duniya ta zama wuri mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ga Allah dukan abu ya yiwu.”—Matta 19:26.

  • Allah yana ɗokin cika alkawarinsa. Alal misali, Jehobah yana “marmarin” ta da matattu don su sake rayuwa.—Ayuba 14:14, 15.

    Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa Yesu, Ɗan Allah ya warkar da masu ciwo. Me ya sa ya yi hakan? Domin yana son yin hakan. (Markus 1:40, 41) Kamar Ubansa, Yesu ya so ya taimaki mabukata.—Yohanna 14:9.

    Saboda haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah da Yesu suna so su taimaka mana mu ji daɗin rayuwa a nan gaba!—Zabura 72:12-14; 145:16; 2 Bitrus 3:9.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR

Ta yaya Allah zai mai da duniya ta zama wuri mai kyau?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a MATTA 6:9, 10 da kuma DANIYEL 2:44.