Koma ka ga abin da ke ciki

Umurni Game da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu

Umurni Game da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu

Abubuwan da Ke Ciki

1. Umurnin da aka bayar a nan zai taimaka wa dukan waɗanda suke da aiki a Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Zai dace waɗanda suke da aiki su duba umurnin da aka bayar a Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu da kuma waɗanda da aka bayar a nan, kafin su shirya aikin da aka ba su. A ƙarfafa dukan masu shela su nemi damar yin aiki a taron. Za a iya ba waɗanda suke halartar taro a kai a kai aiki, idan sun yarda da koyarwar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma rayuwarsu ta jitu da ƙaꞌidodinsa. Mai Kula da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu zai tattauna da duk wani marar shela da yake so ya soma yin aiki a taron. Shi zai gaya wa ɗalibin abin da zai yi don ya cancanci yin hakan, kuma idan ɗalibin ya riga ya cancanta zai gaya masa. Mai kula da taron zai yi hakan a gaban wanda yake nazari da ɗalibin (ko idan yaro ne zai yi hakan a gaban iyayensa da Shaidu ne). Abin da mutum zai yi kafin ya cancanci zama ɗalibi, ɗaya ne da abin da mutum zai yi don ya zama mai shela marar baftisma.—od-E babi na 8 sakin layi na 8.

 GABATARWAR TARO

2. Minti ɗaya. A kowane mako, bayan an yi waƙa da kuma adduꞌar buɗewa, mai gudanar da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu zai ambata abubuwan da za a tattauna a taron. Mai gudanar da taron ya mai da hankali ga batutuwan da za su amfani ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar.

  DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 3Jawabi: Minti goma. Za a ba da jigo da kuma muhimman darussa guda biyu ko uku a cikin Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Dattijo ko kuma bawa mai hidima da ya ƙware ne zai yi wannan jawabin. Idan an soma karatun sabon littafi na Littafi Mai Tsarki, za a nuna bidiyon gabatarwar littafin. Mai jawabin zai iya bayyana yadda jigon yake da alaƙa da bidiyon. Amma, ya tabbata cewa ya tattauna muhimman darussa da ke littafin taron. Idan da lokaci, ya bayyana hotunan da ke cikin littafin taron, an shirya su ne don su ba da ƙarin haske a kan batun da ake tattaunawa. Zai iya nemo bayanai daga wasu littattafai idan hakan zai inganta jawabinsa.

 4Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: Minti goma. Wannan sashe ne na tambayoyi da amsoshi, babu gabatarwa da kuma kammalawa. Dattijo ko kuma bawa mai hidima da ya ƙware ne zai yi aikin. Mai jawabin ya tambayi masu sauraro dukan tambayoyi biyun. Ƙari ga haka, shi ne zai zaɓa ko za a karanta nassosin ko aꞌa. Waɗanda za su yi kalami, su yi hakan cikin sakan 30 ko ƙasa da hakan.

 5Karatun Littafi Mai Tsarki: Minti huɗu. Namiji ne zai yi wannan karatun. Ɗalibin ya karanta ayoyin da aka ce ya karanta ba tare da ya yi gabatarwa ko kammalawa ba. Mai gudanar da taron zai mai da hankali ne musamman ga taimaka wa ɗaliban su yi karatu yadda za a fahimta kuma karatun ya fita sarai. Ƙari ga haka, ya mai da hankali ga yadda ɗaliban suke dakatawa a inda ya dace da yadda suke ɗaga murya da saukar da murya, da kuma yadda suke yin karatu a hanyar da suka saba magana. Da yake a wasu lokuta ayoyin da aka ce a karanta za su iya yin yawa ko su yi kaɗan, mai kula da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu ya yi laꞌakari da abin da ɗalibin zai iya yi kafin ya ba shi aikin.

 KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

6. Minti sha biyar. An tsara wannan sashen taron ne don ya ba wa kowa zarafin shirya yadda zai yi waꞌazi da inganta yadda muke taɗi da kuma yin waꞌazi da koyarwa. Idan da bukata, za a iya ba wa dattawa aiki a sashen nan. Zai dace kowane ɗalibi ya bi abin da aka ce ya yi a littafin Koyarwa ko kuma Ƙaunar Mutane da ke cikin baka biyu,, kusa da inda aka rubuta aikin da za ka yi a Littafin Taro. A wasu lokuta, za a iya samun sashen da aka ce a tattauna. Dattijo ko bawa mai hidima da ya ƙware ne zai gudanar da irin wannan sashen.—Ka duba  sakin layi na 15 don ka ga yadda ake gudanar da sashen da aka ce a tattauna.

7Fara Magana da Mutane: Za a iya ba namiji ko mace wannan aikin. Idan aka ba namiji, to wanda zai yi aikin tare da shi ya kasance namiji ko idan zai yi amfana da mace ce ta zama daga iyalinsu. Idan mace ce, wadda za ta yi aikin tare da ita ta kasance ta mace ko idan namiji ne ya zama daga iyalinsu. Ɗalibin da mataimakinsa za su iya yin aikin a tsaye ko a zaune.—Don samun ƙarin bayani game da abin da ɗalibi zai yi da yadda za a yi, ka duba  sakin layi na 12 da  13

  8Komawa Ziyara: Za a iya ba namiji ko mace wannan aikin. Idan aka ba namiji ne, ya yi aikin da namiji, idan mace ce kuma, ta yi aikin da ta mace. (km-E 5/97 shafi na 2) Ɗalibin da wanda za su yi aikin tare za su iya yin aikin a tsaye ko a zaune. Ɗalibin ya nuna yadda za a sake tattaunawa da wanda aka yi masa waꞌazi.—Don samun ƙarin bayani game da abin da ɗalibi zai yi da yadda za a yi, ka duba  sakin layi na 12 da  13.

 9Almajirtarwa: Za a iya ba namiji ko mace wannan aikin. Idan aka ba namiji ne, ya yi aikin da namiji, idan mace ce kuma, ta yi aikin da ta mace. (km-E 5/97 shafi na 2) Ɗalibin da wanda za su yi aikin tare za su iya yin aikin a tsaye ko a zaune. Ɗalibin ya yi kamar sun riga sun soma nazari. Ba a bukatar gabatarwa ko kuma kammalawa, sai ko an ce ɗalibin ya yi aiki a kan gabatarwa ko kammalawa. Za a iya karanta sakin layin duka, amma ba dole ba ne.

 10Ka Bayyana Imaninka: Idan aka ce a yi sashen nan a matsayin jawabi, namiji ne zai yi. Idan kuma aka ce a yi sashen nan a matsayin gwaji, mace ce ko namiji ne zai iya yi. Idan aka ba namiji, to wanda zai yi aikin tare da shi ya kasance namiji ko idan zai yi amfana da mace ce ta zama daga iyalinsu. Idan mace ce, wadda za ta yi aikin tare da ita ta kasance ta mace ko idan namiji ne ya zama daga iyalinsu. Ɗalibin ya yi amfani da kayan binciken da aka ba shi don ya amsa tambayar da ya kamata ya tattauna da kyau kuma ya yi hakan cikin basira. Ɗalibin ne zai zaɓa ko zai yi amfani da kayan binciken da aka ba shi ko aꞌa.

 11Jawabi: Namiji ne zai yi wannan aikin a matsayin jawabi ga ikilisiya. Idan an ɗauko jawabin daga ƙarin bayani na 1 cikin littafin Ƙaunar Mutane, ɗalibin ya bayyana yadda za a yi amfani da ayoyin a waꞌazi. Alal misali, zai iya bayyana lokacin da ya kamata a yi amfani da wata aya ko abin da ayar take nufi ko kuma yadda za a yi amfani da ita wajen tattauna da wani. Idan an ɗauko jawabin daga wani batu ne a cikin darussan da ke littafin Ƙaunar Mutane, ɗalibin ya mai da hankali ga yadda za a yi amfani da batun a waꞌazi. Zai iya yin amfani da misalin da aka bayar a batu na 1 na darasin ko ayoyin da ke wurin don ya yi bayani.

