Koma ka ga abin da ke ciki

Wane ne Yohanna Mai Baftisma?

Wane ne Yohanna Mai Baftisma?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Yohanna Mai Baftisma annabin Allah ne. (Luka 1:76) An haife shi a shekara ta 2 kafin haihuwar Yesu kuma ya mutu a shekara ta 32 bayan haihuwar Yesu. Allah ya ba shi aikin shirya wa Almasihu ko kuma Kristi hanya. Yohanna ya yi hakan ta wajen yi wa Yahudawa waꞌazi don su komo ga Allah.​—Markus 1:​1-4; Luka 1:​13, 16, 17.

 Waꞌazin da Yohanna yake yi zai taimaka wa masu zuciyar kirki su san cewa Yesu Banazare shi ne Almasihu. (Matiyu 11:10) Yohanna ya karfafa masu sauraran shi su tuba daga zunubansu kuma a yi musu baftisma don su nuna cewa sun tuba. (Luka 3:​3-6) Domin ya yi wa mutane da yawa baftisma, an soma kiran shi Yohanna Mai Baftisma. Baftisma mafi muhimmanci da Yohanna ya yi shi ne wanda ya yi wa Yesu. a​—Markus 1:9.

Ga tambayoyin da za mu tattauna a talifin nan

 Me ya sa Yohanna Mai Baftisma ya yi dabam da sauran mutane?

 An annabta aikin da zai yi: Yohanna ya cika annabci cewa zai zama mai idar da sakon Allah ta wajen yin waꞌazi. (Malakai 3:1; Matiyu 3:​1-3) Shi ne ya zama wanda ya “shirya wa Ubangiji mutanensa,” wato shi ne ya taimaka wa ꞌyanꞌuwansa Yahudawa su amince da wanda Jehobah ya aiko a matsayin wakilinsa, Yesu Kristi.​—Luka 1:17.

 Tarihi: Yesu ya ce “ba a taɓa haifuwar wani a duniyar nan wanda ya kai Yohanna Mai Baftisma girma ba. Amma duk da haka, wanda ya fi kankanta a mulkin sama ya fi shi.” (Matiyu 11:11) Da yake Yohanna annabi ne da kuma mai idar da sako da aka yi annabcinsa, babu bawan Allah da ya yi rayuwa kafin Yohanna da ya fi shi. Abin da Yesu ya fada ya nuna cewa Yohanna ba zai je sama ba. b Wannan annabi mai aminci ya mutu kafin Kristi ya bude hanyar yin rayuwa a sama. (Ibraniyawa 10:​19, 20) Amma Yohanna zai yi rayuwa a duniya saꞌad da Mulkin Allah ya soma sarauta, kuma yana da begen yin rayuwa har abada a Aljanna.​—Zabura 37:29; Luka 23:43.

 Su waye ne iyayen Yohanna Mai Baftisma?

 Iyayen Yohanna su ne Zakariya da Alisabatu. Zakariya firist ne na Yahudawa. Ta muꞌujiza aka haifi Yohanna domin mahaifiyar Yohanna ba ta iya haihuwa ba. Ban da haka ma, ita da Zakariya “sun tsufa.”​—Luka 1:​5-7, 13.

 Wane ne ya kashe Yohanna Mai Baftisma?

 Sarki Hirudus Antibas ne ya sa aka fille kan Yohanna kuma Hirudiya matarsa ce ta zuga shi ya yi hakan. Ta tsani Yohanna domin ya gaya wa Hirudus wanda Bayahude ne cewa aurensu ba bisa dokar Yahudawa ba ne.​—Matiyu 14:​1-12; Markus 6:​16-19.

 Yohanna Mai Baftisma da Yesu sun yi gasa da juna?

 Ba inda aka nuna a Littafi Mai Tsarki cewa Yohanna da Yesu sun yi gasa da juna. (Yohanna 3:​25-30) Yohanna ya bayyana cewa hakkinsa ne ya shirya zuwan Almasihu ba yin gasa da shi ba. Yohanna ya ce: “Na zo ina yin baftisma da ruwa . . . domin a bayyana shi ga mutanen Israꞌila.” Sai ya dada da cewa: “Wannan mutum Dan Allah ne.” (Yohanna 1:​26-34) Saboda haka, Yohanna ya yi farin cikin jin game da yadda Yesu ya yi nasara a hidimarsa.

a Yesu “bai taba yin laifi ba ko kadan.” (1 Bitrus 2:​21, 22) Ya yi baftisma ba don yana bukatar ya tuba ba, amma domin yana ba da kansa don ya yi nufin Allah. Hakan ya kunshi ba da ransa a madadinmu.​—Ibraniyawa 10:​7-10.

b Ka duba talifin nan “Su Waye Za Su Je Sama?