Gabatarwa Don Wa’azi

Bidiyon da aka tsara don su taimaka mana mu soma tattauna Littafi Mai Tsarki da mutane.

Gabatarwar Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya

Shaidan ba ya son iyalai su zauna lafiya. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba da wasu shawarwari da iyalai za su iya bi don su zauna lafiya.

Za Ka So Ka Ji Albishiri?

Ishaya 52:7 ta ce akwai albishiri mai dadi a cikin Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa iyalinka ta zauna lafiya, ka sami abokan kirki da kuma kwanciyar hankali.

Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?

Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa za mu sake ganin ’yan’uwanmu da suka mutu a nan duniya.

Su Wane ne Shaidun Jehobah?

Mutane da yawa suna so san su waye ne Shaidun Jehobah. Ka sami karin bayani da ga wurinmu.