   12Abin da Ɗalibi Zai Yi: Za a yi amfani da abin da ke wannan sakin layi da na biye da shi a aikin “Fara Magana da Mutane” da “Komawa Ziyara.” Sai dai an ba da wani umurni dabam, abin da ake so ɗalibin ya yi shi ne, ya gaya wa maigidan wani batun da ya dace da shi daga Littafi Mai Tsarki kuma ya gaya masa abin da za su tattauna a nan gaba. Ɗalibin ne zai zaɓi batun da zai tattauna da ya dace da lokacin da kuma yankin. Idan yana so, zai iya ba da wani littafi ko ya nuna bidiyo daga Kayan Aiki don Koyarwa. Maimakon su haddace abin da za su faɗa, zai dace ɗalibai su riƙa yi kamar suna tattaunawa ne da mutane yadda suka saba, kuma su nuna sun damu da mai sauraron.

   13Yadda Za A Yi: Ɗalibin ya bi shawarar da aka ba shi ya yi aiki a kai bisa ga yankinsu. Alal misali:

  1.  (1) Waꞌazi Gida-gida: Za a yi wannan aikin yadda ake waꞌazi gida-gida, ko da mun sami maigidan a gidansa ne ko ta waya ko ta wasiƙa. Da kuma yadda za a koma ziyara don ku ci gaba da tattaunawa.

  2.  (2) Saꞌad da Kake Ayyuka na Yau da Kullum: Za a yi aikin nan ne ta wajen somawa da taɗi, saꞌan nan ka yi wa mutumin waꞌazi. Hakan ya haɗa da yi wa mutane waꞌazi a wurin aiki ko makaranta ko unguwarku ko a motar haya ko kuma a wani wurin da kake ayyukanka na yau da kullum.

  3.  (3) Waꞌazi a Inda Jamaꞌa suke: Za a iya yin wannan aiki kamar ana waꞌazi da amalanke ko yin waꞌazi a wurin da ake kasuwanci ko a tituna ko a tasha ko wurin faka motoci ko kuma a duk inda ake samun mutane.

 14Yadda Za A Yi Amfani da Bidiyoyi da Littattafai: Ɗalibin ne zai duba yanayin ya ga ko zai yi amfani da wani bidiyo ko littafi. Idan akwai bidiyo a aikin ko kuma ɗalibin yana so ya yi amfani da wani bidiyo, ya gabatar kuma su tattauna, amma kada ya kunna bidiyon.

  RAYUWAR KIRISTA

15. Bayan waƙa, za a gudanar da sashe ɗaya ko biyu cikin minti 15 da zai taimaka wa masu sauraro su bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Za a iya ba dattijo ko kuma bawa mai hidima da ya ƙware wannan sashen, sai dai ko an ba da wani umurni dabam. Amma dattijo ne kaɗai zai gudanar da sashen bukatun ikilisiya. Idan aka ce a yi sashen nan a matsayin tattaunawa, mai aikin zai iya yin wasu tambayoyi haɗe da waɗanda suke cikin sashen. Zai dace kada ya yi dogon gabatarwa don ya samu isashen lokacin tattauna muhimman batutuwa, kuma ya ba masu sauraro damar yin kalami. Idan aka ce a gana da wani, zai dace wanda za a gana da shi ya yi hakan a kan dakalin magana maimakon ya yi a wurin zamansa idan zai yiwu.

