Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Idin Ketarewa?

Mene ne Idin Ketarewa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Idin Ketarewa biki ne da Yahudawa suke yi domin ’yancin da Allah ya ba su daga bauta a kasar Masar a shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu. Allah ya umurci Isra’ilawa cewa su rika tunawa da wannan rana mai muhimmanci kowace shekara kuma su rika yin hakan a ranar 14 ga watan Abib na Yahudawa, wanda daga baya aka fi sani da sa Nisan.​​—Fitowa 12:42; Levitikus 23:5.

Me ya sa ake kiran sa Idin Ketarewa?

 Furucin nan “Idin Ketarewa” yana nufin lokacin da Allah ya kāre Isra’ilawa daga bala’in da ya kashe dukan ’ya’yan fari na Masarawa. (Fitowa 12:27; 13:15) Kafin wannan annobar ta auku, Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su yanka rago ko akuya, sai su yafa jinin a jikin kofar gidansu. (Fitowa 12:​21, 22) Sa’ad da Allah ya “ketare” gidansu kuma ya ga alamar, sai ya kyale ’ya’yan farinsu da rai.​—Fitowa 12:​7, 13.

Yaya ake yin Idin Ketarewa a zamanin dā?

 Allah ya gaya wa Isra’ilawa dalla-dalla yadda za su yi Idin. a Ga wasu abubuwan da ake yi a lokacin Idin Ketarewa.

  •   Hadaya: Iyalai sukan zabi rago (ko akuya) da ya kai shekara daya a ranar goma ga watan Abib (Nisan), sa’an nan su yanka shi a ranar 14th ga watan. A rana ta farko da Yahudawa suka fara yin Idin Ketarewa, sun yafa jinin ragon a jikin kofar gidansu kuma suka gasa sauran naman suka ci.​—Fitowa 12:​3-9.

  •   Abinci: Bayan naman rago (ko akuya) da suke yankawa, Isra’ilawan suna cin burodi mara yisti da kuma ganye mai daci a ranar Idin.​—Fitowa 12:8.

  •   Idi: Isra’ilawan sukan yi Idin Gurasa Mara Yisti har na kwana bakwai bayan Idin Ketarewa, kuma a wannan lokacin ba sa cin gurasa mai yisti.​—Fitowa 12:​17-20; 2 Labarbaru 30:21.

  •   Koyarwa: Iyaye sukan yi amfani da lokacin Idin Ketarewa don su koya wa yaransu game da Jehobah.​—Fitowa 12:​25-27.

  •   Tafiye-Tafiye: Daga baya, Isra’ilawa sukan yi tafiya zuwa Urushalima don su yi Idin Ketarewa.​—Kubawar Shari’a 16:​5-7; Luka 2:41.

  •   Wasu abubuwan da suke yi: A zamanin Yesu, akan yi wake-wake kuma akan sha ruwan inabi a lokacin Idin.​—Matta 26:​19, 30; Luka 22:​15-18.

Karya game da Idin Ketarewa

 Karya: Isra’ilawa suna cin abincin Idin Ketarewa a ranar 15 ga Nisan.

 Gaskiya: Allah ya gaya wa Isra’ilawa su yanka rago bayan faduwar rana a ranar 14 ga Nisan kuma su ci naman a daren. (Fitowa 12:​6, 8) Isra’ilawa sukan fara kirga kwanakinsu bayan faduwar rana. (Levitikus 23:32) Saboda haka, Isra’ilawan sun ci abincin Idin a farawar 14 ga Nisan.

 Karya: Ya kamata Kiristoci su yi Idin Ketarewa.

 Gaskiya: Bayan Yesu ya yi Idin Ketarewa a ranar 14 ga Nisan shekara ta 33  bayan haihuwarsa, ya kafa wata sabuwar Idi: Jibin Maraice na Ubangiji. (Luka 22:​19, 20; 1 Korintiyawa 11:20) Wannan ya maye gurbin Idin Ketarewa, domin yana tuna mana da hadayar da Kristi ‘Dan Rago na Idin Ketarewa’ ya yi. (1 Korintiyawa 5:7) Hadayar da Yesu ya yi ta fi na Idin Ketarewa, domin ta fanshe dukan mutane daga zunubi da kuma mutuwa.​—Matta 20:28; Ibraniyawa 9:15.

a Daga baya an yi wasu canje-canje da ya kamata. Alal misali, Isra’ilawan sun yi bikin cikin gaggawa domin suna kokarin barin kasar Masar. (Fitowa 12:11) Amma da suka isa Kasar Alkawari, ba sa bukatar su yi Idin cikin gaggawa kuma.