Koma ka ga abin da ke ciki

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | ILIYA

Ya Jimre Har Karshe

Ya Jimre Har Karshe

Iliya ya ji labarin: Sarki Ahab ya mutu. Bari mu yi tunanin cewa wannan annabin na zaune yana shafa gemunsa yayin da yake tunanin yadda ya ji jiki sosai a hannun wannan mugun sarkin. Iliya ya jure kwarai da gaske! Ahab da sarauniyarsa Jezebel sun yi farautarsa sosai kuma sun razanar da shi har ma ya kusan rasa ransa a sakamakon haka. Shi sarki bai hana Jezebel ba yayinda ta ba da umurni cewa a kashe annabawan Jehobah da yawa. Domin yawan hadamar da Ahab yake da shi tare da matarsa, sai suka kulla su kashe Naboth mutum mai adalci da bai yi wani laifi ba, tare da ’ya’yansa. Saboda haka, Iliya ya gaya wa Ahab shari’ar da Jehobah ya yanke, cewa shi da zuriyarsa gaba daya za su sha hukunci. Kuma maganar da Allah ya yi ta cika daidai. Ahab ya mutu kamar yadda Jehobah ya annabta.​—1 Sarakuna 18:4; 21:​1-​26; 22:37, 38; 2 Sarakuna 9:​26.

Duk da haka, Iliya ya san cewa ya kamata ya ci gaba da juriya. A lokacin Jezebel ta na nan da rai, kuma ta ci gaba da nuna mummunar iko bisa iyalinta da kuma al’ummar. Iliya zai fuskanci kalubale da yawa, kuma yana da abubuwa da yawa da zai koya wa abokin aikinsa wanda zai gaje shi, wato Elisha. To bari mu tattauna ayyuka uku na karshe da Iliya ya yi. Za mu ga yadda bangaskiyarsa ta taimaka masa ya jure, mu ma za mu iya ganin yadda za mu iya karfafa bangaskiyarmu a wannan mawuyacin lokaci da muke ciki.

An Shar’anta Ahaziah

Ahaziah, dan Ahab da Jezebel ne sarkin Isra’ila yanzu. Maimakon ya koyi darassi daga wautar da iyayensa suka yi, sai ya bi gurbinsu na mugunta. (1 Sarakuna 22:52) Ya shiga bautar Baal, yadda iyayensa suka yi. Bautar Baal tana sa mutum ya yi abubuwan da ba su dace ba, kamar yin karuwanci a haikali da kuma yin hadaya da yara. Anya akwai abin da zai sa Ahaziah ya canza tafarkinsa ya kuma juya hankalin mutanensa daga wannan rashin imani ga Jehobah?

Farat daya kawai sai bala’i ya fado wa wannan matashin sarki mai girman kai. Ya fado ta wajen tagar gidansa kuma sai ya ji rauni sosai. Duk da cewa yana bakin mutuwa, bai nemi taimakon Jehobah ba. A maimakon haka, sai ya aika sako zuwa wurin magabtansu wato birnin Ekron na Filistin don a tambayi allahnsu Baal-zebub ko yana da wani begen samun sauki. Hakan ya bata wa Jehobah rai kwarai da gaske. Ya tura wani mala’ika zuwa wurin Iliya, cewa ya hana wadannan ’yan aikan idar da sakon. Sai annabin ya tura su wurin sarkin da wata mummanar sako. Ahaziah ya yi babban zunubi don ya nuna kamar Isra’ila ba ta da wani Allah. Jehobah ya kudura cewa Ahaziah ba zai tashi daga gadon jinyarsa ba.​—2 Sarakuna 1:​2-4.

Ahaziah, mai taurin zuciya ya tambaye su cewa: Mutumin da ya yi maku wannan kalaman yaya ne kamaninsa? Sai ’yan aiken suka yi kwatancin annabin da irin rigar annabawa da ya sa mara tsada, nan da nan sai Ahaziah ya ce “Iliya ne.” (2 Sarakuna 1:​7, 8) Ya kamata mu lura da cewa Iliya ya saukaka rayuwarsa, ya mai da hankalinsa ga yin nufin Allah kuma ana ganin haka a irin kaya mara tsada da yake sakawa. Amma ba haka Ahaziah da iyayansa suke ba, domin su mutane ne masu hadama da kuma son kayan duniya. Misalin Iliya yana tuna mana da cewa mu yi rayuwa bisa gargadin da Yesu ya yi mana cewa mu saukaka rayuwarmu, mu kuma mai da hankali akan abubuwa mafi muhimmanci.​—Matta 6:​22-​24.