  16Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: Minti talatin. Dattijon da ya ƙware ne zai yi wannan aikin. (A ikilisiyoyin da ba su da dattawa da yawa, bawa mai hidima da ya ƙware zai iya yin wannan aikin.) Rukunin dattawa ne za su zaɓi waɗanda suka ƙware da za su riƙa gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Ya kamata waɗanda aka zaɓa su fitar da muhimman darussa da za su taimaka wa ikilisiya, kuma su sa a karanta nassosin da suka dace domin ꞌyanꞌuwa su amfana. Ban da haka ma, kada su wuce lokacin da aka ba su. Waɗanda aka zaɓa su gudanar da nazarin, za su amfana ta wajen karanta bayani daga cikin umurnin da aka tanadar a kan yadda za a gudanar da sashen amsoshi da tambayoyi. (w23.04 shafi na 24, akwati) Bayan an gama tattauna sakin layi da aka shirya na makon, sai a kammala nazarin ba tare da ɓata lokaci ba. A kowane mako, za a iya canja mai gudanar da nazarin da kuma wanda zai yi karatu. Idan mai gudanar da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu ya ce a taƙaita nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, to mai gudanar da nazarin ne zai tsai da shawara a kan yadda zai yi hakan. Yana iya sa a karanta wasu sakin layin kuma a bar wasu.

  KAMMALAWA

17. Minti uku. Mai gudanar da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu zai yi bitar muhimman darussa da aka koya a taron. Kuma zai ambata abubuwan da za a tattauna a mako na gaba. Zai iya ambata sunayen ɗaliban da za su yi aiki mako na gaba idan da lokaci. Mai gudanar da taron zai iya yin amfani da wannan lokaci na kammalawa don ya yi sanarwa ko kuma ya karanta wasiƙu, sai dai ko an ba da wani umurni dabam. Kada a sanar da tsarin yin waꞌazi na mako da kuma tsarin tsabtace majamiꞌar mulki, maimakon haka, za a saka su a allon sanarwa. Idan lokaci ba zai isa har a yi sanarwa ko karanta wasiƙu ba, mai gudanar da taron zai iya gaya wa ꞌyanꞌuwan da ke gudanar da sashen Rayuwar Kirista su taƙaita sashensu. (Ka duba  sakin layi na 16 da  19.) Za a kammala taron da waƙa da kuma adduꞌa..

  BA DA SHAWARA DA YABAWA

18. Bayan kowane aikin da ɗalibi ya yi, mai gudanar da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu ya yi amfani da aƙalla minti ɗaya don ya yaba musu kuma ya ba da shawara a kan batun da aka ce ya yi aiki a kai. Saꞌad da mai gudanar da taron ya gabatar da ɗalibi, kada ya ambata darasin da ake bukatar ɗalibin ya yi aiki a kai. Amma bayan ɗalibin ya gama aikinsa, mai gudanar da taron ya yaba masa kuma zai iya ambata darasin da aka ba ɗalibin ya yi aiki a kai. Ƙari ga haka, zai ambata abin da ya sa ɗalibin ya yi aikinsa da kyau ko kuma dalilin da ya sa da yadda ɗalibin yake bukatar ya daɗa yin ƙoƙari a wannan fannin. Mai gudanar da taron zai iya yin kalami a kan wasu ƙarin abubuwa da ya lura da su a aikin da ɗalibin ya yi idan hakan zai amfani ɗalibin ko kuma masu sauraro. Za a iya yin amfani da ƙasidar nan Ƙaunar Mutane ko Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa ko kuma Benefit From Theocratic Ministry School Education don a ba ɗalibin ƙarin shawara bayan taron ko wani lokaci dabam don ya yi gyara a kan darasin da aka ce ya yi aiki a kai ko kuma wani darasi dabam. Don ƙarin bayani a kan aikin mai gudanar da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu da kuma aikin mai ba da shawara na biyu, ka duba  sakin layi na 19 da  24 da kuma  25.

