Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Ya Haramta Auren Wata Kabila Ne?

Littafi Mai Tsarki Ya Haramta Auren Wata Kabila Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Allah bai hana mace da namiji daga kabila dabam-dabam su yi aure ba, domin kowace kabila daya ce a wajen shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowace al’umma . . . , abin karɓa ne gare shi.”—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.

 Ka bincika wadansu ka’idodin Littafi Mai Tsarki da suka tattauna yadda dukan kabilu daya ne a gaban Allah da kuma batun aure.

Duka kabilu daga tushe daya ne

 Dukan mutane sun fito daga Adamu da matarsa Hawwa’u ne. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce da “ita uwar masu-rai duka ce.” (Farawa 3:20) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Daga tushe daya kuwa [Allah] ya yi dukan al’umman mutane.” (Ayyukan Manzanni 17:26) Dukan mutane daga iyali daya ne ko daga wane kabila ne. Amma idan akwai wariya a inda kake da zama fa?

Mutane masu hikima suna yin ‘shawara’ da juna

 Allah ya amince da aure tsakanin kabilu dabam-dabam, amma ba kowa ba ne ya yarda da ra’ayinsa. (Ishaya 55:8, 9) Idan kana shirin auran wani da kabilarku ba daya ba, sai ku tattauna wadannan batun da ke kasa:

  •   Ta yaya za ku bi da matsi da za ku fuskanta a yankinku ko daga dangi?

  •   Ta yaya za ku taimaki yaranku su bi da matsalar nuna wariya?

 Yin ‘shawara’ da juna zai sa ku ci nasara a zaman aurenku.—Misalai 13:10; 21:5.