Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI | RENON YARA

Ku Taimaki Yaranku Su Rage Damuwa a kan Labarai Masu Ta Da Hankali

Ku Taimaki Yaranku Su Rage Damuwa a kan Labarai Masu Ta Da Hankali

 A koyaushe, ana ba da labarai masu ta da hankali, kuma za a iya kallonsu a talabijin ko a waya ko a kwamfuta. A yawancin lokuta, ana nuna munanan abubuwan da suke faruwa ne.

 Kuma yara suna ganin abin da yake faruwa.

 Ta yaya za ku taimaki yaranku su rage damuwa a kan labarai masu ta da hankali?

 Ta yaya labarai suke shafan yara?

  •   Idan aka nuna wani mummunan abu da ya faru, hakan yakan sa yara da yawa su damu sosai. Wasu yara ba sa fadin abin da ke zuciyarsu, amma idan suka kalli aukuwar wani mugun abu, yakan iya tayar musu da hankali sosai. a Musamman idan suka ga cewa iyayensu sun damu a kan abin da ya faru.

  •   Yana yi wa yara wuya su gane gaskiyar abin da suke gani a labarai. Alal misali, wasu sukan dauka cewa abin da suke gani a labarai zai faru da iyalinsu. Kuma wasu kananan yara da suke kallon wani mummunan labari da aka nuna sau da yawa, za su iya dauka cewa abin na faruwa ne a kai a kai.

  •   Yara ba za su iya gane ko an kara gishiri a labaran ba. Yara ba za su san cewa masu watsa labarai suna hakan ne don su jawo hankalin mutane da yawa ba. Abin da ke kawo musu kudi ke nan. Don haka, masu watsa labarai za su iya kara gishiri a labari don su sa mutane su ci gaba da kallon abin da ya faru.

 Ta yaya za ku taimaka wa yaranku su daina damuwa a kan labarai?

  •   Kar ku rika barin yaranku su saurari ko su kalli munanan labarai. Ba wai ana so ka hana yaranka sanin abin da ke faruwa a duniya kwata-kwata ba ne. Amma me amfanin sauraro ko kuma kallon wani mummunan labari a kai a kai?

     Wata mai suna Maria ta ce: “A wasu lokuta idan muna magana game da wani labari, mukan fede biri har wutsiya, ba tare da sanin cewa hakan yana daga wa yaranmu hankali ba.”

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Damuwa a zuciya takan hana mutum sakewa.”​—⁠Karin Magana 12:⁠25.

  •   Ka saurare su da kyau kuma ka nuna tausayi. Idan yana wa danka wuya ya yi magana a kan abin da ya faru, za ka iya ce ya zana hoton abin. Ka bayyana wa danka abin da ya faru daidai yadda zai fahimta, amma ba sai ka fada kome da kome ba.

     Wata mai suna Sarahi ta ce: “Bayan da muka tattauna kuma muka saurari ’yarmu, hakan ya taimaka mata sosai. Amma da mun gaya mata cewa, ‘Haka duniya take, gwamma kin san hakan tun da wuri,’ da mun dada tayar mata da hankali ne.”

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kowa ya kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ba.”​—⁠Yakub 1:⁠19.

  •   Ka taimaka wa yaronka ya gane yadda ake ba da labarai. Alal misali, za a iya ba da labarin garkuwa da mutane kamar lallai zai faru da kowa. Ka gaya wa yaranka matakan da ka dauka don ka kāre su. Kari ga haka, ka tuna cewa abin da ba ya cika faruwa ne ake ba da labarai a kai ba abin da ya saba faruwa ba.

     Wata mai suna Lourdes ta ce: “Ku taimaka wa yaranku su daina jin yadda suke ji. A yawancin lokuta, abin da suke tunani ne yake sa su ji tsoro, don haka idan muka taimaka musu su yi tunanin abubuwa masu kyau, hankalinsu zai kwanta.”

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mai hikima yakan mai da hankali yayin da yake magana, maganarsa kuwa takan kara samun karbuwa.”​—⁠Karin Magana 16:⁠23.

a Idan wani abu ya tayar wa kananan yara hankali, za su iya yin fitsari a kan gado ko su ji tsoron duk wani abin da zai raba su da iyayensu, kamar zuwa makaranta.