     LOKACI

19Kada a ci lokaci, kada kuma kalamin da mai gudanar da taron zai yi ya wuce lokaci. Ko da yake Littafin Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu yana ɗauke da lokacin da za a gabatar da kowane sashe, idan aka tattauna muhimman batun da kyau, bai kamata a kawo wasu bayanai don mutumin yana gani yana da lokaci. Idan ꞌyanꞌuwan da suke gudanar da sauran sashen sun ci lokaci, mai gudanar da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu ko kuma mai ba da shawara na biyu ya yi wa kowannensu gyara tsakanin su biyu kawai. (Ka duba  sakin layi na 24 da  25.) Kada taron, har da waƙa da adduꞌa su wuce awa 1 da minti 45.

 ZIYARAR MAI KULA DA DAꞌIRA

20. A lokacin da mai kula da daꞌira ya ziyarci ikilisiyarku, ku bi tsarin da ke Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu, ba tare da yin waɗannan abubuwa ba: Mai kula da daꞌira zai yi amfani da lokacin Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya da ke sashen Rayuwar Kirista don ya ba da jawabinsa na minti 30. Kafin jawabin mai kula da daꞌira, mai gudanar da Taron Rayuwar ta Kirista da Hidimarmu ya yi bitar taron kuma ya faɗi abin da za a tattauna a mako na gaba, kuma ya yi sanarwa ko ya karanta wasiƙu idan akwai. Bayan haka, sai ya gabatar da mai kula da daꞌira. Bayan jawabin, mai kula da daꞌirar zai kammala taron da waƙar da ya zaɓa. Zai iya kiran wani ɗanꞌuwa ya yi adduꞌar kammalawa. Ba za a gudanar da aji na biyu ba a makon da mai kula da daꞌira yake ziyarar ikilisiyar. Idan akwai wani rukuni, ꞌyan rukunin za su iya yin taronsu, amma za su halarci taron ikilisiyar bayan sun gama nasu taron don su saurari jawabin mai kula da daꞌirar.

 MAKON TARON DAꞌIRA KO TARON YANKI

21. Ba za a yi taron a makon da ake taron daꞌira ko na yanki ba. A tunasar da kowa a ikilisiya ya yi nazarin abin da za a gabatar a taron a gidajensu.

 MAKON TARON TUNAWA DA MUTUWAR YESU

22. Idan ranar Taron Tunawa da Mutuwar Yesu ta faɗi a ranakun Litinin zuwa Jummaꞌa, ba za a yi Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu a makon ba.

 MAI KULA DA TARON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU

23. Dattijon da rukunin dattawa suka zaɓa ne zai zama mai kula da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Shi ne zai tabbatar cewa an gudanar da taron yadda aka ce a yi. Shi da mai ba da shawara na biyu su riƙa tattaunawa a kai a kai. Da zarar an fitar da sabon Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu, mai kula da Taron Rayuwar Kirista da Hidimarmu ya rarraba aiki na wata biyu ga ɗalibai. Hakan ya ƙunshi sashen da ba na ɗalibai ba, da aikin da dattawan masu gudanar da taron da rukunin dattawa suka zaɓa za su yi da kuma na ɗalibai. (Ka duba  sakin layi na 3-16 da  24.) Saꞌad da yake rubuta aikin da kowane ɗalibi zai yi, ya yi laꞌakari da shekarunsu da ƙwarewarsu ko kuma aikin zai dace da su. Zai yi hakan saꞌad da yake ba da sauran ayyuka a taron, A ba kowane ɗalibi aikin da zai yi aƙalla makonni uku kafin ranar da zai yi aikin, kuma a yi amfani da fom ɗin nan Aiki a Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (S-89) Mai kula da taron zai tabbata cewa an manna tsarin ayyukan a allon sanarwa. Rukunin dattawa suna iya su zaɓa wani dattijo ko bawa mai hidima ya taimaka masa, amma dattawa ne kaɗai za su shirya sashen da ba na ɗalibi ba ne.