Ahaziah ya nace sai ya rama, hakan sai ya turo sojojinsa 50 da shugabansu su kama Iliya. Da suka tarad da Iliya, “zamne a bisa kwankolin tudu,” * sai shugaban sojojin ya umurci Iliya cikin sunan sarki “ka sauka”​—watakila da nufin su je su kashe shi. Ka ji fa! Ko da yake sun san cewa Iliya “mutumin Allah na gaskiya ne,” sojojin suna jin cewa ya yi kyau su ci zalin sa kuma su tsoratar da shi. Sun yi kuskure kwarai a hakan! Iliya ya ce wa Shugaban: “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka duk da hamsin din naka.” Sai Allah ya aikata! “Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shi da hamsin din nasa.” (2 Sarakuna 1:​9, 10) Yadda sojojin nan suka rasa rayukansu ya nuna a fili cewa Jehobah ba ya daukarsa da sauki yayinda ake wulakanta bayinsa ko kuwa a nuna masu rashin mutunci.​—1 Labarbaru 16:21, 22.

Ahaziah ya sake aikan wani shugaban soja da mutane 50. Shi shugaba na biyu ya fi na farin mugunta. Abu daya shi ne, bai koyi wani darasi daga yadda mutane 51 nan suka mutu ba, ko da yake kila tokar jikinsu na nan a baje a kan dutse. Na biyu shine, ba ma kawai ya maimaita umurnin reni da wanda ya rigaye shi ya ce wa Iliya wai “Ka sauko” ba amma har ya kara da cewa “da sauri”! Dubi sakarci! Shi da mutanensa sun rasa rayukansu kamar yadda na farkon suka rasa rayukansu. Mafi sakarci ma, shine sarkin. Bai ji komai ba, sai ya sake tura rukunin sojoji na uku. Abin farin ciki shine, shugaba na ukun mutum ne mai hikima. Cikin ladabi ya sami Iliya ya roke shi cewa kada a hallakar da shi da mutanensa. Babu shakka Iliya mutumin Allah ne, kuma ya nuna jinkai irin na Jehobah yayinda ya mayar wa shugaban da martani. Sai mala’ikan Jehobah ya umurci Iliya cewa ya tafi tare da sojojin. Iliya ya bi umurnin kuma ya kara nanata hukuncin Jehobah akan shi mugun sarkin. Daidai kamar yadda kalmar Allah ta ce, Ahaziah ya mutu. Shakara biyu tak ya yi a sarauta.​—2 Sarakuna 1:​11-​17.

Iliya ya nuna wa shugaban sojojin jinkai domin yana da tawali’u

Yaya ne Iliya ya jimre a tsakanin mutanen nan, masu tawaye da taurin zuciya? Wannan tambaya tana da alaka a yau, ko ba haka ba? Ka taba samun matsala yayinda wani wanda ka ke kauna ya ki jin shawara mai kyau amma sai ya ya dinga bin hanyar banza? Ta yaya za mu iya jure irin wannan halin? Idan mun tuna da inda sojojin suka sami Iliya, wato “a bisa kwankolin tudu” hakan zai taimaka mana. Ba za mu iya ce ga kwakwarar dalilin da ya sa Iliya ya je wurin ba, amma muna da tabbacin cewa da yake shi mutum ne mai son yin addu’a sosai, ya je wurin ne domin babu wani surutu a wurin kuma hakan zai taimaka masa ya yi kusa sosai da Allahnsa da yake kauna. (Yakub 5:​16-​18) Mu ma za mu iya kebe lokaci mu kadai don mu kusaci Allah, muna kiransa da sunansa muna kuma gaya masa damuwarmu da kuma abin da ke zuciyarmu. Ta haka mu ma za mu iya jurewa yayinda wadanda ke kewaye da mu ke rayuwar da ba ta dace ba amma suna irin rayuwar da za ta kai ga hallaka ne.

