Koma ka ga abin da ke ciki

Me zan yi don in daina wasa da gabana?

Me zan yi don in daina wasa da gabana?

BABI NA 25

Me zan yi don in daina wasa da gabana?

Wani mai suna Luiz ya ce: “Na soma wasa da gabana (al’aurata) tun ina dan shekara takwas. Daga baya na koyi cewa Allah ba ya son hakan. A duk lokacin da na fada wa jarabar, abin yakan dame ni sosai. Na dauka cewa Allah ba zai taba kaunar mutum irina ba.”

IDAN mutum ya soma balaga, yakan ji sha’awar yin jima’i sosai. Abin da ke sa wasu mutane su soma wasa da gabansu ko al’aurarsu (istimina’i) ke nan. * Mutane da yawa sukan ce, “Ai ba wani abu ba ne tun da jikinka ne.” Amma akwai babban dalilin da ya sa ya kamata mu guji wannan halin. Manzo Bulus ya ce: “Saboda haka, sai ku kashe halin sha’awace-sha’awacen duniya a zuciyarku, wato iskanci, da aikin lalata, da muguwar sha’awa.” (Kolosiyawa 3:5) Idan kana wasa da al’aurarka, kana kara wa kanka sha’awar yin lalata ne maimakon ka kashe sha’awar. Ka yi la’akari kuma da yadda wannan halin yake shafan mu:

● Wasa da gaba yakan sa mutum ya zama da son kai. Domin sa’ad da namiji ko tamace take hakan, abin da suke sa a gaba kawai shi ne jin dadin kansu.

● Idan mutum yana wasa da gabansa, zai yi masa wuya ya daraja mata. Zai dinga gani kamar abin da ake yi da su kawai shi ne yin jima’i. Haka ma yake da mace mai wannan halin.

● Idan namiji ko mace ta saba wasa da gabanta, yakan yi wuya mijinta ko matarsa ta gamsar da shi idan ya yi aure.

Don haka, maimakon ka rika wasa da gabanka don ka gamsar da wannan sha’awar, ka koyi yadda za ka kame kanka. (1 Tasalonikawa 4:​4, 5) Ta yaya za mu yi hakan? Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu mu guji yanayoyin da za su iya tayar mana da sha’awa. (Karin Magana 5:​8, 9) Amma me za ka yi idan wasa da gabanka ya riga ya zama maka jiki? Kila ma ka yi kokari ka daina, amma ka kasa. Mai yiwuwa ka ga kamar ba za ka iya dainawa ba kuma ba za ka taba faranta wa Allah rai yadda ya kamata ba. Yadda wani yaro mai suna Pedro ya ji ke nan. Ya ce: “A duk lokacin da na yi wasa da gabana, abin yakan dame ni sosai. Na ga kamar Allah ba zai taba gafarta min ba. Yin addu’a ma ya bi ya min wuya.”

Idan haka kake ji, kada ka fid rai. Akwai mutane da yawa, matasa da manya da suka shawo kan wannan matsalar. Kai ma za ka iya!

Abin da Za Ka Yi Idan Zuciyarka Tana Damunka

Kamar yadda muka tattauna dazu, zuciyar wadanda suke wasa da gabansu takan dame su sosai. “Wannan bakin ciki iri na halin Allah” ne kuma zai iya taimaka maka ka daina zunubin da kake yi. (2 Korintiyawa 7:11) Amma idan damuwar ta yi yawa, za ta iya sa ka karaya kuma ka fid da rai.​—Karin Magana 24:10.

Don haka, ka yi kokari ka fahimci ra’ayin Allah game da batun. Yin wasa da gabanka hali ne marar kyau. Zai iya sa ka ‘zama bawan sha’awace-sha’awace da kwadayi iri-iri,’ kuma ya sa ka rika tunani marar kyau. (Titus 3:3) Amma kuma yin wasa da gaba bai kai yin fasikanci ko zina muni ba. (Yahuda 7) Idan kana wasa da gabanka, kada ka dauka cewa Allah ba zai taba gafarta maka ba. Abin da zai taimaka maka shi ne, idan sha’awar ta taso, ka ki kuma ka ci gaba da kokartawa!

A duk lokacin da ka fada wa jarabar, za ka ji bakin ciki. Amma ka tuna cewa tun da kokarin dainawa kake yi, kai ba mugu ba ne. Don haka, kada ka fid da rai, a maimakon haka, ka san abin da ya sa ka sake fada wa jarabar kuma ka yi kokarin kauce masa.

Ka nemi lokaci ka yi tunani sosai a kan kaunar da Allah yake mana da jin kansa. Dawuda marubucin zabura wanda shi ma ya taba yin abubuwa marasa kyau, ya ce: “Kamar yadda baba yake tausaya wa ’ya’yansa, haka Yahweh yake tausaya wa masu tsoronsa. Gama shi ya san abin da aka yi mu da shi, yana kuma tuna cewa mu kurar kasa ne.” (Zabura 103:​13, 14) A koyaushe, Jehobah yana sane da kasawarmu kuma shi “mai yin gafara.” (Zabura 86:5) Duk da haka, yana so mu yi iya kokarinmu wajen yi masa biyayya. Yanzu wadanne matakai za su taimaka maka ka daina yin wasa da gabanka?

