Koma ka ga abin da ke ciki

Danꞌuwa Boris Simonenko tare da matarsa Ida

1 GA FABRAIRU, 2023
RASHA

“Ba Yanayina Ne Kawai Nake Bukata In Canja Ba”

“Ba Yanayina Ne Kawai Nake Bukata In Canja Ba”

Nan ba dadewa ba, kotun yankin Vladimir na Birnin Kovrovskiy zai sanar da hukuncin da aka yi wa wani Danꞌuwa mai suna Boris Simonenko. Alkalin bai fadi irin hukunci da za a yanke wa Danꞌuwa Simonenko ba.

Tarihinsa

Muna da tabbaci cewa Boris da iyalinsa za su ci gaba da samun karfi da farin ciki yayin da suke kusa da Jehobah.​—⁠1 Tarihi 16:⁠27.

Lokaci

  1. 8 ga Fabrairu, 2021

    Hukuma ta dauka muryar Danꞌuwa Boris yayin da yake waya domin su yi amfani da shi wajen yin bincike

  2. 17 ga Fabrairu, 2021

    An yi bincike a gidansa. An yi masa tambayoyi kuma aka kulle shi na dan lokaci

  3. 18 ga Fabrairu, 2021

    An soma tuhumarsa da aikata laifi. Laifinsa shi ne yana gudanar da taron Shaidun Jehobah ta intane. An tsare shi kafin a yanke masa hukunci

  4. 13 ga Yuli, 2021

    An sake shi kuma aka tsare shi a cikin gidansa

  5. 17 ga Fabrairu, 2022

    An sake shi amma an hana shi barin kasar

  6. 15 ga Satumba, 2022

    An soma yi masa shariꞌa a kotu