Iliya Ya Mika Rigarsa

Yanzu lokaci ya yi da Iliya zai bar aikin da aka ba shi. Mu lura da abin da ya yi. Yayinda shi da Elisha ke barin garin Gilgal, Iliya ya ce wa Elisha ya dakata a wurin, amma shi zai ci gaba shi kadai, zuwa Bethel, mai kusan kilomita 11. Elisha bai yarda ba sam: “Na rantse da ran Ubangiji, da ranka kuma, ba ni barinka.” Bayan da suka iso Bethel tare, sai Iliya ya ce wa Elisha wai shi kadai ne zai tafi Yariko, mai nisan kilomita 22. Elisha ya sake ba shi amsa kamar yadda ya yi dazun. Hakan ya sake faruwa kafin su je Rafin Urdun, a Yariko, , mai nisan kilomita 8, na uku kenan. Har’ila Elisha ya nace. Ba zai bar Iliya ba sam!​—2 Sarakuna 2:​1-6.

Iliya ya na nuna kauna mai aminci, wannan hali ne mai kyau sosai. Wannan ita ce irin kaunar da Ruth ta nuna wa Na’omi, irin kaunar da ba ta rabuwa sam-sam da wanda ka ke kauna. (Ruth 1:​15, 16) Duk bayin Allah suna bukatar irin wannan hali a yau fiye da kowanne lokaci. Mun ga muhimmancin nuna irin halin nan kamar yadda Elisha ya yi?

Babu shakka irin kauna mai amincin nan daga abokinsa ya karfafa Iliya kwarai da gaske. Domin wannan fa, Elisha sai ya sami gatan ganin mu’ujiza na karshe da Iliya ya yi. A bakin Kogin Urdun, wanda ke gudu da kuma zurfi, sai Iliya ya buga ruwan da rigar aikinsa. Sai ruwan ya rabu! Ba Elisha ne kadai ya ga wannan mu’ujizan ba amma “mutum 50 daga cikin ’ya’yan annabawa,” babu shakka suna cikin mutanen da ake koyad da su don yin ja-gorar a ibada ta gaskiya a kasar. (2 Sarakuna 2:​7, 8) Mai yiwuwa Iliya ne ya shugabanci wannan horarwar. Shekaru kadan da suka shige akwai lokacin da Iliya ke jin cewa shi kadai ne mutum mai bangaskiya da ya rage a kasar. Tun lokacin, Jehobah ya saka wa Iliya domin jurewarsa, ya sa ya ga ci gaba mai girma cikin masu Bautarsa.​—1 Sarakuna 19:10.

Bayan sun ketare Urdun, sai Iliya ya ce wa Elisha,: “Ka yi rokon abin da zan yi maka kafin in rabu da kai.” Iliya ya san lokaci ya yi da zai tafi. Bai yi kishin gata da sunan da abokinsa da ya girme shi zai yi nan gaba ba. A maimakon haka fa, Iliya na marmarin ya taimake shi a kowace hanya. Elisha ya roki abu daya tak: ‘ko zan sami irin ruhun da ka ke da shi kashi biyu?’ (2 Sarakuna 2:9) Ba ya nufin cewa yana son a ba shi ruhu mai tsarki irin wanda Iliya yake da shi kashi biyu. A maimakon haka, yana rokan gādo irin na dan fari, wanda bisa doka ya kamata ya dauki mafi girma, ko kuma ninki biyu domin ya taimaka masa a matsayin mai gida. (Kubawar Shari’a 21:17) Da yake shi ne ya gaji ayyukan ruhaniya da Iliya ke yi, ya ga cewa ya dace ya zama mai karfin zuciya irin ta Iliya don ya iya gudanar da aikin.

Iliya mai tawali’u ne, saboda haka, ya bar Jehoba ya mai da martani. Idan Jehobah ya yarda Elisha ya ga yadda Allah zai dauke tsohon annabin nan, to Allah ya amince da rokon Elisha kenan. Kuma ba da dadewa ba, yayinda wadannan abokai na kud da kud ke tafiya, “suna zance,” sai wani abin al’ajabi ya faru!​—2 Sarakuna 2:​10, 11.

Abotar da ke tsakanin Iliya da Elisha ce ta taimaka musu su jimre a mawuyacin lokuta

Wani haske ya sauko daga sama kuma sai matsowa kusa yake ta yi. Mu yi tunanin wata kara, yayinda iska mai karfi ta taso, tare da wani abu mai walkiya na matsowa da gaggawa zuwa wurin mutanen nan biyu, kuma hakan ya sa suka rabu a dole, kila abin da suka gani ya razanar da su har sai da suka ja baya. Abin da suka gani abin tafiya ne, karusa kuwa, mai walkiya kamar an yi ta da wuta. Iliya ya san cewa lokacinsa ya zo. Ya haura kan karusan ne? Ba a bayyana haka a labarin ba. Amma dai, ya ji an daga shi sama, sama, cikin guguwar iska mai karfi!

