Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Kwalliya?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Kwalliya?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai tattauna wannan batun dalla-dalla ba, amma bai haramta yin ado da kuma kwalliya da gwalla-gwallai ba. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki bai mai da hankali ga yin ado kawai ba, a maimakon haka, ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne mutum ya zama “mai-ladabi mai-lafiya.”​—1 Bitrus 3:​3, 4.

Ba a haramta yin ado ba

  •   Mata masu aminci da suka yi ado a dā. Rifkatu wadda ta auri dan Ibrahim mai suna Ishaku, ta yi kwalliya da azurfa da zinariya da kuma wasu kayan ado masu tsada da baban maigidanta ya ba ta. (Farawa 24:​22, 30, 53) Haka ma Esther, ita ma an ba ta “kayan gyaran jiki” don ta gyara jikinta da shi da yake za ta zama sarauniyar Daular Fasiya. (Esther 2:​7, 9, 12) Watakila wadannan kayan gyaran jikin sun kunshi “kayan kwalliya kala-kala.”​—New International Version; Easy-to-Read Version.

  •   Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kayan ado wajen kwatanta wasu abubuwa masu kyau. Alal misali, ana kwatanta mutum mai ba da shawara mai kyau da “zoben kunne na zinariya . . . ga kunne mai-jin gari.” (Misalai 25:12) Hakazalika, Allah da kansa ya kwatanta sha’anin da ya yi da Isra’ilawa da macen da ta yi ado da tagulla da ‘yan kunne da kuma sarka. Wannan adon ya sa al’ummar Isra’ila ta zama “kyakkyawa kwarai da gaske.”​—Ezekiyel 16:​11-13.

Karya game da yin ado da kuma gwala-gwalai

 Karya: A littafin 1 Bitrus 3:​3, Littafi Mai Tsarki ya haramta “kitson gashi, da sa ado na zinariya, ko yafa tufafi masu ƙawa.”​—1 Bitrus 3:3.

 Gaskiya: A wannan ayar, Littafi Mai Tsarki yana magana ne game da muhimmancin zama mai ibada ba mai ado kawai ba. (1 Bitrus 3:​3-6) An yi irin wannan kwatancin a wani wuri ma a Littafi Mai Tsarki.​—1 Sama’ila 16:7; Misalai 11:22; 31:30; 1 Timotawus 2:​9, 10

 Karya: Da yake Sarauniya Jezebel ce Littafi Mai Tsarki ya ce ta yi gazal, hakan ya nuna cewa yin kwalliya zunubi ne.​—2 Sarakuna 9:30.

 Gaskiya: Jezebel ‘yar sihiri ce kuma ta yi kisan kai da wasu abubuwa masu muni, shi ya sa aka shar’anta ta ba domin kwalliyar da ta yi ba.​—2 Sarakuna 9:​7, 22, 36, 37.