Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne ke Kawo Farin Ciki a Iyali?

Mene Ne ke Kawo Farin Ciki a Iyali?

Kana ganin . . .

  • ƙauna ce?

  • kuɗi ne?

  • ko wani abu dabam?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

Albarka ta . . . tabbata ga waɗanda ke jin maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”—Luka 11:28, Littafi Mai Tsarki.

ABIN DA ZA KA IYA MORA IDAN KA BI ƘA’IDAR NAN

Ƙauna.—Afisawa 5:28, 29.

Mutunci.—Afisawa 5:33.

Kwanciyar hankali.—Markus 10:6-9.

ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?

Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai biyu:

  • Allah ne Tushen iyali. Littafi Mai Tsarki ya ce “kowane iyali . . . ya sami sunansa” daga Jehobah Allah. (Afisawa 3:14, 15) Abin nufi shi ne, Jehobah ne ya kafa iyali. Me ya sa sanin hakan yake da muhimmanci?

    Ka yi la’akari da wannan: Idan ka ci wani abinci mai daɗi kuma kana son ka san kayan miya da aka dafa abincin da su, wane ne za ka tambaya? Wadda ta dafa abincin, ko ba haka ba?

    Hakazalika, idan muna son mu san abubuwan da ke kawo farin ciki a iyali, zai dace mu nemi shawara daga wurin Wanda ya kafa iyali, wato, Jehobah.—Farawa 2:18-24.

  • Allah ya damu da ku. Zai dace iyalai su nemi shawara daga wurin Jehobah, wato, shawarar da yake tanadarwa ta Kalmarsa. Me ya sa? “Domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:6, 7) Jehobah yana ƙaunar ku kuma shawararsa tana da amfani sosai!—Misalai 3:5, 6; Ishaya 48:17, 18.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR

Me zai iya taimaka maka ka kasance miji ko mata ko kuma mahaifin kirki?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a AFISAWA 5:1, 2 da kuma KOLOSIYAWA 3:18-21.