Ka bincika irin abubuwan da kake kallo. Kana kallon fina-finai ko shirye-shiryen telibijin masu ta da sha’awa? Ko akwai dandalin da kake shiga da suke nuna abubuwan ta da sha’awa? Wani marubucin zabura ya yi addu’a ga Allah ya ce: “[Ka] kawar da idanuna daga abubuwan banza, [ka] rayar da ni cikin hanyarka.” *​—Zabura 119:37.

Ka yi kokari ka rika tunani a kan abubuwa masu kyau. Wani kirista mai suna William ya ce: “Kafin ka kwanta, ka karanta wani abin da ke Littafi Mai Tsarki. Zai dace abu na karshe da za mu yi tunaninsa kafin mu kwanta ya zama na Allah. Yin hakan abu ne mai muhimmanci sosai.”​—Filibiyawa 4:8.

Ka ce a taimaka maka. Kunya za ta iya sa ka ki gaya ma wani abin da kake fama da shi. Amma abin da zai taimaka maka ka daina wannan hali marar kyau ke nan. Wani Kirista mai suna David ya ga tabbacin hakan. Ya ce: “Na gaya wa babana abin da ke faruwa, kuma ba zan taba mantawa da abin da ya gaya min ba. Ya kalle ni yana murmushi kuma ya ce, ‘Ka burge ni sosai da ka gaya mini.’ Ya san cewa bai min sauki in gaya masa batun ba. Abin da ya fada ya kara min kwarin gwiwar daina wannan halin.

“Sai babana ya nuna min wasu nassosi don ya tabbatar min cewa ni ba malalaci ba ne. Ya kuma nuna min wasu nassosi don ya taimaka min in ga cewa, yadda nake wasa da gabana bai dace ba ko kadan. Ya ce min in yi iya kokarina in guji yin hakan. Kuma ya ce wata rana, za mu sake maganar. Ya ce idan ma jarabar ta taso kuma na fada mata, kada in bar hakan ya sa ni sanyin gwiwa. A maimakon hakan, in kara dagewa don kada in yi saurin fada masa yadda na yi a karon da ya shige.” Shin David ya amfana da ya gaya ma wani matsalar da yake ciki kuwa? Kwarai da gaske. David ya ce: “Yadda na gaya ma wani abin da ke damu na da taimakon da na samu daga wurinsa ya amfane ni sosai. Ba abin da ya taimaka min a famar da na yi da wannan halin kamar yadda na gaya wa wani yanayin da nake ciki da taimakon da na samu daga wurinsa.” *

A BABI NA GABA Za mu bincika dalilin da ya sa bai dace wadanda ba su yi aure ba, su yi jima’i..

[Karin bayannai]

^ Sha’awar yin jima’i da ke zuwa wa mutum ba zato ba daya yake da wasa da al’aura ba. Alal misali, yaro zai iya tashiwa daga barci yana jin sha’awa sosai ko maniyi ya fita daga gabansa babu zato. Haka ma, sha’awa za ta iya taso wa ’yan mata ba zato musamman kafin su bi wata (lokacin al’ada) ko bayan hakan. Wannan ba daya yake da wadanda suke wasa da al’aurarsu ba domin su suke tayar wa kansu sha’awar.

^ Don karin bayani, ka duba babi na 33 na littafin nan Questions Young People Ask​—Answers That Work, Littafi na 2.

^ Don karin bayani, ka karanta littafin nan Questions Young People Ask​—Answers That Work, Littafi na 2 shafaffuka na 239-241.

NASOSI

“Ka guje wa mugayen sha’awace-sha’awace na matasa, ka sa kai ga neman adalci, da bangaskiya, da kauna, da kuma salama, tare da wadanda suke kira ga Ubangiji da zuciya mai tsabta.”​2 Timoti 2:22.

SHAWARA

Ka yi addu’a tun kafin sha’awar ta fi karfinka. Ka roki Jehobah ya ba ka “cikakken ikon da ya fi duka,” don kada ka fada wa jaraba.​—2 Korintiyawa 4:7.

SHIN KA SANI . . .

Idan rago ya ji sha’awar yin jima’i, yakan biye masa. Amma jarumi yakan kame kansa ko a lokacin da yake shi kadai.

ABUBUWAN DA ZAN YI!

Zan sa zuciyata ta rika tunanin abubuwan da suka dace ta wajen ․․․․․

Idan sha’awar ta taso min, maimakon in biye mata, zan ․․․․․

A kan wannan batun, ga wasu tambayoyi da zan so in yi wa iyayena ․․․․․

ME RA’AYINKA?

● Me ya sa yake da muhimmanci mu rika tuna cewa Jehobah “mai yin gafara” ne?​—Zabura 86:5.

● Da yake Allah ne ya yi mu yadda za mu iya jin sha’awar yin jima’i kuma ya ce ka rika kame kanka, hakan bai nuna cewa ya san za ka iya kame kanka ba?

[Bayani a shafi na 182]

Wata mai suna Sarah ta ce: “Da na shawo kan wannan matsalar, zuciyata ta daina damuna don ina yin abin Jehobah yake so, kuma ba na so in yi wasa da hakan!”

[Hoto a shafi na 180]

Idan kana gudu kuma ka fadi, ba sai ka koma ka soma gudun daga farko ba. Haka ma, idan kana kokarin daina wasa da gabanka kuma ka fada wa jarabar, ba ya nufin cewa kokarin da ka yi, ya zama banza.