Koma ka ga abin da ke ciki

Ta Yaya Za Mu Bi Halin “Basamariye Mai Kirki”?

Ta Yaya Za Mu Bi Halin “Basamariye Mai Kirki”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Ana yawan amfani da wannan furucin “Basamariye Mai Kirki” (Good Samaritan) don a kwatanta mutumin da ya taimaka ma wani da yake da bukata. An samo wannan furucin daga wani labari ne da Yesu ya bayar game da wani makwabci mai kirki. Yesu ya ba da wannan labarin don ya nuna cewa makwabcin kirki yana taimaka wa mutane ko da daga ina suka fito.

A wannan talifin, za mu tattauna:

 Me Yesu ya fada a labarin “Basamariye Mai Kirki”?

Ga labarin da Yesu ya bayar a takaice: Wani Bayahude ya fito daga Yariko za shi Urushalima. Ya gamu da mafasa, sun kwace kudinsa suka masa dukan tsiya kuma suka bar shi a bakin mutuwa.

Wani firist Bayahude ya zo wucewa ya gan shi amma bai taimaka masa ba. Bayan haka, wani malamin addini, Bayahude, shi ma ya zo ya wuce bai taimaka masa ba. Ko da yake sun fito daga wuri daya, babu wani daga cikinsu da ya dakata don ya taimaka wa mutumin.

Daga baya, sai ga wani mutum daga wata kasa dabam ya zo wucewa. Mutumin Basamariye ne. (Luka 10:33; 17:​16-18) Da ya ga mutumin, sai tausayi ya kama shi, ya daure raunukansa. Bayan haka, sai ya dauke shi ya kai shi wurin jinya kuma ya kula da shi. Washe gari, ya biya kudin jinyar kuma ya gaya wa mai jinyar cewa ya ci gaba da jinyar, zai biya.​—Luka 10:​30-35.

 Me ya sa Yesu ya ba da wannan labarin?

Yesu ya ba da wannan labarin ne don ya daidaita raꞌayin wani mutum da yake tunanin cewa makwabtansa su ne mutanen kabilarsa da addininsa. Yesu ya so ya fahimtar da mutumin cewa ba ꞌyanꞌuwansa Yahudawa ne kadai ya kamata ya ce ‘makwabtansa’ ba. (Luka 10:​36, 37) Allah ya sa an rubuta wannan labarin a Littafi Mai Tsarki don duk wanda yake so ya faranta masa rai, ya dauki darasi.​—2 Timoti 3:​16, 17.

 Wane darasi za mu koya daga wannan labarin?

Labarin nan ya nuna mana cewa a kan gane makwabcin kirki ta wurin ayyukansa da halinsa. Makwabcin kirki yakan taimaka ma wanda yake cikin matsala ko da daga ina ya fito. Ban da haka ma, yakan yi wa mutane alheri kamar yadda yake so a yi masa.​—Matiyu 7:12.

 Su waye ne Samariyawan?

Samariyawan suna zama ne a arewacin Yahudiya. Kuma a cikinsu akwai zuriyar Yahudawa da suka auri wadanda ba Yahudawa ba.

A zamanin Yesu, Samariyawan sun riga sun ware kansu suna da nasu addinin. Sun amince da littattafai biyar na farko na Nassosin Helenanci, amma sun ki sauran.

Yahudawa da yawa a zamanin Yesu sun ki jinin Samariyawa, ba sa son ma wani abu ya hada su. (Yohanna 4:9) Wasu ma sun mai da kalmar nan “Samariyawa” ta zama zagi.​—Yohanna 8:48.

 Labarin “Basamariye Mai Kirki,” labari ne da ya faru da gaske?

Nassi bai nuna cewa labarin nan na Basamariye, abu ne da ya faru da gaske ba. Amma Yesu sau da yawa yakan yi amfani da halin mutane da wuraren da kowa ya sani a koyarwarsa domin mutane su fahimci abin da yake fada da kyau.

Tarihi ya nuna cewa abubuwa da yawa da ya fada a labarin, haka ne. Alal misali:

  • Akwai hanyar da ta fito daga Urushalima zuwa Yariko mai nisan fiye da kilomita 20 kuma gangara ne sosai. Abin da Yesu ya fada daidai ne, domin idan mutum ya fito daga Urushalima za shi Yariko, ‘gangarawa’ zai yi.​—Luka 10:30.

  • Firistoci da shugabannin addinin Yahudawa da suke zama a Yariko kullum suna bin wannan hanyar zuwa Urushalima.

  • ꞌYan fashi sun saba boyewa a wannan hanyar domin ba ya cikin gari. Idan mutum ya zo wucewa sai su yi masa sata, musamman idan shi kadai ne.