    MAI GUDANAR DA TARON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU

24. Dattawa dabam-dabam ne za su riƙa gudanar da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. (Idan babu dattawa da yawa, za a iya ba ƙwararrun bayi masu hidima.) Shi ne yake da hakkin shirya gabatarwar taron da na kammalawa. Shi ne zai gabatar a kowane sashe kuma zai iya ba da wasu jawabai a taron idan babu dattawa da yawa a ikilisiyar, musamman sashen da ake bukata a nuna wani bidiyo ba tare da ƙarin bayani ba. Ya taƙaita kalaman da zai yi bayan kowane sashe. Rukunin dattawa ne za su tsai da shawara a kan dattawan da suka cancanci yin wannan aikin. Waɗannan dattawan ne za su riƙa gabatar da taron a kai a kai. Za a iya yin amfani da mai kula da Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu a matsayin mai gudanar da taro fiye da wasu dattawa da suka ƙware a yin wannan aikin dangane ga yanayin ikilisiyar. Idan wani dattijo ya cancanci gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, ba mamaki zai cancanci gudanar da wannan taron. Don Allah ku lura cewa ana bukatar dattijon da zai gudanar da taro a makon ya yaba ma ɗaliban da suka yi aiki a taron kuma ya ba su shawarar da ta dace idan da bukata. Mai gudanar da taron ya tabbata cewa ba a ci lokaci ba. (Ka duba  sakin layi na 17 da  19.) Idan mai gudanar da taron yana so kuma akwai isashen fili a dakalin magana, za a iya ajiye masa wani makarufo a gefe don ya riƙa kiran ꞌyanꞌuwan da za su yi aiki yayin da suke zuwa wajen makarufo da ke inda masu jawabi suke tsayawa. Hakazalika, mai gudanar da taron zai iya zama a kujera a kan dakalin saꞌad da ɗalibi yake karatun Littafi Mai Tsarki da kuma saꞌad da ɗalibai suke aiki a sashen Ka Yi Waꞌazi da Ƙwazo. Hakan zai iya rage cin lokaci.

    MAI BA DA SHAWARA NA BIYU

25. Idan zai yiwu, zai fi kyau a ba dattijon da ya ƙware a yin jawabi wannan aikin. Hakkin mai ba da shawara na biyu ne ya yi ma dattawa ko bayi masu hidima gyara a kan duk wani jawabin da suka yi, idan da bukata. Ya yi hakan tsakanin su biyu kawai. Waɗannan jawaban sun haɗa da jawabai a Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu da jawabai ga jamaꞌa da karatu ko gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro da kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. (Ka duba  sakin layi na 19.) Idan akwai ƙwararrun dattawa da yawa da suka iya koyarwa a ikilisiyarku, zai dace ku riƙa canja dattijon da ke ba da shawara na biyu kowace shekara. Mai ba da shawara na biyu ba ya bukatar ya riƙa yi wa dattawa da bayi masu hidima gyara bayan kowane jawabi.

 WASU AZUZUWA

26. Ikilisiyoyi za su iya yin amfani da wasu azuzuwa idan suna da ɗalibai da yawa. A tabbatar cewa akwai ɗanꞌuwan da zai riƙa ba da shawara a kowane aji. Zai fi dacewa dattijo ya yi wannan aikin. Amma idan ba zai yiwu ba, bawa mai hidima da ya ƙware zai iya yin wannan aikin. Rukunin dattawa su zaɓi ɗanꞌuwan da ya cancanci yin wannan aikin, kuma su duba su ga idan da bukatar su riƙa canja ꞌyanꞌuwa da suke aikin. Mai ba da shawarar ya bi umurnin da ke  sakin layi na 18. Idan akwai wani aji, a ce wa ɗaliban su je ajin da za su yi aikinsu bayan an kammala sashen Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah. Su dawo cikin majamiꞌar saꞌad da ɗalibi na ƙarshe ya kammala aikinsa.

 BIDIYOYI

27. Za a kalli bidiyoyin da aka zaɓa a wannan taron. Za a sami bidiyoyin a manhajar JW Library® kuma za a iya sauke bidiyoyin da waya ko kuma da kwamfuta.

© 2023 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania

S-38-HA 11/23