Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI

Ta Yaya Za Ka Taimaka Wa Yaronka Idan Ana Cin Zalinsa?

Ta Yaya Za Ka Taimaka Wa Yaronka Idan Ana Cin Zalinsa?

 Danka ya gaya maka cewa ana cin zalinsa a makaranta. Mene ne za ka yi? Za ka bukaci malaman makarantar su hukunta yaron da ke ci zalin danka ne? Za ka koya wa yaronka yadda zai dauki fansa ne? Kafin ka yanke shawara, ka bincika abin da cin zali yake nufi. a

 Me ya kamata in sani game da cin zali?

 Mene ne cin zali yake nufi? Cin zali yana nufin cewa a jawo wa mutum illa ko kuma bakin ciki da gangan. Saboda haka, ba kowane zagi ko kuma cin zarafi ba ne yake nufin cewa an ci zalin mutum.

 Abin da ya sa ya kamata mu san abin da cin zali yake nufi: Wasu mutane suna yin amfani da kalmar nan “cin zali” don su kimanta kowane abin bacin rai da aka yi musu. Wasu iyaye suna sa baki a kowane abin da wani ya yi wa yaransu, ko da abin bai taka-kara-ya-karya ba. Amma yin hakan bai dace ba, domin yaran ba za su koyi sasanta matsaloli ba, kuma suna bukatar koyan hakan domin za su bukace shi sa’ad da suka girma.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ka zama mai saurin fushi.”—Mai-Wa’azi 7:9.

 Gaskiyar al’amari: Hakika kana bukatar ka sa baki a wasu matsaloli da yaronka ke fuskata, amma wasu matsalolin za su ba yaronka damar koyan yadda zai rika sha’ani da mutane.—Kolosiyawa 3:13.

 Mene ne za ka yi idan yaronka ya gaya maka cewa ana cin zalinsa?

 Ta yaya zan taimaka masa?

  •   Ka saurari danka da hakuri. Ka yi kokarin sanin (1) abin da ya faru da kuma (2) dalilin da ya sa ake cin zalinsa. Kada ka dau mataki ba tare da samun cikakken bayani ba. Don ka sami cikakken bayani za ka bukaci tattaunawa da malaman yaronka ko kuma iyayen yaron da ke cin zalin danka.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Wanda ya amsa magana tun bai ji ba, wawanci ne da abin kunyarsa.”—Karin Magana 18:13.

  •   Idan ana cin zalin yaronka, ka taimaka masa ya fahimci cewa yadda ya bi da yanayin yana iya sa ya gyaru ko kuma ya dada muni. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amsawa a hankali takan kwantar da fushi, amma yin magana da zafi tana tā da fushi.” (Karin Magana 15:1) Hakika, daukan fansa yana iya sa yanayin ya dada muni, maimakon a sasanta al’amarin.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi.”—1 Bitrus 3:9.

  •   Ka bayana wa yaronka cewa idan ya ki rama abin da aka yi masa hakan ba ya nufin cewa matsoraci ne shi. A maimakon haka, wannan zai nuna cewa shi ba matsoraci ba ne domin bai bar mai cin zalin ya bi da shi yadda yake so ba. A takaice dai, yana yin nasara a kan mai cin zalin ba tare da shi kansa ya zama mai cin zali ba.

     Yana da muhimmanci yaronka ya san hakan musamman ma idan ana cin zalinsa a Intane. Idan ka mayar wa mai cin zalin martani, hakan zai ba shi damar ci gaba, kuma hakan zai sa danka ma ya kasance da irin halayen masu cin zali! Saboda haka, a wasu lokuta abin da ya dace shi ne kin mai da martani. Yin hakan yana iya sa mai cin zalin ya daina damin danka.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Inda babu itace, wuta takan mutu.”—Karin Magana 26:20.

  •   Yaronka yana iya guje wa mutane da kuma wuraren da za a iya cin zalinsa. Alal misali, idan ya san wurin da zai iya haduwa da mai cin zalin ko kuma rukuninsu, zai dace ya bi wata hanyar.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Mai hankali yakan ga hatsari, ya kauce, amma marar tunani yakan sa kai, ya sha wahala.”—Karin Magana 22:3.

Wataƙila za ka bukaci ka tattauna da malaman makarantar yaronka.

 KA GWADA BIN WANNAN SHAWARAR: Ka taimaka wa yaronka ya yi tunanin yadda zai amfana daga bin wannan shawarwarin. Alal misali:

  •  Mene ne zai faru idan bai mayar da martani sa’ad da ake cin zalinsa ba?

  •  Idan muka gaya wa mai cin zalin da gaba gadi ya daina kuma fa?

  •  Ta yaya fara’a za ta sa a daina cin zalinka?

 Cin zali ya bambanta, ko da a wace hanya ce ake yin hakan. Don haka, ka taimaka wa yaronka don ya san hanyar magance hakan. Ka tabbatar masa cewa za ka goyi bayansa.

 Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “A koyaushe aboki yana nuna ƙauna, an haifi ɗan’uwa kuwa domin taimako a kwanakin masifa.”—Karin Magana 17:17.

a Ko da yake a wannan talifin an ambata yaro, ka’idodi da aka tattauna ya shafi yara mata.