Elisha sai kallo yake yi, cike da mamaki. Domin yana ganin yadda wannan abin mamaki ke faruwa, Elisha ya san cewa lallai fa Jehobah zai ba shi “ninki biyu” na karfin zuciya irin ta Iliya. Amma bakin ciki ya sa bai yi tunanin nan ba. Bai san ko ina ne babban amininsa zai je ba, amma kuma bai san ko zai sake ganin Iliya ba. Sai ya yi ihu, “Ubana, ubana! Karusar Isra’ila da mahayansa kuma.” Yana ji yana gani yayin da abokinsa ya bace masa; sai Elisha ya yake rigarsa cikin bakin ciki.​—2 Sarakuna 2:​12.

Yayinda Iliya ke tasowa zuwa sararin sama, ya ji abokinsa na kukar kila ma yayi dan hawaye don ya bar shi ne? Ko ma yaya ne, babu shakka ya san samun irin wannan abokin ya taimaka masa kwarai ya jimre a mawuyacin lokuta. Zai yi kyau mu yi koyi da Iliya, mu yi abokai da mutanen da ke kaunar Allah kuma da ke son yin nufinsa!

Jehobah ya dauki Iliya zuwa wani gari don ya yi sabon aiki

Aiki Na Karshe

Daga nan ina ne Iliya ya je? Wasu addinai na koyad da cewa an dauke shi ne zuwa sama ya kasance da Allah. Amma hakan ba zai yiwu ba. Shekaru da yawa bayan haka, Yesu Kristi ya ce ba wanda ya taba hawa sama kafin shi ya zo duniya. (Yohanna 3:​13) Saboda haka yayinda muka karanta cewa “Iliya kuwa ya hau cikin guguwa zuwa sama,” dole mu tambaya, wane sammai? (2 Sarakuna 2:​11) Yayin da Littafi Mai Tsarki ya ambaci “sammai” ba ya nufin inda Jehobah ke zama kawai, amma yana kuma nufin sararin sama, inda gajimare ke haduwa da kuma inda tsuntsaye ke tashi. (Zabura 147:8) Ga wannan sammai ne Iliya ya haura. To sai me kuma?

Jehobah ya dai dauke shi annabin zuwa wani aiki dabam, zuwa wani gari kusa da Yahuda. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Iliya ya yi aiki a wannan wurin, watakila ma shekaru fiye da bakwai. Mugun Sarki Jehoram ne ke sarautar Yahuda a wannan lokacin.. Ya auri ’yar Ahab da Jezebel, saboda haka mugun halayensu na nan har’ila. Jehobah ya sa Iliya ya rubuta wasikar hukunci ma Jehoram. Kamar yadda aka annabta, Jehoram ya yi wata mutuwar azaba. Mafi muni shine, “Ba wanda ya ji zafin mutuwarsa.”​—2 Labarbaru 21:12-​20.

Lallai kuwa akwai bambanci sosai tsakanin wannan mugun mutum da Iliya! Mu dai ba mu san yaushe ne ko kuwa yaya ne Iliya ya mutu ba. Amma dai mun san cewa Iliya bai yi irin mutuwar Jehoram ba, wanda ba wanda yi ji zafin mutuwarsa. Elisha ya yi kewar abokinsa sosai. Sauran annabawan da suka rike amincinsu ma sun yi kewarsa. Jehobah da kansa ya ci gaba da daraja Iliya bayan shekaru 1,000, domin ya yi amfani da kamannin wannan kaunataccen annabin a wahayin sake kamani. (Matta 17:​1-9) Kana son ka yi koyi da Iliya ka kuma gina bangaskiya da zai jure duk wani wahala? To kar ka manta, , ka yi abota da wadanda ke kaunar Allah, ka mai da hankalinka sosai a bautar Jehobah, da kuma ka dinga yin addu’a daga zuci a kowane lokaci. Bari kai ma ka sami wuri na dindindin a cikin zuciyar Jehobah!

^ sakin layi na 6 Wasu dalibai sun fada cewa wannan dutsen da aka ambata a nan Dutsen Karmel ne, inda Allah ya taimaka wa Iliya ya ci nasara akan annabawan Baal shekarun baya. Hakazalika, Littafi Mai Tsarki bai fadi ko wanne dutse ba ne.