Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 9

Shin Ya Kamata in Yi Imani da Koyarwar Juyin Halitta?

Shin Ya Kamata in Yi Imani da Koyarwar Juyin Halitta?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Rayuwa ba ta da ma’ana idan koyarwar juyin halitta (wato, evolution) gaskiya ce. Idan da gaske ne cewa an halicci abubuwa, za mu samu amsoshi masu gamsarwa game da tambayoyi na rayuwa da kuma abin da zai faru a nan gaba.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Alex ya rikice. Ya yi imani da Allah kuma ya gaskata cewa Allah ne ya halicci kome. Amma yau malaminsa mai koyar da ilimin halittu ya ce juyin halitta gaskiya ne domin binciken da ’yan kimiyya suka yi ya gano hakan. Alex ya ce ba ya so a mai da shi saniyar ware, ‘Idan masana kimiyya sun tabbatar da cewa juyin halitta gaskiya ne, wane ne ni in musanta abin da suka ce.’

A ce kai ne Alex, za ka amince da koyarwar juyin halitta domin littattafan kimiyya sun nuna cewa hakan gaskiya ne?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

Mutanen da suka yi imani da wannan ra’ayin da waɗanda ba su yi imani da hakan ba, suna saurin faɗin abin da suka yi imani da shi ba tare da sanin dalilin da ya sa suka yi imani da hakan ba.

  • Wasu mutane sun gaskata cewa Allah ne ya halicci dukan abubuwa domin hakan addininsu ya koyar da su.

  • Wasu mutane kuma sun yi imani da juyin halitta domin an koyar da su a makaranta.

TAMBAYOYI SHIDA DA ZA KA YI LA’AKARI DA SU

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane gida akwai mai-kafa shi; amma wanda ya kafa dukan abu Allah ne.” (Ibraniyawa 3:4) Shin ya kamata ka gaskata da hakan?

Yin da’awa cewa babu Mahalicci yana kama da cewa babu wanda ya gina wannan gidan

RA’AYI: Kome a sama da ƙasa sun bayyana ne haka farat ɗaya.

1. Mene ne ko kuma wane ne ya sa abubuwa suka bayyana haka farat ɗaya?

2. Wanne ne ya fi dacewa? A ce abubuwa sun bayana haka kwatsam ko kuma wani ne ya halicce su?

RA’AYI: Mutane sun fito ne daga dabbobi.

3. Idan ’yan Adam sun fito ne daga dabbobi, alal misali gwaggon biri, me ya sa akwai bambanci sosai tsakanin basirar da ’yan Adam suke da ita da na gwaggon biri?

4. Me ya sa halittu, kome ƙanƙantarsu, suke da wuyar fahimta?

RA’AYI: An tabbatar da cewa juyin halittu gaskiya ne.

5. Shin wanda yake ba da wannan hujjar ya taɓa bincika batun da kansa?

6. Mutane nawa ne suka yi imani da koyarwar juyin halitta domin an gaya musu cewa dukan masu basira sun yi imani da shi?

Julia ta ce: “Idan kana tafiya a jeji, sai ka iske wani gidan katako mai kyau sosai, shin za ka ce: ‘Abin mamaki! Itatuwa sun faɗo kuma sun gina gida da kansu?’ A’a! Ba za ka yi wannan tunanin ba. To me ya sa za ka yi imani cewa duk wani abin da ke sama da ƙasa sun bayyana ne haka farat ɗaya?”

Gwen ta ce: “Idan wani ya gaya maka cewa na’urorin buga littattafai sun fashe kuma tawadar da ke cikin na’urorin ta tarwatse a jikin bango da silin, sai hakan ya zama ƙamus, za ka yarda?”

ME YA SA YA KAMATA KA YI IMANI DA ALLAH?

Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa ka ka yi amfani da hankalinka. (Romawa 12:1) Saboda haka, bai kamata ka yi imani da Allah don

  • YADDA KAKE JI BA (A ganina, dole ne akwai wanda ya fi kowa iko)

  • RA’AYIN WASU BA (Ina zama a yankin da mutane suke son ibada)

  • MATSI BA (Iyayena sun rene ni in yi imani da Allah, saboda haka, ban da zaɓi)

Maimakon haka, ka kasance da ƙwaƙƙwaran dalilai don bayyana imaninka.

Teresa ta ce: “A duk lokacin da nake cikin aji kuma malaminmu yana bayyana mana yadda jikinmu yake aiki, hakan na sa in tabbatar wa kaina cewa akwai Allah. Duka gaɓoɓin jikinmu, har da ƙananan gaɓoɓi suna da aikinsu, kuma a yawancin lokaci, waɗannan gaɓoɓin suna aikinsu ba tare da saninmu ba. Hakika, jikin ’yan Adam abin al’ajabi ne!”

Richard ya ce: “Idan na ga gini mai tsawo, da babban jirgin ruwa da kuma mota, ina tambayar kaina, ‘waye ne ya ƙera waɗannan abubuwan?’ Hakika, waɗanda suka ƙera mota suna da basira sosai. Wajibi ne dukan ɓangarorin motar su yi aiki da kyau don kome ya tafi daidai. Idan wani ne ya ƙera mota, to babu shakka, akwai wanda ya halicci ’yan Adam.”

Anthony ya ce: “Yayin da na ci gaba da yin nazarin kimiyya, hakan na sa in fahimci cewa babu wata shaidar da ta tabbatar da juyin halitta. . . . A ganina, ya fi ‘wuya’ a gaskata da koyarwar juyin halitta fiye da gaskata cewa akwai Mahalicci.”

ABIN DA ZA KA YI TUNANI A KAI

Duk da cewa sun yi shekaru da yawa suna bincike, har ila masana kimiyya suna ba da bayanai dabam-dabam a kan juyin halitta. Idan masana kimiyya sun kasa kasancewa da ra’ayi guda, duk da cewa su ƙwararru ne, shin kana ganin laifi ne idan ka yi shakkar wannan koyarwar?