Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 9

Ku Bauta wa Jehobah a Matsayin Iyali

Ku Bauta wa Jehobah a Matsayin Iyali

“Ku yi sujada ga wanda ya yi sama da duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 14:7

Kamar yadda kuka koya a wannan ƙasidar, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawarwari da yawa da za su taimaka wa ku da iyalinku. Jehobah yana so ku zauna lafiya. Ya yi alkawari cewa idan kuka ba wa ibadarsa fifiko a rayuwarku, sauran “waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku.” (Matta 6:33) Allah yana so ku ƙulla abota da shi. Saboda haka, ku yi iyakacin ƙoƙarinku ku ƙarfafa dangantakarku da Allah. Babu gatan da ya kai wannan a rayuwar ɗan Adam.Matta 22:37, 38.

1 KU ƘARFAFA DANGANTAKARKU DA JEHOBAH

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Zan zama Uba gare ku, ku za ku zama ’ya’ya maza da mata gare ni, in ji Ubangiji.’ (2 Korintiyawa 6:18) Allah yana so ku zama abokansa na kud da kud. Addu’a tana ɗaya daga cikin hanyoyin yin hakan. Jehobah yana so ku riƙa yin “addu’a ba fasawa.” (1 Tasalonikawa 5:17) Yana ɗokin jin abin da ke cikin zuciyarku. (Filibiyawa 4:6) Idan ka yi addu’a tare da iyalinka, za su ga cewa ka gaskata da Allah sosai.

Ƙari ga yin addu’a ga Allah, kuna bukatar ku saurare shi. Za ku iya yin hakan ta wajen karanta Kalmarsa da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. (Zabura 1:1, 2) Ku yi bimbini a kan abubuwan da kuka koya. (Zabura 77:11, 12) Kuna bukatar ku riƙa halartan taron Kirista idan kuna so ku saurari Allah.—Zabura 122:1-4.

Yin wa’azi ma zai taimaka muku ku ƙarfafa dangantakarku da Jehobah. Idan kuna yin hakan a kai a kai, za ku kusaci Jehobah sosai.Matta 28:19, 20.

SHAWARA:

  • Ku keɓe lokaci don yin addu’a da kuma karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana

  • A matsayin iyali, ku ɗauki ibada da muhimmanci fiye da nishaɗi da shaƙatawa

2 KU JI DAƊIN IBADA TA IYALI

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙub 4:8) Kuna bukatar ku tsara yadda za ku yi ibada ta iyali* kuma ku riƙa bin wannan tsarin. (Farawa 18:19) Ƙari ga hakan, wajibi ne ku yi nufin Allah a kowace rana. Ku ƙarfafa dangantakar iyalinku da Allah ta wajen tattaunawa game da shi “sa’anda kana zaune cikin gidanka, da sa’anda ka ke tafiya a kan hanya, da sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi.” (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Ku ƙudurta cewa za ku bi misalin Joshua, wanda ya ce: “Da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”Joshua 24:15.

SHAWARA:

  • Ku kasance da tsarin ibada ta iyali da zai shafi bukatun kowa a iyalinku