Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI | RENON YARA

Me Zan Yi In Dana Ya Gaji da Zama Ba Abin Yi?

Me Zan Yi In Dana Ya Gaji da Zama Ba Abin Yi?

 Idan yaronka yana zaune a gida kuma bai da abin yi, sai ya ce maka, “Na gaji da zama!” Me za ka yi? Kila za ka so ka kunna masa talabijin kuma ka ce ya je ya yi kallo ko ka ce ya yi wasannin bidiyo, amma kafin ka yi hakan, ga wasu abubuwa da ya kamata ka sani.

Abubuwan da wasu iyaye suka gano game da yaran da suke jin haka

  •   Irin wasa da kuma yawan lokacin da yaron yake dauka yana yinsa zai iya kara bata lamarin. Wani mahaifi mai suna Robert ya ce: “Wasu yara sun gwammace su rika kallon talabijin ko su yi ta wasannin bidiyo domin suna ganin ba za su ji dadin yin wasu abubuwa ba.”

     Matarsa mai suna Barbara ma ta yarda da hakan. Ta ce: “Rayuwa tana bukatar kwazo da kuma yin tunani, kuma ba kowane lokaci ba ne za ka ga sakamakon abin da kake yi nan da nan. Idan yaranka sun saba daukan lokaci sosai suna kallon talabijin da yin wasan bidiyo, zai yi musu wuya su ji dadin yin wani abu dabam.”

  •   Yawan amfani da dandalin sada zumunta zai iya sa yaro bakin ciki. Idan yaro yana yawan kallon hotuna da bidiyoyi da abokansa suke sakawa game da kansu, hakan zai iya sa yaron ya ga kamar ba ya jin dadin rayuwa. Wata yarinya mai suna Beth ta ce, “Yana da sauki mutum ya dauka cewa, ‘kowa yana walawa ban da ni.’”

     Kari ga haka, idan mutum ya yi awoyi da dama yana amfani da dandalin sada zumunta, a karshe zai iya ji kamar bai yi wani abin kirki ba kuma zai gaji da zama. Wani matashi mai suna Chris ya ce: “Za ka ga kamar kana yin abin kirki ne amma a karshe za ka ga cewa ba abin da ka cim ma.”

  •   Rasa abin yi zai iya ba ka damar yin sabon abu. Wata mahaifiya mai suna Katherine ta ce idan yaro ya gaji da zama, wannan dama ce wa yaron ya yi tunanin wani sabon abin da zai yi. Ta kuma ba da misali, ta ce: “Yaro zai iya daukan kwali ya mai da shi abin saka abubuwa da za su zama masa kayan tarihi a nan gaba, ko ya mai da kwalin ya zama masa mota ko kwalekwale ko jirgin sama. Kuma zai iya daukan bargo ya rufe kujera ko tebur da shi don ya zama masa tenti.”

     Wata mai nazarin ilimin halin dan Adam da ake kira Sherry Turkle ta ce, zama babu abin yi “dama ce na tunanin wani sabon abin da za ka iya yi.” a Don haka, rashin abin yi zai iya amfanar mutum. Wani littafi mai suna Disconnected ya ce: “Idan kana daga nauyi, hakan zai taimaka wajen gina jikinka. Hakazalika, rasa abin yi zai iya sa ka yi tunanin yin wani sabon abu.”

 Gaskiyar batun: A duk lokacin da yaranka suka gaji da zama don sun rasa abin yi, ka tuna cewa wannan dama ce na taimaka musu su kirkiro wani sabon abu.

Abin da za ka iya yi idan yaranka sun gaji da zama

  •   Idan zai yiwu, ka bar yaranka su yi wasa a waje. Barbara da muka ambata dazu ta ce: “Hasken rana da iska mai dadi zai iya sa mutum ya wartsake sosai. Da yaranmu suka soma wasa a waje, sai suka soma yin abubuwa da dama da ba su saba yi ba a dā.”

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ga kowane abu akwai lokacinsa, akwai . . . lokacin dariya, . . . da lokacin farin ciki [‘yin tsalle-tsalle,’ NW].”​—Mai-Wa’azi 3:​1, 4.

     Ka tambayi kanka: Me zan iya yi don in ba wa yarana damar yin wasa a waje? Idan ba zai yiwu ka bar yaranka su yi wasa a waje ba, wadanne wasanni da ake yi a cikin daki ne za su ba yarana damar kirkiro sabbin abubuwa?

  •   Ka karfafa yaranka su taimaka wa mutane. Wata mahaifiya mai suna Lillian ta ce “za ku iya taya abokanku da suka tsufa yankan ciyawa, ko ku yi musu shara, ko ku dafa abinci ku kai musu, ko ku je gidansa ku gaishe shi. Taimaka wa mutane yana sa mutum farin ciki sosai.”

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mai bayarwa hannu sake zai kara yalwata, mai taimaka wa wadansu, shi kansa zai sami taimako.”​—Karin Magana 11:25.

     Ka tambayi kanka: Me zan iya yi don yarana su ji dadin taimaka wa mutane?

  •   Ka kafa wa yaranka misali. Abin da kake fada game da ayyukan da kake yi a kullum zai iya shafan yaranka. Wata mahaifiya mai suna Sarah ta ce: “Idan muna magana kamar ba ma jin dadin ayyukan da muke yi, yaranmu ma za su ji hakan. Amma idan furucinmu yana nuna cewa muna jin dadin ayyukan da muke yi, hakan zai sa yaranmu ma su ji dadin abin da suke yi.”

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Zuciya mai murna kullum tana cikin jin dadi.”​—Karin Magana 15:15.

     Ka tambayi kanka: Me da me nake fada game da ayyukan da nake yi a kullum? Me nake yi idan ba na jin dadin wani abin da nake yi?

 Shawara: Ka taimaki yaranka su yi tunanin wasu sabbin abubuwa da za su iya yi. Wata mahaifiya mai suna Allison ta ce “Mun ajiye wani akwati don kowa ya rubuta shawararsa game da abin da za a iya yi kuma ya saka a ciki.”

a Daga littafin nan Reclaiming Conversation.