Koma ka ga abin da ke ciki

Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?

Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?

Mece ce amsarka?

  • E.

  • A’a.

  • Wataƙila.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Allah . . . zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4, Littafi Mai Tsarki.

ABIN DA ZA KA IYA MORA SABODA ALKAWARIN NAN

Za ka kasance da tabbaci cewa ba Allah ne sanadin matsalolinmu ba.—Yaƙub 1:13.

Za ka sami kwanciyar hankali saboda sanin cewa Allah ya damu da mu sa’ad da muke shan wahala.—Zakariya 2:8.

Za mu kasance da bege cewa dukan wahala za ta ƙare.—Zabura 37:9-11.

ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?

Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai biyu:

  • Allah ya tsani wahala da rashin adalci. Ka yi la’akari da yadda Jehobah Allah ya ji sa’ad da aka tsananta wa mutanensa a zamanin dā. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya damu saboda “waɗanda suka tsananta masu da wulaƙanci.”—Alƙalawa 2:18.

    Allah ya tsani waɗanda suke wulaƙanta mutane. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana ƙyamar “masu-zub da jinin mara-laifi.”—Misalai 6:16, 17.

  • Allah ya damu da kowannenmu. Hakika, kowane mutum yana ‘sane da nasa annoba da nasa baƙin ciki,’ kuma Jehobah ma yana sane da hakan!2 Labarbaru 6:29, 30.

    Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa wajen kawo ƙarshen matsalolin da kowannenmu yake fuskanta. (Matta 6:9, 10) A yanzu hakan ma, yana ƙarfafa dukan waɗanda suke biɗar sa da gaske.—Ayyukan Manzanni 17:27; 2 Korintiyawa 1:3, 4.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR

Me ya sa Allah ya kyale shan wahala?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a ROMAWA 5:12 da kuma 2 BITRUS 3:9.