Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Luwadi?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Luwadi?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Allah ya halicci mutane su yi jima’i cikin gamin aure na mata da miji ne kawai. (Farawa 1:​27, 28; Levitikus 18:22; Misalai 5:​18, 19) Littafi Mai Tsarki ya haramta jima’i da ba tsakanin mata da miji ba, luwadi ko kuma tsakanin wani da wata. (1 Korintiyawa 6:​18) Wannan ya hada da yin jima’in lalaci, jima’i ta shafa al’aurar wani da kuma ta tsotsar al’aurar wani ko kuma ta duwawu.

 Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya haramta luwadi, bai amince da a ki wadanda suke halin ba. Maimako, an ce Kiristoci su “girmama dukan mutane.”​—1 Bitrus 2:​17, Good News Translation.

Ana iya haifan mutum dan luwadi

? Littafi Mai Tsarki bai ce kome ba game da a haife mutum da sha’awar yin luwadi, amma ya ce dukanmu muna da halin taka dokar Allah. (Romawa 7:​21-​25) Littafi Mai Tsarki ya haramta aikata luwadi maimakon yana zance game da sha’awar yin haka.

Yadda za ka faranta wa Allah duk da sha’awarka na ka aikata luwadi.

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sai ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’awacen duniya.” (Kolosiyawa 3:5, Contemporary English Version) Kana bukatar ka lura da tunaninka don a iya kashe mugun sha’awa da ke kai ga yin miyagun ayyuka. Idan kullum kana tunani mai kyau, zai yi maka sauki ga kawar da mugun sha’awa daga zuciyarka. (Filibbiyawa 4:8; Yakub 1:​14, 15) Ko da yake da farko zai yi wuya, amma a hankali zai kasance da sauki. Allah ya yi alkawarin zai taimake ka ‘ka yi tunani a kan wadannan abubuwa.’​—Afisawa 4:​22-​24.

 Haka ma miliyoyin wadanda suke sha’awar jima’i suke fama don su bi mizanan Littafi Mai Tsarki. Alal misali, wasu marasa aure da ba su kai aure ba ko kuma wadanda abokan aurensu ba su iya kosar da su game da jima’i ba, suna nan suna fama da rike kansu duk da jarabar da suke fuskanta. Sun iya kasance da farin ciki, kuma haka ma wadanda suke sha’awar luwadi za su iya hakan idan da gaske suna don su faranta wa Allah rai.​—Kubawar Shari’a 30:19.