Koma ka ga abin da ke ciki

21 GA MARIS, 2017
RASHA

Shaidun Jehobah Sun Dauki Mataki don Barazanar Yi Musu Takunkumi a Rasha

Shaidun Jehobah Sun Dauki Mataki don Barazanar Yi Musu Takunkumi a Rasha

NEW YORK​—Yayin da suke fuskantar barazanar da ya kusa kai ga hana yin ibadarsu a Rasha, Shaidun Jehobah a faɗin duniya suka fara wata kamfen na roko ta wajen rubuta wasiku ma Kremlin da ma’aikatan babban kotu. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah na gayyatar Shaidu sama da 8,000,000 a duniya su yi hakan.

A ranar 15 ga Maris, 2017, Jam’iyar Harkokin Shari’a ta Rasha ta yi wa Cibiyar Hukumar Shaidun Jehobah wata bakar sharri a gaban babban kotu na Rasha da cewa su masu tsattsauran ra’ayi ne. Da’awar nan na da niyar kai wa har ga hana ayyukan wannan Cibiyar Hukumar. Da zarar Babban Kotun ya amince da wannan da’awar, za a rufe hedkwatar Shaidun Jehobah da ke kusa da St. Petersburg. Daga baya, waɗansu kungiyoyin adinai 400 da ke kasar da aka yi rajistarsu za a ƙwace su, dokar zata hana ayyukan ikilisiya fiya da 2,300 and kasar Rasha. Gwamnati za ta iya kwace dukiyar da ke kasa na Cibiyar Hukumar, har ma tare da wuraren ibadar Shaidu da ke kasar ga baki daya. Haka ma, duk Mashaidin Jehobah da aka iske shi na harkar ibadarsa zai zo gaban kotu. Babban Kotun zai yanke shari’ar a ranar 5 ga Afrilu.

Kakakin Babbar Hedkwatar Shaidu, shi David A. Semonian ya ce, “Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah na niyyar kara mai da wa wannan batun hankali sosai. Wannan ba ya bisa ka’ida yayin da ake hukumta masu zaman lafiya, ‘yan kasa masu kiyaye doka a kan laifin tsattsauran ra’ayi. Irin wannan hukunci a cikin rashin kyakkyawar dalili ce ko kuma cikin rashin gaskiya.”

Wannan kamfen na Shaidu cikin duniya baki daya ba yau aka fara ba. Kusan shekaru 20 da suka shige, domin su kare kan ‘yan’uwa a Rasha, Shaidu sun yi rubutu game da sharrin da membobin gwamnati da suke mulki a wannan lokaci suka yi. Bugu da kari, Shaidu sun dauki matakin kamfen na rubuta wasiku da aka saba yi don su sa ma’aikatan gwamnati su hana irin tsanantawar da ake yi wa Shaidu a wasu kasashe, da ya kunshi Urdun, Koriya da Malawi.

Mr. Semonian ya dada nanatawa da cewa” “Karanta Littafi Mai Tsarki, rera wakoki, da yin addu’a a tarayyar masu ibada ba laifi ba ne,” “Muna fatan cewa kamfen namun nan ta rubuta wasiku a fadin duniya baki daya zai sa ma’aikatan gwamnatin Rasha su hana wannan halin ketare dokar zaluntar ‘ya’uwanmu na cikin ibada.”

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Ofishin labarai, +1-845-524-3000

Rasha: Yaroslav Sivulskiy, +7-812-702-2691